Connect with us

KIWON LAFIYA

Ko A Na Iya Gane Aikin Kwakwalwar Matattu?  

Published

on

Marasa lafiya gaskiya ne suna nan a cikin irin wani hali na  rashin sanin inda kansu yake, ko kuma ana iya kiran shi al’amarin na rai kwakwai, mutu kuma kwakwai, abin dai ya kasance kala wa kala ke nan, ko kuma ta wani bangaren babu tabbas, wato na (tsakanin rayuwa da kuma mutuwa).

Su kuwa manyan masana ilmin kimiyya uku kokarine suke yi na ceto su, kamar yadda Roger ya kawo rahotanni akan yadda su al’amuran suke.

Adrian Owen ya bayyana cewar” Kama kaddara cewar ka farka ko kuma aka tashi ne a cikin wani akwati”.

Sai ya kuma ci gaba da karin bayani inda kuma a wannan lokacin sai ya ce ” kamar dai ka ji garau wato sarai tun daga kan ‘yan yatsun hannuwan ka ya zuwa ‘yan yatsun kafa.  Na san cewar kamar dai ya yi kokarin yin karin haske shi wannan al’amarin ba zai yi maka dadi ba, dalili kuwa kana dai cikin akwati kana kuma dukkan na al’amuran da ake yi a kewaye da kai, amma kuma sai dai wani abu daban wanda kuma shine ba za a iya jin muryar ka ba.

Amma kuma maganar gaskiya ita ce shi akwatin da aka sa shi mutumin daure yake, wanda kuma ba karamin dauri bane tare da fuskarka da lebanta ta yadda ma kai ba yadda za ka iya yin wata magana ba ko kuma yin wani surutu.

Da farko, wannan al’amari ya yi kama da wasa. Sai batu na gaskiya. Kana gani da jin yadda ‘yan uwanka ke alhinin makomar da ka samu kanka. Ka daskare cikin sanyi.

Sai ka ji kuma ka kasance a cikin wani yanayi na zafi. Kuma koda wanne lokaci da yaushe kana fama da matukar bukatar ziyarar ‘yan uwa da kuma abokan ka al’amarin da kuma ba makawa sai ya ragu. Abokin da kuke zama tare shi ma sai ya bari. Kai ma dai ka san babu wani abin da zaka iya yi dangane da shi wannan halin da kake ciki.”

Shi kuwa Owen ya bayyana cewar suna tattaunawa ta kafar sadarwa ta Skyoe.  Kuma har yanzu yana nan Landan wanda kuma ta kasance babban birni ne Landan, ta kasar Birtaniya, shi ma dai yana can a Landan wadda take da kimnanin mil dubu uku da rabi daga Jami’ar Western Ontariodake can  kasar Canada.

Yadda shi jan gashin Owen da gemunsa wadanda kuma aka daddatse su, tuni suka bayyana akan shi akwatin talabijin dina, inda aka zayyana ma shi ita irin siffar sa tare da kwatanta ma shi yadda wadanda ba sa iya yin magana ke shan azaba: wato su marasa lafiyar da yake kula da su.

Su mutanen da “rashin lafiyar ta mayar da su gasu – gasu nan dai” saboda kuwa a farke suke amma luma ba tare da sanin su ba.  Hattana ma Idanun su suna bude har a wasu lokutan ma su kan jujjuya.

Suna iya yin murmushi, su ma har kama hannun wani, su yi kuka ko kuma gyaran murya ta. Sai dai wani abu shi ne motsin tafa hannu bai dame su ba, ba sa iya gani ko fahimtar wata magana.

Motsinsu ba da wata niyya ko kuma manufa ya ke kasancewa ba, sai dai kwatsam ya zama an yi shi. Alamu kuma suna nuna abin da yake damfare a kwakwalwarsu bai da wani cikakken amfani, babu wata sosuwar zuciya ko a dauri wata niyya, wasu dabi’u da suka ta’allaka a jikin wasu daga cikin mu.

Ga kuma shi tunanin nasu wanda shi ma a tauyaye yake matuka. Har yanzu dai, idan idanun su suka bude, sai kuma a kasance cikin wani hali na mamakin cewa akwai wata ‘yar alamar farkawa tare da su.

