Daga CRI Hausa
Wani kwararre mai nazarin harkokin kasar Sin, Robert Lawrence Kuhn, kuma shugaban gidauniyar Kuhn, ya ce batun kiyaye muhalli na da matukar muhimmanci ga shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 da kuma burin da kasar Sin take son cimmawa kafin shekarar 2035, a lokacin da take da niyyar zama kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu dake da karfin demokradiyya da al’adu da kuma ci gaba.
Yayin taron kwamitin zurfafa gyare-gyare na kwamitin tsakiya na JKS na baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya batun kiyaye muhalli cikin muhimman bangarorin gyare-gyare 4 da za a mayar da hankali kansu a shekarar 2021.
A cewar Robert Kuhn, wata mahanga ta hango burin Sin na kiyaye muhalli ita ce, sabbin dabaru raya kasa, dake ingiza shirin shekaru biyar-biyar karo na 14, inda aka sanya batun kiyaye muhalli a matsayi na 3 cikin jerin batutuwa 5.
Ya ce zuwa 2025, burin Sin shi ne, ci gaban masana’antu masu kiyaye muhalli da ci gaba da rage abubuwan dake gurbata muhalli da rage fitar da sinadarin carbon da bunkasa tsarukan masana’antu da makamashi da sufuri da kuma inganta samar da kayayyakin more rayuwa da suka dace da kiyaye muhalli. Zuwa shekarar 2035 kuma, karfin amfani da makamashi da albarkatu a muhimman masana’antu da kayayyakin ya kai mizanin na duniya. (Fa’iza Mustapha)