Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ko Akwai Yiyuwar Katse Hulda Tsakanin Sin Da Amurka?

Published

on

Kwanan baya gwamnatin Amurka ta bayyana cewa, za ta yanke hukunci kan kuduri game da katse huldar dake tsakaninta da kasar Sin daga duk fannoni, amma a sa’i daya kuma, wani babban jami’in kasar mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya ya furta cewa, ba zai yiyu ba a katse huldar dake tsakanin sassan biyu a bangaren tattalin arziki. Hakika masana tattalin arziki da kafofin watsa labarai na kasa da kasa da dama suna ganin cewa, ba mai yiyuwa ba ne a katse hulda tsakanin Sin da Amurka, ana wadannan tsokacin ne domin biyan bukatun yin takara a babban zaben da za a gudanar a kasar.

Farfesa Henry Farrell na jami’ar George Washington da farfesa Abraham Newman na jami’ar Georgetown na Amurka sun wallafa wani rahoto mai taken “Matakin katse hulda da kasar Sin da bai dace ba da aka dauka” a shafin yanar gizo na mujallar harkokin kasashen waje wato Foreign Affairs ta kasar cikin hadin gwiwa, inda suka yi nuni da cewa, idan Amurka ta katse huldar tattalin arziki da kasar Sin ba zata, hakan zai yi lalata huldar tattalin arzikin dake tsakanin sassan biyu, kuma zai katse huldar tattalin arzikin dake tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya.
Jaridar Wall Street Journal ita ma ta gabatar da wani rahoto a kwanakin baya bayan nan, inda aka bayyana cewa, duk da cewa, kasashen na yiwa juna shisshigi a harkokin tattalin arziki da cinikayya, amma adadin cinikayyar dake tsakanin sassan biyu a watan Aflilun da ya gabata ya kai dala biliyan 39.7, adadin da ya karu da kaso 43 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Fabrairun bana, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta sake kasancewa kasa mafi girma wadda take gudanar da cinikayya da Amurka a fadin duniya, hakan ya sake shaida cewa, ba zai yiyu ba su katse huldar tattalin arziki a tsakaninsu.
Kana ‘yan siyasar Amurka suna kokarin shawo kan kamfanonin Amurka domin su janye daga kasar Sin su komo kasarsu, amma kamfanonin Amurka suna ci gaba da zuba jari a kasar Sin, saboda sun gano cewa, idan sun bar kasar Sin, za su bar babbar kasuwa mai boyayyen karfi na kasar Sin.
Rukunin Rhodium na Amurka ya taba fitar da wani rahoto a kwanan baya, inda aka bayyana cewa, a cikin watanni 18 da suka gabata, an fi nuna kuzari wajen zuba jari a kasar Sin, abin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru goma da suka wuce.
Hakazalika shugaban kasar Sin ya gabatar da wani jawabi yayin taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya da aka kira ta kafar bidiyo, inda ya jaddada cewa, ko a fannin dakile annobar cutar COVID-19, ko a fannin farfado da tattalin arziki, ya dace a hada kai, haka kuma a gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, tsokacin da ya yi ya kara karfafa wa al’ummun kasa da kasa gwiwa yayin da suke kokarin kandagarkin annobar da kuma raya tattalin arziki, haka kuma ya kara karfin imanin al’ummun kasa da kasa kan makomar tattalin arzikin kasar Sin.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Advertisement

labarai