Shekaru goma da suka gabata, amsar tambaya akan shi al’amarin kawai ba a bukatarta ko kuma a ce kawai a’a! Kada a sake kasancewa a cikin hakan da ita ko kadan, ta hanyar amfani da na’urar daukar hoton bibiyar kwakwalwa, Owen ya gano cewa wasu kawai a suna cikin halin da aka yi masukamar wani tarnaki, suke a daure cikin jikinsu, duk da haka suna iya yin tunani har su dan ji wani abu wannan kuma ya kasance ne da irin halin da suke.

Yawan wadanda suke fama da rashin lafiya, ko dai wata matsala ta kasa farfadowa suna karuwa a shekrun nan, wani abin mamakin kuma shi ne likitoci sun samu dabarun ceto marasa lafiyar da suka samu munanan raunuka.

A yau, majiyatan da jikinsu ke dabaibaye da jagwabewa da tsukewar kwakwalwa sun cika asibitoci masu yawa a fadin duniya -a  nahiyar Turai kadai yawan wadanda su kan kasance a cikin irin wannan yanayi, suna da yawa amma  a  some sun kai misalin kimanin 230,000 a kowace shekarta, inda daga cikinsu 30,00 ke kasancewa a yanayin lankwamewa.

Irin wadannan su ne wadanda suka fi shiga matsanancin hali, inda ake matukar kulawa dasu da na’urorin kula da lafiya na zamani masu tsada. Owen na da matukar fahimtar shi al’amarin.

A shekarar 1997, wata kawarsa wadda kuma ta kusa da shi ce, ta ta shi yadda ta saba ta hau keke don zuwa wajen aiki. Anne (wadda aka canza sunan ta) ta samu nakasa ne a magudanar jininta da ke kaiwa ga kokon kai, wadda aka sani da raunannar jijiyar jinin kwakwalwa.

Sai ga shi cikin minti biyar da fara tafiyarta, sai ita jijiyar makwararar jininta ta fashe, inda nan take ta yi karo da wata bishiya. Daga nan kuma fa ba ta sake farfadowa ba.

Hotunan mutane da ke somewa a fina-finai irin su Hable con Ella (wasan kwaikwayon mutanen Spain da ke nufin yi mata magana) wani al’amari ne wanda ya kaucewa tabbatacciyar gaskiya.

Wannan masifa ta sa Owen ya shiga wani zurfin tunani, ta yadda hadarin Anne ya kawo masa wani canji a tsawon rayuwar sa.

Daga nan fa sai kuma ya fara jefa alamar tambaya akan marasa lafiyar da ke cikin matsananciyar suma da kuma wadanda sumar tasu ba ta kai kamari ba, da kuma wadanda suka samu kansu a tsakanin al’amuran biyu (matsanaciya da sassaukar suma)?

A wannan shekarar ce kuma sai ya koma Cibiyar binciken Likitanci da ke nazarin fannoni kimiyyar kwakwalwa a jami’ar Cambridge, inda masu bincike suka yi amfani da dabarun daukar hotuna daban-daban.

Daya daga cikin dabarun mai lakabin PET na nuna yadda ita kwakwalwar ke gabatar da ayyukanta, wadanda kuma suka hada da amfani da iskar odygen da kuma sarrafa sikari.

Sai kuma dayar dabarar wadda take da taken fMRI na nuna sassan kwakwalwa da ke aiki ta hanyar gano dishi-dishin jini da ke kwarara da yawa. Owen ya cika da tunanin yin amfani da wannan fasahar kere-kere ga majiyata, irin kawarsa da ke halin rai kwakwai, mutu kwakwai.

 

Kudurin Farfadowa:

Tsawon rabin karnin da ya wuce, idan zuciyarka ta daina bugawa nan da nan kuma sai a tabbatar da mutuwarka, ko da kuwa dukkan jikinka yana farke sai kawai likitoci su kai ka wurin da ake ajiye ko kuma kula da gawa wato (macuware).

Shi irin wannan al’amarin shi ne wanda ya nuna cewar a tarihi an sha samun wadanda “suka mutu, suka kuma farfado.”

Kamar dai yadda shi wannan al’amarin ya taba faruwa a cikin shekarar 2011, inda a majalisar lardin Malatya da ke tsakiyar kasar Turkiyya ta ba da sanarwar kera macuware mai narkakawa da kofofin sanyaya gawa da a ke iya bude su daga ciki.

Sai dai kuma matsalar dai ita ce har yanzu ma’anar da ita kimiyya ta ba wa “mutuwa” ba a cimma wata matsaya a kanta ba, tamkar yadda farkawa ta ke ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: