Kisan Zabarmari: Majalisar Wakilai Ta Yi Sammacin Buhari

Haraji

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

 

Majalisar Wakilan Nijeriya ta aike wa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari sammaci bisa mummunan kisan kiyashin da a ke yi wa manoma da masunta a Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a Jihar Borno.

’Yan majalisar sun yanke shawarar gayyatar shugaban kasar ne a jiya Talata bayan da Hon. Satomi Ahmed ya gabatar da kudirin hakan a matsayin bukatar kasa ta gaggawa.

Shi dai wannan hari da a ka yi a ranar Asabar da ta gabata, 28 ga Nuwamba, 2020, ya bar gawarwaki 43 nan take, wadanda a ka yi jana’izarsu a washegari Lahadi, sannan wasu rahotanni sun bayyana cewa, an kashe kimanin mutane 110, baya ga wadanda su ka bace.

Shi kansa Shugaba Buhari ya yi tir da kisan kiyashin, kuma ya aike da babbar tawaga, don yin ta’aziyya a karkashin jagorancin  Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, zuwa Jihar Borno.

Tun da fari an samu turjiya kan kudirin sammacin shugaban kasar, amma bayan zaman sirri da shugabannin majalisar su ka yi, sai a ka sake amincewa da gabatar da kudirin, don kiran Shugaba Buhari ya zo da kansa ya yi wa majalisar bayani kan kalubalen tsaron da a ke ciki a kasar.

Nan take ’yan majalisar su ka hada baki wajen amince da gayyatar.

Exit mobile version