MALAM ABDULLAHI MUHAMMAD TAHIR, Shi ne shugaban cibiyar nan na horar da kangararrun mutane mai suna ‘Malam Kawo Rehabilitation’ da ke titin Yakubu Wanka a cikin garin Bauchi. walau yara ne ko manya. Allah ya ba shi baiwar da sirrukun gyara wa kangararru halayensu domin su zama na kwarai, daga kan ‘yan shaye-shaye, fitinannu, ɓarayi, da waɗanda suka fi ƙarfin iyayensu. Dukkaninsu Malam Kawo na iya sarrafa su ya kuma daidaita su, su zama mutane kwarai. A bisa haka ne wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ya yi mana hirar musamman da shi domin jin yadda ya ke yi. Ga hirar kamar haka:
Ka gabatar mana da kanka..?
Bismillahir Rahmahnir Rahim….! Sunana Abdullahi Muhammad Tahir, shugaban cibiyar gyara tarbiyyar Kangararrun mutane mai suna ‘Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphans Center’ da ke titin Yakubu Wanka a nan cikin garin Bauchi. kuma ni ne sarkin Malaman Kagadaman Dass, har-wala yau ni ne sarkin Hausawan ƙaramar hukumar Dass. Haka zalika ni ne sarkin Malaman masu maganin gargajiya na Jihar Bauchi.
Wannan cibiyar tamu ta Malam Kawo Rehabilitation tana gudanar da ayyuka da daman gaske. Na farko dai shi ne muna karantar da yara ƙanana na ɓangaren allo, Islamiyya da kuma na boko. Haka kuma mu kan kai wasu yaran da suke wannan cibiyar koyon sana’a amma ya danganta da yanayin yaro. Aikinmu na biyu kuma shi ne muna kula da marayu, domin a yanzu haka muna da marayu da marasa galihu da daman gaske a nan cibiyar. Daga cikin abubuwan da muke yi, akan samu wasu ɗaiɗaikun mutane da suke zuwa neman taimako ka santuwar muna taimaka wa gajiyayu da masu cututtuka da dai sauran taimakon jin ƙai, duk muna yi a wannan cibiyar.
Ko za ka yi mana ƙarin bayani dangane da wannan cibiyar taka?
Wannan cibiyar, mun kafata ne a shekara ta 2002, mun kuma fara tafiya da ɗalibai 10. A lokacin ɗalibai kawai muke koyarwa, domin a lokacin ba mu fara taimaka wajen magance kangararru domin basu tarbiyya ba. na kuma fara wannan koyarwar ne tun a cikin gidana, har na gangaro jama’a suka fara turo min ‘ya’yansu dai tafiya-ta yi tafiya har muka fara fitowa kofar gida, jama’a suka fara kawo mana kangararrun yaransu muna kula da su. Yara ƙanana za ka samesu su ba, baligai ba, amma sun ƙi boko sun kuma ƙi karatun addini babu kuma wanda ya isa da su, idan an kaisu wajen sana’o’i ba za su yi ba; wasu kuma ma har da ɗauke-ɗauke ko ma shaye-shaye, duk mu kan basu tarbiyya, tun muna kula da yara har aka zo aka fara kawo mana manya muna lura da su. Matakin farko kangararrun yaran basu da yawa na ke amsa, ko an kawo min sai na ce sai na sallami waɗanda suke hanu na, bayan da jama’a suka sanni sosai sai ya zama zuwan yana yawa kullum jama’a suna kawo yaransu da suka zama musu ƙarfen ƙafa, yanzu haka mun tarbiyyantar da kangararru bila-adadin, kuma yanzu da muke hira da kai ɗin nan ma akwai yara da suka fi ƙarfin iyayensu wato kangarru da dama wanda na ke kan kula da su a halin yanzu.
Ko akwai wasu nasarorin da ka iya cimmawa daga 2002 zuwa yau a wannan sa’ayin naka?
Babban nasarar da na samu a kan wannan aikin nawa shi ne, akwai wasu waɗanda an fitar da rai dangane da shiriyarsu, har su dawo su yi rayuwa daidai irin na al’umma, an kaisu makarantu da dama sun ƙi yi, wasu an kaisu makarantu irin wannan na cikin gida da waje amma sun ƙarara. Cikin har dar Allah mun zo mun tsaya mun yi musu magani sun saitu, sun dawo cikin haiyacinsu yanzu haka daga cikin yaran da na nutsar akwai waɗanda suna karatu a ƙasashen waje, akwai kuma waɗanda yanzu haka suna cikin jami’o’in ƙasar nan suna karatunsu amma da hakan ya gagara, wasu kuma sun kama sana’o’insu suna kai wannan shi ne babbar nasarata, na iya shiryar da kangararrun da iyayensu suka cire tsammanin za su dawo haihaucinsu. Manufarmu ke nan mu gyara wa mutumin da ya yi daban da mutane halinsa ya zuwa ya dawo cikin mutane domin ya ci gaba da tafiyar da rayuwarsa kamar yadda ya dace. Bayan haka kuma, a cikin yaran da na gyara musu halinsu, akwai waɗanda sun kware sosai kan sana’o’I, yanzu haka ina da yaran da sun kware sosai wajen haɗa allunan talla, da zanen jikinsu, muna da teloli, akwai masu aikin ofis, muna kuma da injiniyoyi dukka a ƙarƙashina suka dawo cikin haiyacinsu har su ka zo suna iya taɓuka wasu abubuwan amfani wannan babbar nasarace a gare ni.
Muna bin hanyoyi ne na almajiranci. Akwai addu’o’in da na ke yi ne, idan Allah ya zaɓeka ya ce kai za ka yi kaza wannan ba wayonka ne ba ko kuma dabarar ka bane. Ni karan kaina abun na bani mamaki, a faɗin garin manyan mutanen cikin garin nan ɗaiɗai ne waɗanda basu kawo min ‘ya’yayensu da suka gagaresu ba. cikin ikon Allah za ka ga an kawo mutum a ɗaure, wani ma sojoji ne za su kawo mana shi nan, wasu ‘yan sanda, wasu ‘yan kwamiti wasu ‘yan banga wasu iyayensu da dai sauransu za a kawo mutum ya hana mutanen unguwa sakewa ya zama kangararre ya hana dangi da ‘yan uwa zaman lafiya, wani ma sai ka ji ya ce zai kashe wasu, amma cikin ikon Allah ana bani yaro, da zarar na samu waje na ajiye shi sai ka ga an samu canji sosai. Alal haƙiƙa addu’o’I ne na ke yi da wasu ‘yan abubuwa a cikin dare da na ke yi idan na yi sujjadar sallah, sai a faɗa min ga abun da zan yi, sai a faɗa wa zuciyata, kuma ba wai jinno bane, kawai zan ji abun ne ya zo cikin zuciyata. Abun da kawai zan ce maka wata baiwace da Allah ya taimakeni da ita, domin ni da ka ganni bana dokan yaro ko kaɗan, wasu daga cikin cibiyoyin shiryar da kangararru za ka tarar ana dukan mutum domin dole ya canza halinsa ko ya yi abun da ake son ya yi, amma ni cikin ikon Allah bana dukan yaro ko sau ɗaya. Cikin ikon Allah za ka samu duk takerancin yaro muna zaune da shi a nan lafiya kuma yana yin dukanin abun da ake buƙatar ya yi.
Ke nan kana nufin duk tagayyarancin mutum ba sai ka dukashi ba kuma zai shiryu?
A wannan cibiyar tawa, matuƙar ka ga an daki mutum ko yaro abu guda ne kacal zai sanya bugeshi. Na ɗaya idan muka nemi yaro ya yi sallah a lokuta biyar ɗin nan ya ce ba zai yi sallah ba, ko kuma ba zai sha magani ba, ko ya ce shi ba zai yi abubuwan da muke buƙata ba. kai bamu ma taɓa samun makamancin hakan ba cikin ikon Allah. A cikin gida kuma inda na ke ajiye yaran, akwai dokokin gidan, kamar yadda Allah ya ce ko tafiya za ku yi ku nemi shugaba a tsakaninku. A cikin gidan akwai sarkin gida, akwai sarkin ɗaki, kowacce ɗaki akwai sarkinta da kuma mataimakin sarkin.
Daga ranar da aka kawo ka ga dokoki nan a jere za ka gani. Na farko dai mu babu faɗa, na biyu za ka yi addini, na uku babba ba zai je ɗakin yara ba, na huɗu yara ba su zuwa ɗakin manya, na biyar mutum biyu ba za su shiga bayan gida tare ba; na shida mutum biyu ba za su shiga cikin mayafi (bargo) guda ɗaya ba, na bakwai duk ranar da muka samu wani ya ce zai kusanci ɗan uwansa na miji mu kan ce hukuncinsa kisa ne. babu ruwanmu domin nan gidan, gida ne na gyaran tarbiyya kuma gida ne na almajirai, gidane kuma na addini. dole ne wanda ya ke gidan nan ya hawaita Istigfari, kuma daga cikin dokokin gidan mun haramta mutum ya ke taɗi ko bada labarin abubuwan da yake yi a baya can.
Ta wasu hanyoyi ka ke samun kuɗaɗen gudanar da wannan cibiyar?
Muna da cikakkun izininmu daga gwamnati. Ni dama can almajiri ne, daman shi almajiri ya kan kasance mai yin addu’a ma wasu kan wasu buƙatunsu daga bisani su baiwa mutum ɗan abun sadaka. Bayan haka ina da yara da suke sana’o’I suna taimaka ma wannan cibiyar sosai. Kafin na zo i-yau ni ɗin nan ɗan kasuwa ne, a da ina da shanu har uku santaran maket, amma a dalilin wannan cibiyar kayan shagona sun ƙare na saida shagunan, da ina da mota da mashin duk na saida su dukka a dalilin wannan cibiyar. A da baya can lokacin da na ke da hali idan an kawo yara bana faɗin abun da za a bani, sai dai duk abun da mutum ya kalato ya miƙo na kan amsa.
Bana noma amma kullum za mu ci abinci da ni da yaran da suke nan makarantar, ina rokon Allah ne kan ya zama mai taimakonmu wajen ciyar da yara nan. Amma da tafiya ta yi nisa, yara suka min yawa, idan an kawo min almajirai, ko marayu da marasa galihu ba na cewa komai. amma idan an kawo min ɓarayi, masu shaye-shaye da sauran waɗanda suka zama kangararru su mu kan bada form ne a cika, muna kuma rijista domin samun wani tallafin haraji. Wannan dai sune hanyoyin da muke tafiyar da wannan cibiyar.
Wasu tsari ku ke bi wajen ilmantar da yaran da suke hanunku?
Ke nan har da kangararrun wasu jahohi ake kawo maka?
Tabbas, a cikin yara ƙananan ina da yara daga Jos akwai yaran Neja, Gwambe da Kano waɗanda aka kawo min su domin na tarbiyyatar da su, a manya kuma kangararrun da suke hanuna akwai na Legas, akwai na Fatakul, Kaduna, Gombe na sallami na wasu daga Adamawa sakamakon sun shiriya, muna da manyan kangararru daga Gombe da Kano, Abuja da kuma irin su Maraban Yanya a halin yanzu waɗanda dukka muna basu kulawa wajen ganin sun dawo mutanen kwarai. Haka kuma a ƙananan hukumomin nan 20 na jihar Bauchi ina ganin ƙananan hukumomi 3 ne kacal babu wasu yaran da aka kawo min domin na risina su.
Daf da za ka zo wannan wajen, yau kafin mu je sallar juma’a wani mutum bafulatani ya zo tun daga Marar Raban Burku, kusa da Yanya na Abuja inda ya zo kan maganar yaronsa ɗan shekara 19 yana shaye-shaye ya na kuma sata ya rasa yadda zai yi da shi, shi ne ya samu labarina don haka ya zo domin mu yi ƙoƙarin shawo masa kan ɗansa da ya zama kangararre a cikin al’umma.
Kana da wani shiri na taimakawa ta fuskacin matan nan ne?
Eh zan iya samu wannan damar, kuma abu ne mai sauƙi da zarar gwamnati ta taimaka mana da muhallin da zan keɓe na mata na musamman. Mu samar musu da matan da za su ke kula da su. Wasu daga asibiti a zo da su sun ƙi, a kawo su wajen masu ruƙiya sai a zo a ce min zan iya kuwa, da zarar kuma aka bamu dama sai ka ji cikin ikon Allah mun samu bakin zaren magance matsalar.
Ko kuna fuskantar wasu ƙalubale a wannan cibiyar taku?
Gaskiya ƙalubale suna da tarin yawa, sau tarin lokaci akan zo a ce mani shinkafar da ta yi saura ba za ta kai abincin da za a ci na yau ba. na fa wai na gobe ba. a yau da muke hira da kai ma na tashi da safe aka ce sam shinkafar da take ƙasa ba za ta kainmu abincin yau ba; dubu ashirin kacal a jikina na ɗauka na bayar aka sayo shinkafa kafin zuwanka nan aka shiga da ita. Buhun nan kwana uku kacan za ta yi mana. sannan muna da matsalar muhalli, duk da girman nan wajen amma ya kamasa mana, yanzu idan da za mu shiga da kai za ka ga yaran da muke da su, sun mammatsu, irin waɗannan cibiyar kuma bai kamata a ce ana samun cinkoso ba. kuma akwai yanayin gine-gine da ake buƙata a irin wannan cibiyar. Bayan nan kuma, kamar irina da na ke shirya da kowani irin kangararre, akwai ɓarayin da akan kawo sun a gyarasu, wasu ɓarayin da suke waje suna jin haushin ina gyara mambobinsu, haka masu shaye-shaye ma suna jin haushin ina daidita kwakwalwar mambobinsu, masu ɗaure wa ɓarayin ma gindi da abokansu duk suna jin haushin na ɗaure musu mutane. Akwai lokacin da ‘yan sara kusan su 70 da makamai suka zo nan suka ce wai sun zo wajena ne basu yarda da abun da na ke yi ba, domin duk wanda aka kawo daga cikin abokansu ina hanasa shaƙatawa wannan ba daidai bane. wannan dalilin irinsu da yawa, amma a ce maka duk inda zan je sai na hau acaɓa ka ga wannan babbar matsalace a gareni ƙalubale ta fuskacin tsaro. Sannan ƙalubane akwai waɗanda suke koyar da yaran nan ina biyansu albashi, mai wanke-wanke ana biyansa akwai ƙalubale sosai. Ni na rike ‘ya’yan manya-manya a ƙasai nan amma har yau babu wani wanda ya ce bari ya tuna da ni tun da na shiryar masa da yara.
Ko kana da wasu kira ga gwamnati ko wasu ƙungiyoyi?
Ina kira ga ‘yan jaridu a farko da suke tallafa wa irin cibiyoyin nan namu, domin kowa ya san gudunmawar ‘yan jarida a duniya. Sannan ga gwamnatin tarayya ina kira tare ta da ta sani ayyukan da muke yin a taimaka wa mutanenta wani sashi ne na haƙƙin da ke kanta muka ɗauke mata, don haka da buƙatar gwamnatin tarayya take la’akari da gudunmawar da irin gudunmawar da muke bayarwa ta kuma taimaka mana, taimakon da ya dace. Ga ita kuma gwamnatin jiha gaskiya tana taimakawa amma taimakon yana kasawa sosai, domin hidimar nan fa na al’umma ne baki ɗaya, idan mutane suka zama sun samu matsala na taɓarɓarewar tarbiyya al’ummar ma fa ba za ta zauna lafiya ba. don haka taimakon da muke tsayawa muke bayarwa ya kamata ake la’akari da su ana yi mana abubuwan da suka dace.
Ina son yin noma amma babu yadda zan yi na yi noman, yau idan na je yin noma aka zo nema na a lokacin da na je noman nan ka ga da matsala. Sannan dukka a wannan satan, muna samun matsala na rashin lafiya na yaranmu dukka ka ga kuɗi ne yake yinsu.
Tambayarmu ta ƙarshe Mal. Kawo, ka san rayuwa dole akwai mutuwa a cikinta. Shin kana da wani shiri ne na koyar da wani wannan sirrin naka ko da bayanka ne a ci gaba da amfana da kai?
Ina son wanda zai gaje ni, amma gaskiya shi wannan aikin na buƙatar haƙuri da juriya ne. ina da burin na samu mai gajin nawa. Amma gaskiya dole sai na samu mai dauriya. Akwai wasu ƙungiyoyin da suke irin wannan aikin suka zo suka ce mana mu yi maja, na ce musu wannan aikin nawa ba irin nasu na kaza da kaza bane. Sannan kuma dole ne sai mutum yana da laƙanin wannan abun. Amma ina rubutawa a rubuce ko da bayan na rasu da yardar Allah abubuwan ba za su bace ba, insha Allahu.