Connect with us

JIYA DA YAU

Ko Goben Rayuwar Bahaushe A Kasar Hausa Za Ta Zama Sai Madalla Kuwa?

Published

on

Kamar yadda muka yi duba ga rayuwar Bahaushe a jiya mai nisa, da jiya ta kusa, sannan mu ka kalli rayuwar Bahaushe a yau za mu ga cewa akwai bambance-bambance ma su yawa, kama ga salon tsarin rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran al’amuran rayuwarsa. Da wannan ne za mu iya hasashen ya gobensa za ta kasance, shin za ta haifar da ɗa mai ido ko kuwa?
Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce da dama a kan yadda rayuwar Bahaushe za ta kasance a gobe in har Bahaushen bai canza ba. Kamar yadda mu ka ce a baya mutukar mu ka bar samari da ‘yan mata suna cin karensu babu babbaka ta fuskar shaye-shaye da yawan tazubar ga ‘yan mata babu shakka wannan ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba. Hakazalika, idan muka kasance babu taimakon juna a tsakanin masu shi da marasa shi barace-barace ya yi yawa babu tausayin juna babu shakka aikin ɓarna zai yawaita, kamar sace-sace da zinace-zinace da sauran miyagun laifuffuka wanda ba zai haifarwa wannan yankin ɗa mai ido ba.
Hakazalika, shehin malami, ferfesa Amfani(2012) a cikin mukalarsa mai taken Hausawa: jiya da yau. Ya nuna cewa, ” Idan taɓarɓarewar al’amura da muke gani a yau suka ci gaba, to goben Hausawa ba za ta yi kyau ba. ”
INA MAFITA?
Malamin ya yi tsokaci a kan hanyoyin da za a bi a bulle ko kuma a samu ɗa mai ido kamar haka:
Akwai mafita kala biyu; 1. Wadda kowa da kowa sai ya sa hannu. 2. Akwai kuma mafitar da masana da masu mulki ne kawai za su iya samar da ita. Ya ci gaba da cewa, me Bahaushe ya fahimta da ci gaba? Da alama a irin tsarin zamani, Bahaushe ya so ya yi wa ci gaba mummunar fahimta. Ci gaban al’umma ba ya tabbata sai an shimfida shi bisa wasu halaye da falsafa na kwarai. Falsafar Bahaushe tana kunshe ne cikin karin magana da maganganun azanci. Misali, duk halayen kwarai da aka san Hausawa da su, tilas ne a koma musu don a samu ci gaba. Ana iya inganta waɗannan halaye na kwarai don su dace da zamani kamar yadda wannan masani ya nuna. Alal misali, juriya da kwazo da gaskiya da rikon amana da mutunta sana’a da ladabi da biyayya, abubuwa ne waɗanda a kowane zamani, ci gaba ba ya yiwuwa sai da su. Idan wata al’umma ta yi watsi da waɗannan kyawawan halaye, waɗanda su ne gishirin tafiya a kowace tafiya ta ci gaba, to babu shakka inda wannan al’umma za ta je a cikin zarafofin duniya. Wani ginshikin ci gaba kuma shi ne ilmi na addini da na sana’a.
Wannan masani, ya ci gaba da kawo mafita a cikin makalar tasa, inda ya nuna, idan muka koma ga masana a cikin al’ummar Hausawa, sai mu ga lalle suna da hakki na su, sannan hakkin masana ne su kafa kungiyoyi irin na zamani (NGO’s) masu karfi na daidaita tunanin al’umma. Waɗannan kungiyoyi su ne za su rika wayar da kan mutane kan harkoki daban-daban.
Ta ɓangaren masu mulki kuwa, tilas ne hukuma ta yi wa al’umma jagoranci na kwarai. A duniyar mutanen kwarai, mutum ba ya zama shugaba sai ya san mutanen da yake shugabanta. Tilas ne ya san asalinsu, ya san inda suka fito da inda suka fito da inda za su; ya san matsalolinsu da bukatunsu, ya san falsafarsu ta rayuwa, ya taya su hangen nesa don cimma burinsu na rayuwa. A yau shugabanni sun jahilci al’ummomin da suke shugabanta. Don haka zai yi wuya shugabanni su burge waɗanda suke shugabanta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: