Connect with us

MANYAN LABARAI

Kisan Matukiyar Jirgin Yaki: An Bankado Wadanda Ake Zargi

Published

on

Hukumar Sojin Saman Nijeriya ta bayyana sunan wasu mutum uku da ake zarginsu da hannu a mutuwar jami’a Tolulope Arotile, wacce ita ce mace ta farko matukiyar jirgin yakin soji a tarihin Nijeriya, wanda ya afku a makon da ya gabata.

Hukumar ta bayyana sunan Nehemiah Adejoh, Igbekele Folorunsho, da Festus Gbayegun; a matsayin wadanda ake zargi a mutum matukiyar, inda sakamakon binciken farko ya nuna akwai alamar tambaya akan mutanen.

A takardar da hukumar Sojin Saman Nijeriya ta fitar, wacce Shugaban rundunar Ibikunle Daramola ya sanyawa hannu, ta nuna akwai alamun tambaya akan mutanen uku, duba da yadda suka yi mu’amala ta karshe da matukiyar kafin daga bisani daya daga cikinsu ya ture ta da mota. Hukumar ta bayyana cewa ta mika mutanen ga hukumar ‘yan sanda don cigaba da gudanar da bincike da hukunta wanda aka samu da laifi.
Advertisement

labarai