Connect with us

Madubin Rayuwa

Ko Ka San Dimbin Hikimomin Da Allah Ya Kunsa A Cikin Sauro?

Published

on

Sauro wanda a Turance ake kira da Moskuito, wata ‘yar karamar halitta ce sananniya da take da tarihi da kuma dinbin shekarru a doron kasa, asali har a cikin Alkur’ani an ambaci wannan halittar.

Ita dai wannan halittar ta Jalla wa Azza, duk da zamanta ‘yar kankanuwa amma kuma takan tagayyara halitta mafi daraja a doron kasa waton Dan Adam.

Ga sauro dan karami da shi amma kuma sai ya zo kobai cije ka ba da kukansa kawai zai iya hanaka bacci har garin Allah ya waye.

Shin wannan bai isa ya zamo aya a gare mu ba ?

A zahiri, idan muka kalli gangan jikin halittar sauro zamu ga yana da kai, yana da idanuwa 4, biyu manya (compound ayes) da kuma idanuwa biyu kanani (simple eyes) sai dai a badini an ce yana da idanuwa kusan dari a gangar jikinsa. Yana da irin wani tsinke mai kaifin gaske da yake amfani da shi ya tsotsi jini nan take. Yana da antena wacce take zama kamar igiyar dake samar mashi da bayyannai a kan hanyoyin da zai kai shi zuwa ga abin da yake bukata. Sauro yana da kirji, yana da ciki, yana da kafafuwa, yana da fukafukai. Yana buga wadannan fukafukin nasa kusan sau dari biyar a cikin dakika daya. Wanda hakan ke sa muna jin sautin nasa a sanda ya tunkaro jikinmu. Haka kuma wannan sautin shi ke sa namijin sauro ya san inda macen take har ya kai gare ta su hadu.

Sauro kalmar namiji ne amma kuma namijin sauro baya cizo kuma baya shan jini ya dogarane a kan ciyawa da sauran furanni. Macen sauro a Turance ake kira ‘Anophelene Moskuito’ ita ke cizo kuma ita ke shan jini har ta yi silar afkuwar malaria wa jikin mutum.

Macen sauro takan sha jinin mutum ne dan tana bukatar sinadirai wanda ake samu a cikin jinin mutum dan ta samu damar kankesar kwai ta. Macan sauro takan sha jinin da ya ninkata nauyi sau uku a lokaci guda.

Sauro yana da karfin ji ta yanda ya kan ji sautin fitar iskan da muke fitarwa daga huhunmu a lokacin da muke bacci. Wannan sautin ne yake bi har ya kai ga inda mutum yake.

Macen sauro tafi namijin sauro jimawa a doron kasa. Domin shi namijin yana rayuwa tsakanin kwana goma zuwa ashirin sai ya mutu. A yayin da ita matar takan iya daukar wata uku zuwa kwana dari kamin ta mutu.

Sauro yana da irin wata na’ura a cikin cikinsa mai bashi damar sanin inda jijiyar dake dauke da jini take. Wannan ya sa duk inda sauro zai ciza to za ka ga wajen yana mai dauke da jini.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: