’Yan sanda a Kano sun ce sun cafke Adamu Musa mai shekaru 50, dansa Sule Malam da kuma jikansa, Isyaku Sule, saboda kashe wani da ake zargi da satar mutane da ‘yarsa ‘yar shekara biyar a kauyen Gomo da ke Karamar Hukumar Sumaila. Kakakin rundunar ‘yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya fada a cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata cewa, Musa ya furta da bakinsa “ya umurci’ ya’yansa maza uku da jikansa da su kashe wani mutum ake zargin mai satar mutane ne.”
Kiyawa Kiyawa ya fada a ranar 26 ga watan Agusta, wadanda ake zargin sun mamaye matsugunin Madunkuri da ke kauyen Gomo, Karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano, ”sun kai hari sun kashe wani matashi mai suna Kabiru Ya’u mai shekara 30 da ‘yarsa Harira Kabiru. Ya ce wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun yi amfani da adduna da kuma gora wajen yi wa wadanda suka kashe fyade. A cewarsa, ‘Operation Puff Adder’ sun kama wadanda ake zargin a ranar 19 ga watan Disamba kimanin kwanaki 119 bayan faruwar lamarin.