Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi watsi da ratoton Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai cewa manoma 110 ne mayakan Boko Haram suka kashe a Zabarmari, Jihar Borno.
A ranar Lahadi, Ofishin MDD na Nijeriya, ta bakin Babban Jami’inta, David Kallon, ya ce bayan mutum 43 da aka binne a ranar, an gano ragowara gawarwaki a warwatse wanda hakan ya kai adadin ga 110.
Amma safiyar Litinin, kakakin Hedikwatar Tsaron, Manjo Janar John Enenche ya yi watsi da rahoton inda ya ce manoman shinkafa 43 ne mayakan suka kashe sabanin rahoton na MDD.
Enenche wanda ya kasance bako a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce sojoji tare da mazauna ne suka tattara tare da kirga gawarwakin kuma 43 suka samu ba 110 ba.