Ko Dai An Ba Shugabanni Kwangilar Rashin Tsaro Ne A Arewa? -Shugaban Matasan Arewa A Kudu  

Arewa

Ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azza a Arewa, Shugaban Matasan ‘Yan Arewa mazauna Legas, Ibrahim Ya’u Galadanchi ya kafa alamar tambaya kan cewa ko dai an ba shugabannin da ke madafun iko ne a kasar nan kwangilar haifar da rashin tsaro a Arewa?

Sakamakon wannan tambaya, ya jawo hankalin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan yadda yankin Arewa ke ci gaba da zama kufai bisa yadda ‘yan bindaga da masu garkuwa da mutane suke baje kolinsu.

A cewar Ibrahim Galadanci, babu shakka girman matsalar tsaro na ci gaba da gasa wa jama’a gyada a tafin hannu, kuma hakan ya sa fushin jama’ar yankin Arewacin kasar nan ya fara bayyana karara.

Yanzu haka dai hankulan mafi yawan mutanen yankin a tashe suke, da alamu kuma an kai su bango dangane da yadda matsalar ta tsaro ke matukar ci masu tuwo a kwarya.

A wasu lokuta da suka gabata, bayan munanan hare-hare na baya-bayan nan a Arewacin Nijeriya, Kungiyar Dattawan Arewacin NIjeriya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga mukaminsa saboda yadda yanayin tsaron kasar ke ta ci gaba da tabarbarewa.

Kungiyar ta Arewa ta ce shi kansa Shugaba Buhari ya taba cewa shugaban da ya gada wato Goodluck Jonathan ya yi murabus saboda matsalar tsaro a wancan lokacin, saboda haka shi ma tun da yanzu ya gaza, to ya sauka.

Dattawan na Arewa sun ce Buhari bai da wani zabi illa kawai ya yi murabus ganin ya gaza sauke amanar da ya dauka musamman a halin da kasar ta sami kanta a halin yanzu na tabarbarewar tsaro.

Shugaban matasan ya ce, “To ni a nan ba na ba shi shawarar ya sauka, amma ina bukatar ya dauki matakin gaggawa, domin idan ya sauka ba mu san abun da zai faru ba nan gaba. Kuma ya zama wajibi a rika hukunta duk wadanda aka kama a bainar jama’a, domin ya zama izina ga ‘yan baya.

Galadanchi ya kara da cewa ya kamata Shugaba Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda kuma a samar da doka kan duk wanda aka kama da laifin garkuwa zai fuskanci hukunci kisa ko daurin rai da rai a gidan yari.

Ya ci gaba da cewa ya kamata a bai wa Mangunu wata uku ko dai ya kawo karshen matsalar tsaro a Arewa ko ya sauka daga mukanminsa.

ya yi kira da matsasa su shirya zanga-zangar guda miliyan biyu domin nuna fushin bisa abubuwan da suke faruwa.

Hakazalika, ya bukaci a hukunta tsafaffin ministoci da Buhari ya sauke a kwanan nan, Sabo Nanono da Saleh Maman da kuma dukkan ministocin gwamnatin tarayya na yanzu. Kuma bukaci Shugaba Buhari ya kara nada dan asalin Jihar Kano a matsayin minista, domin jihar ta masa rana fiye da sauran jihohin kasar nan.

 

 

Exit mobile version