Connect with us

WASANNI

Klopp Na Son Chelsea Ta Doke Manchester City A Wasansu Na Gaba

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na bukatar alfarma daga Manchester City kafin lashe kofin gasar firimiyar Ingila a karon farko cikin shekaru 30 cikin wannan mako bayan ta yi canjaras babu ci tsakaninta da Eberton a karawar da suka yi a bayan-fage a ranar Lahadin data gabata.

Kadan ya rage Eberton ta sauya sakamakon wasan, ya yin da kwallon Tom Dabies ta daki karfe, sannan kuma mai tsaron ragar Liverpool, Alisson Berker ya kade kwallon Dominic Calbert-Lewin, lamarin da ya hana Eberton samun nasarar doke Liverpool a karon farko cikin shekaru 10.
Liverpool dai ta buga wasan ne ba tare da nuna karsashin da aka san ‘yan wasanta da shi ba koda yake har yanzu kungiyar na da damar lashe gasar firmiyar ta Ingila, lura da tazarar maki 23 da ta bai wa Manchester City a teburin gasar.
Yanzu haka watakila Liverpool ta dage kofin a ranar Laraba mai zuwa a gidanta, inda za ta fafata da Crystal Palace, amma da shardin cewa, sai Manchester City ta yi barin maki a karawar da za ta yi da Chelsea  a wasanta na gaba.
A bangare guda kocin Liverpool Jurgen Kloop ya jinjina wa mai tsaron raga, Alisson Berker bisa namijin kokarinsa wajen hana kwallaye shiga cikin ragar kungiyar a yayin wasan na hamayya wanda yake da tarihi sosai.
Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa yana fatan Chelsea ta samu nasara akan Manchester City a wasan da zasu fafata wanda hakan zai bawa Liverpool din damar lashe firimiyar tun kafin a kammala wasannin na bana.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: