Da maraicen ranar Laraba 26/3/18 wani gangamin mahara dauke da muggan makamai suka kai hari a garin Birane dake kasar Zurmi cikin jihar Zamfara, inda suka kashe utane 38 suka ji wa 10 mummunan rauni.
Wakilinmu ya ruwaito daga wata majiya mai tushe yadda lamarin ya faro: Gumngjun barayi ne suka hadu da wasu ‘ya nbanga su biyu suna farauta, sai barayin suk,a kashe dan banga daya suka ji wa dayan ranni. Isar dayan da aka jiwa rauni gida ya ba da labarin abin da ya same shi tare da dan’uwansa, sai sauran ’yan banga suka fita daji don neman barayin su dauki fansa. Sun isa wata tunga suka iske barayi uku da dabbobinsu, ganinsu su kuma barayin suka gudu suka bar dabbobin ‘yan bangar suka koro dabbobin zuwa garin Birane.
Bayan sun zo da su gari suka sanar da masarautar Zurmi inda masarauta ta ce masu su koro su zuwa garin Zurmi inda ake tara dabbobn da aka kwato daga barayi i (wajen sojoji) . kafin su koro sai suka sami sako daga barayin cewa, su shirya suna nan tafe za su zo su kwaci dabbobinsu. Inda su kuma ‘yan bangar suka ce suna jiransu, sannan kuma suka sake sanar da masarauta ga abin da ake ciki. Sarki ya sanar da sojoji amma ba su tafi ba. Ta kai har sarki ya je da kansa wajen sojoji amma sai ya iske soja goma sha uku ne wajen kawai . Wannan ya faru ranar Talata, ranar Laraba ganin ranar kasuwar Birane ke ci, dan haka su ‘yan banga suka yo ganagami suka tsare garin ta ko’ina. Su kuma barayin suma sun yo nasu gangami suka tare hanyar zuwa garin kimanin kilo mita uku daga garin suka tsaya cikin da daji, suka yi kwanton bauna suna dakon duo k wanda zai je garin ko fita.
Malama Sakina daya ce daga wadanda abin ya rutsa da su amma ba ta mutu ba. Ga abin da shaida wa wakilinmu: ”Na zo kauyenmu Gidan Kayya don in gai da iyayena, da zan koma garin da nake aure Jena sai na je kasuwa na shigo mota, a kan hanya muna cikin tafiya sai muka ji direbanmu ya ce, ‘ga ko mutanen nan can, sai ya taka burki muka ga ya kashe mota ya fita a guje, sai muma muka diddiro kasa. To ni da na diro sai na bi maza a guje sauran mata suka bi nasu waje. Da barayin suka iso suna harbi sai mazan suka kwakkwanta nima sai na kwanta. da suka same mu sai na ji wani ya ce, wannan ba ta mutu ba. Shi ne su kai man sara biyar, uku a kai daya a wuya daya kuma a hannu (ya karye). Sun kashe duk mazan. Wanda duk suka kashe sai kuma su sassare shi da adda.”
Sakina ta bayyana cewa mai martaba sarkin Zumi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad tne yake daukar dawainiyar asibitinsu. Galibin wadanda aka kashen sun fito daga kauyukan Tungar Fulani, Tunfa, Mashema, Gidan Kayya, Birane, Garin Kada,Mayasa, Gidan tsika, Tungar Nasarawada Jena
Zayyanu Ab ubabakar, dan garin Zurmi ne kuma daya daga cikin wadanda lamarina ya ruts a da su. Wakilinmu ya ziyarce shi a asibiti, ga abin da ya shaida masa: ”Na dauki wata mata (kabo-kabo), daga Zurmi zuwa Tungar Fulani, na bar Birane ban kai tungar ba na raba tsakiya, sai ga su wadannan mutane (barayi) mun hadu da su a kan hanya, bayan na wuce mota a tsaye. Sai bayan na wuce motar sannan na gane ashe su ma hange su suka yi suka tsaya. Ban ankara ba sai na gan ni cikinsu, suna ta wucewa, sai da na kai tsakiyasu sai wani ya zo a goje ya harba bindinga kusa da kaina. Jin wannan karar, nan muka kife a kan mashin ni da wadda na goyo.
