Kishin Al’umma Ya Sa Muke Hidima Ba Don Siyasa Kadai Ba – Aminu Boyi

Aminu Boyi

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Kyakkyawar manufa da kyautatawa matasa da hidimta al’umma tarbiyace da muka samu data iyaye, don yiwa al’umma hidima yanzu muka Fara. Jawabin Haka ya fito daga Bakin matashin dan siyasa Mai kishin kaunar ganin ana samawa da matasa a kowane mataki na sha’knin rayuwar Yau da kulluma musamman a Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Aminu Boyi lokacin da yake yiwa manema labarai bayani Kan kyawawan manufofinsa a siyasance da Kuma al’amarin Yau da kullum.

Aminu Boyi ya ci gaba da cewa, dole sai an sauya akidar rufa rufa da wakaci was tashi matukar ana fatan ganin al’amura sun kyautata. Musamman a irin wannan lokaci na siyasa da kowa ke Baje kolinsa domin ganin Jama’a sun Gamsu dashi tare da sahale Masa jagorancinsa. Wannan tasa “Ni irin tarbiyar da muka samu Babu ko a Mutu ko ayi rai abatun takara, wannan tasa Muke cikin nutsuwa Kuma Muke tare da matasa ako da yaushe.

Da aka tambayeshi me yake gani ko Mai zaice dangane da kiranye kiranyen da Jama’a ke Masa na sake fitowa takara akakar zaben Shekara ta 2023? Sai amsa da cewa ba don kaina nake siyasa ba, duk abinda al’umma Suka hangs daga gareni Wanda suke kyautata min zaton bayar da tawa gudunmawar ko shakka Babu ashieye nake sai dai Kuma sai an Yi hakuri domin akwai sauran lokaci, Muna son abaiwa wadanda ke damar karasa zangonsu, sannan ai dora kowannensu akan sikeli.

Da yake tsokaci Kan kirar da ake ganin ta tasowa Jam’iyyar APC, wadda ake ganin na zaman  barazanar ga nasarar Jam’iyar akakar zaben Shekara ta 2023?  Sai ya amsa da cewa, wannan abun da duk ake ganin yanzu matakin nasara ne, domin sai kana da farin jini ake rurumarka, don wannan alama ce ta nasarar Jam’iyya.

Exit mobile version