Daga Rabiu Ali Indabawa,
A ranar Litinin Kwamishinan ‘yan sanda na Delta, Mohammed Ali, ya zargi kungiyoyin asiri da laifin yawan kashe-kashen da ake yi wa ‘yan sanda a wasu sassan jihar. Ya gargadi ‘yan kungiyar da su daina ko kuma su fuskanci sakamakon ayyukansu. Ali ya yi magana a kan sake kisan wani dan sanda a Warri a ranar Alhamis.
Ya kuma ce, rundunar ‘yan sanda na cikin fargaba kan yawan kashe-kashen da ake yi wa ‘yan sanda lokacin da suke gudanar da ayyukansu na halal. CP Aliyu ya sake jaddada kudurinsa na kare lafiyar maza da jami’ai a kowane bangare na jihar da aka tura su yin aiki.
Ya ce, “Daga bayanan kashe-kashen ya zuwa yanzu, mun fahimci cewa wadanda ke da alhakin kisan ‘yan sanda da kuma kwace bindigoginsu mambobin kungiyar ‘yan ta’adda ne, musamman na kungiyoyin asiri, wadanda suke matukar bukatar makamai da alburusai, don su samu fifiko a kan sauran kungiyoyin da suke kishiyantarsu a wani yanki.
“A kwanan nan mun kaddamar da ‘Yankin Bincike na Dindindin’ a wasu wurare masu mahimmanci musamman a cikin yankin Warri da kewayenta inda wannan laifin ya bayyana yana karuwa a cikin kwanan, sannan nan kuma mun tura karin maza don wannan dalili.”
Ya bukaci mambobin yankin su hada kai da ‘yan sanda wajen dakile laifuka masu karfi a cikin al’umma ta hanyar fallasa bayanai masu amfani da za su iya kai wa ga kame wadannan masu laifi. CP Aliyu ya lura cewa sai da irin wannan bayanai masu amfani ne kawai ‘yan sanda za su iya aiki yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, wani jami’in ‘yan banga da aka bayyana a ranar Litinin a garin Otokutu, yankin Ughelli na Karamar Hukumar Delta ta Yamma, ya daba wa wani Omezu Martins wuka har lahira. An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma. Duk da cewa bayanai game da lamarin ba su bayyana ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, an samu labarin cewa dan sandan ya je ne don sasanta wani rikici tsakanin abokinsa da mamacin.
Majiyoyi sun yi ikirarin rashin fahimtar da ke tsakanin su biyun ya kusan kai wa ga fada lokacin da dan banga ya dabawa Martins wuka a kirji.
Rahotanni sun ce an garzaya da wanda aka kashen zuwa asibiti a yankin, amma daga baya ya mutu. A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu a Sedeco, Karamar Hukumar Ubwie da ke jihar.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi. Kakakin rundunar ‘yan sandar Delta, DSP Edafe Bright, ya tabbata da faruwar lamarin ga jaridar The Nation ta wayar tarho.
“Zan iya Tabbatar da batun ‘yan banga da wani mutum da aka dabawa wuka yam utu har lahira. Kuma DPO din ya ce suna binciken kan lamarin har yanzu,” inji DSP Bright.