Kisan Mutane A Zamfara: Matawalle Ya Sanya Takalmin Karfe

Matawalle

Daga Hussaini Yero,

Tura takai bango a Jihar Zamfara sakamon kashe mutane babu kakautawa a fadin jihar, yanzu haka Gwamna Bello Matawalle, ya sanya takalmin karfen take duk wanda ke da hannu a ciki komai girmansa .

Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke wa al’umma jihar jawabi na musamman a kafofin yada labarai.

A jawabin sa gwamna Matawalle ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai kauyan Kadawa cikin Karamar Hukumar Zurmi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 49,” in ji Matawalle.

Gwamna Matawalle ya jaddada cewa, za mu ci gaba da aiki tukuru domin kalubalantar wadannan marasa imani da rashin son zaman lafiyar.

“Kuma a ‘yan kwanakin nan, mun fahimci cewa, hare-haren ta’addanci sun karu matuka a sassa daban-daban na jihar nan. Wadannan ‘yan’ ta’addar ba sa la’akari da kiyayewa daga hakkin kashe kananan yara, mata, da tsofaffi. Hakika rashin imaninsu ya kai matuka. Kuma muna sane da cewa wadannan hare-hare sun yi sanadiyyar raba iyalai da dama daga matsugunnansu. wannan abin alhini ne da damuwa ga gwamnati,” in ji Gwamnan.

Gwamna Matawalle ya kara da cewa, al’ummar Jihar Zamfara sun san yadda muka shigo wannan gwamnati tamu mun yi iyakacin kokarin mu domin ganin mun ci galaba a kan wadannan makiyan, mun samu nasarori da dama, amma abin bakin ciki shi ne a ‘yan kwanakin nan lamarin ya sauya sanadiyyar ayyukan wadansu fandararru a sassan jihar nan.

Kuma mun fahimci cewa, akwai wasu marasa kishin kasa wadanda burinsu shi ne tarwatsa jihar domin biyan bukatun kansu. Ina kira ga al’umma su ci gaba da addu’o’i domin Allah ya tona asirin wadannan kangararru da kuma masu taimaka ma su.

Matawalle ya tabbatar wa al’aummar wannan jiha cewa ba za mu yi kasa a gwiwa wajen yakar wadannan bata gari ba, kuma a wannan yaki da muke yi da ta’addanci, gwamnatinmu ta dauki matakin ba sani ba sabo, duk wanda aka samu da hannu za’a daukin matakin da ya dace akansa komai girman matsayinsa.

Irin wadannan matakai su ne irin wadanda muka fara dauka akan manyan sarakuna kamar na Maru, Dansadu, da kuma na baya-bayan nan.

“Haka zalika, gwamnatinmu za ta fara aiwatar da shawarwarin da ke kunshe a cikin rahoton kwamitin Tsohon Babban Sufetan ‘yan sanda, MD Abubkar.

Idan al’umma za su tuna, a lokacin da na karbar rahoton kwaminitin a ranar 11 ga Oktoba 2019, na tabbatar wa da al’umma cewa za mu yi amfani da wasu daga cikin shawarwarin kwamitin domin kai karshen wannan matsala wadda ta ki ci ta ki cinyewa, wadda muka gada.

“A karshe ina son na yi amfani da wannan dama domin jaddada kirana ga al’ummar jiha da su tashi tsaye domin kare garuruwansu idan an kawo ma su harin ta’addanci. Duk wanda ya ce gwamnati ta ce kada su kare kansu karya yake yi Wa wannan gwamnanti. Abin da kawai muka hana shi ne yawo da makamai a kasuwannni don takalar fitina.

Exit mobile version