Connect with us

RAHOTANNI

Kishin Ilimin Arewa: Bayan Sardauna Babu Kamar Jonathan – Tanko Yakasai

Published

on

An bayyana cewa, tun bayan Firimiyan Jihar Arewa, Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, ba a samu shugaban da ya ke kishin ilimi a Arewa kamar tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ba.

Wannan jawabin ya fito ne daga dakin daya daga cikin dattawan Nijerya daga Arewa mai shekaru 94 a duniya, Alhaji Tanko Yakasai, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai gidansa da ke birnin Kano ranar Litinin da ta gabata.
Alhaji Tanko Yakasai, tsohon dan NEPU, tsohon Kwamishina Yada Labarai, Matasa da Wasanni kuma tsohon Mai Ba Wa Shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha, shawara, ya ce mulkin Jonathan akwai sabu biyu na alheri da duk rashin adalcinsa mutum ba zai ce ba haka ba ne da ya yi wa Arewa.
A cewarsa, “na farko shi ne ya kafa jamioi 12 da ya yi a Najeriya, wanda ya ba wa jihohin Arewa guda tara daga ciki, Kudu guda uku. Wannan alkairi ne ga Arewa da alummar Arewa da tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi da babu wani shugaba a shugabannin da mu ka yi cikin shekara 21, domin Obasanjo bai yi haka ba, ’Yar’Adua shi ma bai yi haka ba duk da shi ma ya taho da tsari mai kyau rai ya yi halinsa. Haka yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shekara biyar bai yi irin wannan tsari na gina jamioi 12 ba, kamar yadda Janaton ya yi ma na a Arewa.”
Dattijo Yakasai ya ce, wani abu na biyu wanda shi ma Arewa ta samu duk da yanzu ba mu san makomar abin ba, amma dai Janaton ya nuna kishinsa ga Arewa, wanda shi ne Shugaban kasa dan Kudu da ya zo ya gina tsangayu na karatun Alkur
ani, domin inganta karatun allo, domin inganta shi da sabunta shi daidai da zamani, wanda wannan ba karamin al`amari ba ne, musamman da a ke ta koke-koke na cewa, dadadden tsarin na bukatar sabuntawa da ingantawa.
“To, Jonathan ya gina makarantu, domin gyara harkar almajirci da wasu su ka jahilta su ke gani kamar almajirci wani abu ne maras kyau, a’a ba haka ba ne. Fita don neman ilimi ko don tsira da addini ba sabon abu ba ne a tarihi.”
Idam dai za a iya tunawa, ko a karshe mulkin Jonathan a 2015 ya daga darajar Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano (FCE) zuwa mataki na jami’a, amma bayan zuwan mulkin Shugaba Buhari a ka yi mi’ara-koma-baya.
Advertisement

labarai