Mun dade nan kwance sai na kusa da karshe ya zo, ya harbe ni nan a baya. Bayan ya harbe ni na kife, a lokacin ban san inda nake ba. Daga baya na farfado sai na ga mutane suna dirikewa daga mota suna gudu suna shiga daji. Ni ma sai na yunkura in tashi sai na ga jin yana ta zuba. A haka dai Allah ya ban kwarin guiwar da na daga mashin din zan buga sai ga wani ya keta ihu ya nufo ni da bindiga zi kara harbi na. Ina waigawa na gan shi dab da ni, sai Allah ya sa na yi watsi da mashi din na yi ta kaina. Ina gudu yana bi na yana harbi Allah bai ba shi sa’ata ba, har na kai wata ‘yar korama na gangara na fadi karkashi wata bishiyar kalgo. To a nan Allah ya kubutar da ni, shi kuma sai ya koma. Na dade nan kwance ina jin karar bindigogi. Daga baya can dai na ji karar ta lafa sai na rarrafa ina duba wayata don in ga inda zan sami ‘serbice’. Can da na kai inda serbice yake sai na sami wuri na labe na kirsa waya cikin garin Zurmi na sanar da su halin da muke ciki. Na ce, yanzu haka an harbe ni. Daga nan sai aka sanar da Amiru (Bafaden sarki) sai aka sanar da sojoji. Kafin su zo har sun kone motar da kayanci sun tafi da babur dina.
Zayyanu ya bayyana cewa cikin dare sojoji suka dauko shi tare da wasu gawar waki kamar ashirin, suka ce saura sai da safe a zo nemansu. A kofar gidan sarkin Birani aka, a yanayin da ban taba tsammanin zan rayuba. kai gawarwakin. Ni kuma suka kawo ni nanAsibiti. Ita kuwa matar da ya dauko sai da safe da aka koma neman sauran gawarwaki aka tsinnto ta takwana cikin daji.
Zayyanu ya ce, maharan akalla za su kai dari hudu, domin Baburansu sun kai dari biyu kowane dauke da mutum uku. Daaga karshe ya yi kira ga Hukuma da cewa, ya kamata ta dauki al’amarin nan da muhimmanci domin a samar da zaman lafiya a wannan yanki dakasa baki daya.
Yanzu haka sai jama’a ke tatururuwa zuwa fadar mai martaba sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad, domin jajanta masa game da wannan da’adanci da ya faru a kasarsa. Ko ranar juma’a 16/2/18 Shugabanb ‘yan sanda na kasa, Ibrahim K. Idris da Gamnoni Zamfara Dr Abdul’aziz Abubakar yari da na Borno, Kashin Shettima da Aminu Tambuwal na Sakkwato, Abubakar Bagudu na Kebbi da Umar Almakura na jihar Nassarawa duk sun zo garin na Zurmi domin jajanta wa sarki. Inda sarkin ya gaya wa gwamnonin cewa, “mu kam ba jaje muke bukata daga gwamnati ba, abin da muke bukata shi ne kare rayukanmu da dukiyoyinmu.”
“Yanzu dai shekar daya ke nan da gwananatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dr Abdul’aziz Abubakar Yari, ta yi taron sulhu da barayi a kasar Zurmi a kan su daina sata da kashe-kashe. Ita kuma za ta biya masu bukatunsu. Sai ga shi har yanzu ba ta canza zane ba tsakanin al’ummar wannan yanki da barayin. Inda bayan satar dabbobin har da na mutane ake yi ba kakkautawa, ga kuma kashe-kaahen na ci gaba”. Cewar wsu da suke tofa albarkacin bakinsu a kan wannan lamari.