Abdullahi Muhammad Sheka" />

Kishin ‘Yan Kasuwarmu Ya Sa Mu Ka Raba Tallafin Abinci – Sharif Wada

AMBASADA ALHAJI SHARIF SAGIR WADA, shi ne Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Kasuwar Kantin Kwari, mai kuma kaunar cigaban harkokin kasuwanci a Jihar Kano da Kasa baki-daya. A tattaunawarsa da wakilinmu A Kano, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, ya bayyana tsananin damuwar ‘yan kasuwar bisa halin da duniya ke ciki a wannan lokaci da ake fuskanta na Annobar Cutar Cobid-19, sanan ya jaddada aniyarsa ta tallafawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano, na taimakawa masu karamin karfi a lokacin zaman gida da takaita zirga- zirga da Gwamnati ta umarci jama’a su yi, a wani yunkuri na dakile yaduwar wannan cuta a Jihar Kano. Ga dai yadda tatattaunawar ta kasance:

Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatu?

Alhamdulillahi! Ni dai kamar yadda aka sani, sunana Ambasada Alhaji Sharif Sagir Wada, Shugaban Kungyar Hadaddiyar ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari a halin yanzu.

Kwanan nan aka ji wani kokarin da kuke yi na tallafawa kananan ‘yan Kasuwa da kayan abinci, shin ko mene ne dalilin yin wannan hange?

Gaksiya ne, Shugabancin wannan kasuwa bayan yin dogon nazari irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kano, karkashin Gwamna Dakat Abdullahi Umar Ganduje ke yi domin ganin an rage radadin matsin rayuwa da kuncin da masu karamin karfi ke fuskanta. Wannan tasa a matsayinmu na ‘yan kasuwa, mun san halin da kananan ‘yan kasuwar ke ciki, musamman ganin yadda aka dauki matakin rufe iyakokin da ke shigowa Jihar Kano, kuma kamar yadda aka sani sai baki sun shigo wasu ‘yan kasuwar ke samun abin sawa abakin salati. Don haka, sai muka yanke shawarar tuntubar Attajiran da ke cikin wannan kasuwa domin neman tallafinsu, kuma Alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu.

Zuwa yanzu kenan an fara samun abinda ake fatan samu domin rabawa kananna ‘Yan Kasuwar?

Ba abinda za mu ce da Attajiran Kasuwar Kantin Kwari sai godiya, domin sun amsa kiran da muka yi musu ta hanyar bayar da gagarumar gudunma, wadda mu kanmu mun yi mamaki kwarai da gaske, ya zuwa yanzu an samu gudunmawar kayan abinci da suka hada da shinkafa, taliya, sabulu da sauran abubuwan da ake bukata wajen yakar wannan mummunar cuta.

 

Wace hanya kuka bi wajen zakulo wadanda ya kamata su amfana da wannan tallafi?

Alhamdulillahi, kasancewar akwai kananan ‘yan kasuwa masu yawa, wadanda suka hada da ‘yan tebura, ‘yan dako da sauransu, hakan tasa muka yi amfani da Shugabannin rassan kungiyar ‘yan kasuwar ta kwari, wadanda suka hada da ’yan tebura da sauransu, inda muka kira Shugabaninsu wanda muka damkawa kowace kungiya nata kason tare da bukatarsu da su koma layukansu, domin duba wadanda suka cancanci samun wannan tallafi, sakamakon cewa mai daki shi ya san wurin da ke masa yoyo.

Yanzu wannan yunkurin kuna ganin sakon ya kai ga wadanda ake fata?

Ko shakka babu, kamar yadda ku ‘yan Jaridu kuka gane wa idonku, tun a ranar Litinin da ta gabata muka fara aikin rabon wannan tallafi, kuma Alhamdulillahi dukkanin wadanda aka damkawa wannan amana, suna isar da ita ga wadanda aka tsara domin su. Kuma ana cigaba da gudanar da wannan aiki, wanda saboda yawan jama’armu muna ganin kila mu cigaba da wannan aiki har zuwa watan Azumi.

Akwai wasu da ake gani a matsayin jagororin wannan kungiya, shin ko a bangarensu wace gudunamawa suka bayar?

Mu na godiya ta musamman ga Shugaban Kwamatin Amintattun wannan Kasuwa ta Kantin Kwari, karkashin Shugabncin Alhaji Bature Abdul’aziz, wanda duk abinda ake yi da shawarsu da kuma yardarsu, ya yi matukar kokari musamman a wannan lokaci da al’amura suka zama abinda suka zama. Babu shakka, dole mu gode mu su tare da sauran masu ruwa da tsaki a cikin harkokin gudanar da cigaban wannan kasuwa mai dadadden tarihi.

A baya Kungiyar Kasuwar Kantin Kwari, ta yi fama da matsala tsakaninta da sabon Manajan da Gwamnati ta turo kasuwar, zuwa yanzu an ji shiru ko mene ne sirrin hakan?

Alhamdulillahi, mu da ma da Allah da muka dogara, kuma kamar yadda aka sani mu Kasuwar Kwari ce a gabanmu da cigabanta, wannan tasa muka koma teburin sulhu tare da sauraron shawarwarin iyayen kungiyar, kuma muna yi wa Allah godiya da irin goyon bayan da ‘yan kasuwa suke baiwa wannan Shugabanci, yanzu an yi walkiya an ga kowa, ‘yan kasuwa sun gamsu tare da mika wilayarsu ga Shugabancin wannan kasuwa.

