Connect with us

WASANNI

Klopp Ya Lashe Kyautar Gwarzon Kociyan Firimiyar Ingila

Published

on

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Jurgen Klopp ne ya lashe kyautar gwarzon mai horarwa a gasar Firimiyar Ingila, kyautar da kungiyar masu horarwa ta gasar ke bayarwa duk shekara.

Tawagar Klopp ta lashe kofin gasar Firimiya a bana, a karon farko cikin shekaru 30 wanda hakan yasa ya kasance babu mai koyarwar da yayi abin kirkin da yayi duba da irin tarihin shekara 30 daya karya a gasar ta firimiya.
A bangaren masu horar da mata ‘yan wasan tamola kuwa, Emma Hayes ce ta lashe wannan kyauta, bayan da ya jagoranci tawagar mata ta kungiyar Chelsea zuwa ga lashe kofin kalubale na mata a wannan kaka.
A bangaren gasar da ke bi da Firimiya kuwa, wato Championship, kocin kungiyar kwallon kafa ta Leeds United, Marcelo Bielsa ne ya ci wannan kyauta, sakamakon jagorantar tawagarsa zuwa samun shiga gasar Firimiyar Ingila.
Publicité
Da yake sanar da kocin da ya lashe kyautar gwarzon mai horarwa a gasar Firimiyar Ingila ta tashar Sky Sports, kuma tsohon kocin Manchester United Sir Aled ya ce lallai Klopp ya cancanci kyautar.
Advertisement

labarai