Abba Ibrahim Wada" />

Ko Ka San Alkalin Wasan Da Ya Ba Da Katin Kora Sau 99 A Duniya?

Alkalin wasa Mike Dean, dan kasar Ingila yana shirin kafa tarihin bayar da jan kati (Red Card) na 100 a wasan da zai jagoranta tsakain kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da Chelsea a ranar Lahadi mai zuwa.
Mike Dean, wanda yafara alkalancin wasannin firimiya a shekara ta 2000 kawo yanzu ya bayar da jan kati 99 a tarihin wasannin daya busa na gasar firimiya yayinda yake harin jan kati na 100 a babban wasa tsakain Chelsea da Manchester City.
Alkalin wasan ya fara alkalancin wasa a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Leceister City ta kara da Southmapton a gasar firimiya a kakar wasa ta 1999 zuwa 2000 sannan zai da yayi watanni takwas kafin yafara bayar da jankati a tarihinsa.
Dan wasa Nolberto Solano, tsohon dan wasan Newcastle United shine wanda Dean yafara bawa jan kati inda daga nan kuma yabawa ‘yan wasa da dama jan kati inda jimulla ya bawa kungiyoyin gasar firimiya kati sau 99.
Kungiyoyin Chelsea da Manchester City, sune kungiyoyin da Dean yabawa jan kati mafi yawa inda kowacce kungiya yabata jankati guda tara sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Newcastle guda bakwai sai Arsenal wadda yabawa ‘yan wasanta sau shida.
Kungiyoyin Stoke City da Tottenham da kuma Westbrom, sune kungiyoyin da Mike Dean yabawa jan kati sau biyar biyar sai kuma kungiyiyi masu uku da kuma masu guda biyu da guda daya.
Jimulla yanzu Mike Dean yayi alkalancin wasannin firimiya sau 473 yayinda wasan da zai busa ranar Lahadi shine wasa na 473 kuma duka kungiyoyin biyu daman yafi basu jan kati kamar yadda muka fada a baya.

Exit mobile version