Ya dangantaka take tsakanin kungiyar kasuwar da kuma bangaren Gwamnati?

Alhamdulillahi, kamar yadda masana tarihi suka bayyana tun sama da shekaru 40 ake da wannan kungiya kuma ake aiki tare da bangaren gwamnati, musamman a wannan lokaci da aka samu Gwamna wanda ke nuna damuwa da harkokin kasuwanci. Aikin kungiyar kasuwa daban, haka kuma aikin bangaren wakilin gwamnati shi ma daban. An kuma yi wakilai daga bangaren gwmantoci daban-daban, wanda kungiyar kasuwar suka yi aiki tare har kuma suka kammala cikin Natija. Wannan tasa duk wanda aka kawo babban abinda muke fatan nusar da shi shi ne fatan yin aiki tare domin dan kasuwa shi ne ya san matsalar dan’uwansa dan kasuwa.

Saboda haka, duk lokacin da aka kawo sabon Manajan Darakta, fatan da muke da shi shi ne samun hadin kan ‘yan kasuwa da Shugabancinsu, hakan ne zai ba shi damar yin aiki tare, domin kawo cigaban da ake fata.

Yanzu da ake fama da matsaloli iri daban-daban, wadanda suka hada da matsalar Jami’an hana Fasakauri, wasu kudade da ake karba daga hannun ‘yan kasuwa, shin ko me ake ciki zuwa yanzu?

Alhamdulillahi, batun harkokin Kwastan kullum muna kokarin fahimtar da su tare da neman hada hannu da kungiyoyin ‘yan kasuwa wajen yaki da Fasakaurin kayan da gwamnati ta haramta shigo da su, mu Shugabannin wannan kasuwa a shirye muke wajen hada karfi domin dakile shige da ficen kayan da aka haramta shigo da su cikin kasa. Kuma Alhamdulillahi, ana samun cigaba kwarai da gaske.

Haka nan, shi ma bangaren wasu kudade da ka yi Magana, wannan tuni Hukomin da abin ya shafa suka dauki matakan da suka dace, domin hana waccan matsala, akwai batun wata Naira Miliyan guda da ake karba a hannun bakinmu, wannan
kudi abinda muka nema shi ne samun hujjar karbar su, wanda kuma ba mu samu ba har wasu masu kishin kasuwar suka shigo ciki aka kuma dauki matakin da ake kai a halin yanzu.

Zuwa yanzu wadanne abubuwa Shugabancinka ya sa a gaba?

Kamar yadda aka sani, akwai batutuwa masu yawa wadanda muka sanya a gaba, da farko dai yanzu mun dauki gabaren kokarin hada kan ‘yan kasuwa da sauran wakilan gidaje da layuka, wanda kuma Alhamdulillahi yanzu kusan dukkanin wadannan bangarori sun yi mubayi’a da wannan Shugabanci. Muna aiki babu dare  babu rana wajen samar da kyakkyawan tsarin tsaro da kuma tsaftar wannan kasuwa.

Yaya dangantaka ke tsakaninku da bakin haure wadanda ke gudanar da harkokin kasuwanci a cikin Kasuwar Kantin Kwari?

Mu na yi wa Allah godiya, domin akwai kyakkyawar fahimta tsakaninmu da Aminanmu baki, wadanda ake gudanar da harkokinsu a cikin wannan kasuwa. Musamman ‘yan Kasashen Waje, wadanda muke zaune tare da su. Sannan akwai tsare-tsare wadanda doka ta tanada ga duk wanda ke gudanar da harkokinsa a cikin Kasuwar Kwari, kuma suna ba mu hadin kai kwarai da gaske.

Ganin ka na da Abokan aiki da kuke Shugabantar wannan kungiya, shin ko ya dangantaka take a tsakaninku?

An zo wurin, domin akwai kyakkyawar fahimta da aiki tare da kuma tsayawa tsayin daka wajen yin aiki tare, babu shakka duk nasarar da na samu a karkashin wannan Shugabanci, ya samu ne sakamakon kyakkyawar fahimtar da ke tsakaninmu, kuma ido ba mudu ba ya san kima, aikin tattara wadannan kayan tallafi ke tabbatar da aiki tare da nake yin bayani, domin dukkanmu babu wanda ke runtsawa matukar akwai wata matsala da ke addabar kasuwar da ‘yan kasuwar, babu shakka ina mika godiya ta musamman gare su tare da fatan cigaba da wannan kyakkyawar niyya.

Mene ne sakonka na karshe?

Sakona da farko dai zai tafi ne ga Abokanan aikinmu, wadanda mu ke yin aiki tare domin jagorantar harkokin Kasuwancin Kasuwar Kwari, wadda ita mu ka sani nan kuma mu ke gudanar da harkokinmu na yau da kullum, sannan ina kara mika sakon godiya ga Gwamna da Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa irin kulawar da ake baiwa harkokin kasuwarnci da taimakon ‘yan kasuwa. Sannan, muna rokon Allah ya kara zaunar mana da Jiharmu ta Kano da kasa baki-daya lafiya, Allah kuma Ya magance ma na wannan lalura da ke addabar duniya baki-daya, amin.

Exit mobile version