Daga Mustapha Ibrahim, Kano
Alhaji Ahmed Rabiu kwamishinan ciniki da masana’antu a 2015 zuwa 2019 kuma shugaban kamfanin Dala Inland Dry Pout da ke Kano ya bayyana cewa aikin katafarin tashir tsandauri na sauke kaya daga kasa shan waje dama cikin gida na hadin gwuwa a tsaka nin gwanatin tarayya da gwanatin jihar Kano wanda aka samu tsaiko da jinkiri saka makon matsalolin tattalin arziki da kuma matsalar zuwan Korona, amma yanzu gwamnan jihar kano Dakta. Abdullahi Umar Ganduje ya yi rawar gani ya kuma nu na kishin sad a son cigaban Kano, bisa sanya zunzurutin kudi har Naira Billiyon Biyu da Naira Milliyon 300 wanda hakan ta sa nan da wata uku masu zuwa Kanawa da sauran Alummar Arewa da Nijeriya za su fara cin gajiyar wannan aikin na tashar tsandauri da ke unguwar zawaciki, da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano Nijeriya.
Hon. Ahmed Rabiu Ya Bayyana Haka ne a yayin ziyarar gani da Ido da manema labarai su ka kai a wannan wurin aiki dan ganewa idonsu yadda aikin tashar tsandaurin Kano ya ke a wannan lokaci, ya ce yanzu haka wannan kudi ya sa aikin ya tasu gadan gadan inda aike tituna a cikin tashar da gina dabi da manyan motoci kamar 4 zuwa 5 zasu hau suyi tsaya dan sauke kaya mai kimanin nauyi Ton 150 sai kuma aikin wurin sauke kaya da kuma ofis ofis na gudanar da ayuka da sauran gine gine da ake bukata dan tafi da ayuka kamar masaukin baki da wuraran cin abinci da sauran su duk yan zu ana nan anayi wanda nan watan Yuni watu rabin shekarar 2021 za’a amfani da wannan tashar tsandauri ta Kano.
Hon. Ahmed Rabiu ya ce wannan aikin yadda mutikar amfani ga Alumma domin zai maid a Kano Jiha Mai karfin Kudin shiga da karfin tattalin arziki kamar legas ko fiyi da legas a afrika, kuma matakin farko matasa kamar 200 za su samu aikin yi kuma sauran kamfanoni da za su baiyyana a tashar za su dauki matasa sama da 2000 aikin yi kuma za’a samu bun kasar tattalin arziki saka makon yin wannan tasha ta ya yadda dakon kaya zai karo kuma zaiyi sauki mai yauwa a saka makon wannan aiki wanda hakan zai sa a samu dadewa na titi nan mu dade sauran amfani mai yauwa a wannan aiki ya ce wannan tashar tsandauri na da fadin Hikta, daya da rabi a yanzu a matakin farko da aike aiki a kanta ya yin da fadinta gaba daya ya kai hikta biyar dama in da ana ganin za’a iya fakin din Tirela kamar 1000 in an kamala wannan aiki gaba daya.
A karshe dai Hon. Ahmed Rabiu ya yaba wa shugaban kasa kan kadamar da aikin titin jirgin kasa daga Katsina zuwa Maradi da cewa wani abu ne da zai kawu wa Nijeriya da makutanta dama afirika baki daya cigaba a wannan lokaci da de sauran abubawa da shugaban ya ke yin a cigaban kasa.