Daga Abubakar Abba
Kasuwannin Mai a ranar Lititin data wuce, sun tsaya da kafar su, a wannan watan sabanin satin da ya wuce, sakamakon, yawan hako Mai da kasar Amuka ta yi haka Matatun Mai, sun ci gaba da aiki bayan aukuwar Guguwar Matsanciyar isakar nan da ake mata lakabi da ‘Hurricane Harbey’ ta yi barna a kasar.
A wani hasashe da aka fitar na Danyen Mai a kasar ta Amurka, ya nun cewar Danyen Mai tsaya akan Dalar Amuka 50.0 akan ko wacce Ganga a karfe daya na Agogon 0547 GMT,kashi hamsin inda ya kusa da fiye da watanni uku na sama da na Alhamis din da ta wuce.
Bugu da kari, wani hasashen na kudin Mai a wajen Kasar ta Amurka, ya nuna cewar, kudin Mai ya kai Dalar Amurka 55.71 na Gangar Mai har zuwa kashi tara, wanda ba yi nisa da kusan watanni biyar da ya haura da Dalar Amurka har zuwa 55.99 a ranar Alhamis da ta gaba ta, inda kuma aka sai da Man Brent akan Dalar Amurka hamsin da shida a ranar Larabar
da ta wuce.
Bankin ANZ a ranar Litinin din da ta wuce yace, a bisa bukata daga Hukumar Mai ta duniya wato OPEC da kuma IEF sun ci gaba da ce-ce kuce a kasuwar Mai, haka Matatun Mai sun ci gaba da gudanar da ayyukan su bayan ta’adin da matsaninan ciyar iskar ta janyo a kasar.
Matatar Mai ta Royal Dutch dake jihar Tedas, tana daya daga cikin Matatun Mai dake kan ga ba wajen fara aiki a ranar Lahadin da ta wuce, inda a yanzu Matatar zata iya fara sarrafa Gangar Mai har na 325,700 a ko wacce rana.
Sake fara ci gaban Matatun Man, ya faru ne akan alamar ci gaba na Masana’antar Sahele dake Kasar ta Amurka.
Bankin na ANZ ya bayyana cewar, a satin da ya ganbata ne, harkokin
hakar Mai a kasar ta Amurka, su ja da baya matuka.
Kamfanin ‘Baker Hughes’ ya bayyana cewa, wasu Kamfanoni a kasar ta Amurka sun yanke hakar Mai a ranar sha biyar ga watan Satumbar wannan shekarar, inda aka samu jimlar ragi ta 749, wanda shine mafi karanci tun daga watan Yuni.