Abba Ibrahim Wada" />

Klopp Ya Jinjina Wa Allison Bayan Wasan Manchester

Allison

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Jurgen Klopp, ya jinjinawa mai tsaron ragar kungiyar, Allisn Becker sakamakon kokarin da yayi a fafatawar da sukayi da Manchester United a filin wasa na Anfield a ranar Lahadin data gabata.

Sai dai duk da haka Manchester United ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar Premier Ingila da maki uku a kan Liberpool dake rike da kambun gasar, bayan canjaras din da sukayi da ita, to sai dai jarumtakar da mai tsaron ragar Liberpool Alisson Becker ya nuna ya hanata gagarumin nasara da ya bayyana a Anfield.

Liberpool ta ci gaba da kasancewa ta hudu a kan teburi, bayan da ta gaza yin nasara a wasanni uku a jere na gasar, amma ta na mai jinjina ga Allison dan kasar Brazil da tsawaita wasanni 68 wanda ta buga a gida ba tare da an doke ta ba a gasar Premier, bayan da ya hana Bruno Fernandes da Paul Pogba harin da sukayi ta kaiwa.

“Tabbas Allison mai tsaron raga ne wanda yasan abinda yakeyi kuma yake da kwazo domin ya nuna kuma kowa yaga abinda yayi a shekarun baya da kuma wannan shekarar hakan yasa dole ne mu jinjina masa” in ji Klopp

Manchester United ma dai ta buga wasanni 12 ba a doke ta ba a gasar ta firimiya wanda hakan yasa yanzu take zaune a mataki na daya akan teburin da maki 36 sai Manchester City a mataki na biyu.

Exit mobile version