Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Zidane Ya Ajiye Aiki A Real Madrid?

Published

on

Mai koyarwa Zinedine Zidane ya yanke shawarar ya bar kungiyar Real Madrid kwanaki biyar bayan ya jagoranci ‘yan wasansa ga nasarar lashe kofi Zakarun Turai karo na uku a jere.

Matakin murabus din Zidane ya jefa Real Madrid cikin wani yanayi na rashin tabbas ga nasarorin da ta samu a zamaninsa bayan da aka fara has ashen cewa abune mai wahala kungiyar taci gaba da samun nasara kamar a lokacinsa

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya kadu matuka da matakin murabus din Zidane, inda yanzu zai shiga neman wanda ya fi dacewa ya maye gurbinsa inda tuni aka fara hasashen cewa kungiyar tafara tattaunawa akan wanda zai maye gurbin nasa.

Shin ko wane dalili ne ya sa Zidane yin murabus, sannan ya Real Madrid ta dauki murabus dinsa bayan day an wasan kungiyar nada dana yanzu suka dinga tofa albarkacin bakinsu bayan da sukaji labarin tafiyar Zidane din.

 

  • Zidane Ya Yiwa Duniya Bazata

Lalle labarin murabus din ya girgiza shugaban gudanarwar kungiyar, Florentino Perez, wanda ya zauna kusa da Zidane a lokacin da yake sanar da matakinsa Fuskarsa ta nuna yadda labarin ya zo ma shi babu zato babu tsammani.

Shugaban na Real Madrid ya sanar da cewa Zidane ya shaida ma sa zai yi murabus a kwana guda kafin ya sanar wa duniya zai bar Real Madrid kuma yayi kokarin shawo kan Zidane din amma ya fahimci tuni y agama yanke hukunci kuma yasan halin Zidane idan ya yanke hukunci.

Sannan ya ce wanda Zidan kawai ya shaida wa matakinsa na yin murabu shi ne Keftin din kungiyar, Sergio Ramos wanda shima a ranar ya shaida masa da safe kafin a kirawo taron manema labarai.

Zidane ya fito ya bayyana dalilin da ya tilasta ma shi yin murabus, inda ya amsa cewa ba shi da tabbacin kungiyar za ta ci gaba da samun nasara a karkashinsa saboda haka ya yanke hukuncin tafiya domin a rabu cikin mutunci.

Zidane ya ce “kungiyar na bukatar sabon salo kuma yan wasan kungiyar suna bukatar sabon mai koyarwa saboda abinda yake koya musu sun gaji da sauraro kuma suna bukatar sabon salon daukar horo”

Sannan Zidane ya bayyana irin kalubale da matsin lamba da ke tattare da aikin inda yace koyar da kungiya kamar Real Madrid abune mai wahala domin da duniya kake Magana kuma duk abind ayafaru kai za’a dinga kallo.

Sai dai Zidane bai fadi asalin dalilin da ya tursasa ma shi daukar matakin ba Ko da yake da aka tambaye shi ya fadi babban kalubalen da ya fuskanta, sai Zidane ya bayyana cewa yadda Leganes ta fitar da Real Madrid a gasar Copa del Ray a watan Janairu.

An tambayi Zidane, ko don ya lashe kofin zakarun Turai sau uku a jere ne, dalilin da ya yanke shawarar cewa yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya tafi, sai ya amsa cikin dariya yana cewa watakila haka ne.

 

  • Ya Makomar Real Madrid Za Ta Kasance?

Akwai masu koyarwa da dama da ake tunanin za su iya maye gurbin Zidane, kuma Kocin Tottenham Mauricio Pochettino na daya daga cikin wadanda ke sahun gaba.

Ana tunanin Pochettino ne shugaba Perez zai bawa aikin horar da Real Madrid saboda yadda ya jima yana sha’awarsa tun yana aikin horar da Espanyol, kungiyar da ke da alakar kawance da Real Madrid.

Kuma Perez ya yaba da rawar da Tottenham ta taka a gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata inda yace kungiyar tasamu wannan nasara ne duk saboda irin kokarin Pochettino.

Sai dai Pochettino bai dade da sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar da Tottenham ba, kuma ana ganin zai yi wahala mai koyarwar yayi gaggawar barin kungiyar bayan ya amince zai ci gaba da aikinsa a Ingila.

Ko da yake wasu rahotanni sun ce a cikin kwantaragin da ya sanya wa hannu akwai inda aka bayyana zai iya ajiye aikinsa idan har Real Madrid ta neme shi.

Sauran wadanda ake ganin za su iya maye gurbin Zidane sun hada da kocin Chelsea Antonio Conte, da kocin Jamus Joachim Low da tsohon kocin Napoli Maurizio Sarri, yayin da wasu ke ganin Perez zai iya sake dauko Jose Mourinho Kocin Manchester United.

 

  • Mene Ne Makomar Bale Da Ronaldo?

Makomar Cristiano Ronaldo na daya daga cikin tambayoyin da aka yi wa Zidane a lokacin da yake sanar da matakinsa na barin Real Madrid.

An tambayi Zidane ko rashin tabbas ga makomar Ronaldo a Real Madrid na daga cikin dalilan da suka sa ya yi murabus. Nan take ya girgiza kai ya amsa cewa a’a inda yace babu wani dan wasa da zaisa ya yanke hukuncin da baiyi niyya ba.

Sai dai kuma ana ganin daga cikin manyan batutuwan da duk wanda Perez zai dauka a matsayin sabon kocin Real Madrid, zai fuskanta shi ne makomar Ronaldo da Gareth Bale a kungiyar.

Sannan da batun dauko dan wasa Naymar, yayin da rahotanni suka ce dan wasan na Brazil ya nuna yana sha’awar barin Paris St-Germain zuwa Real Madrid nan gaba bayan da Real Madrid din ta nuna tana bukatarsa.

Kazalika sabon kocin zai fuskanci kalubale zabin sabbin ‘yan wasa a madadin wasu tsoffin ‘yan wasan Real Madrid din da ake ganin zasu bar kungiyar.

Keylor Nabas zai ci gaba da zama golan Madrid na farko ne ko kuwa idan an dauko Thibaut Courtois ko Dabid de Gea za su karbe wurinsa?

Shin lokaci ya yi da Benzema zai kama gabansa? Luca Modric da ke hararar shekara 33, zai ci gaba? Tsakanin Eden Hazard da Robert Lewandowski da Mohamed Salah wa ya fi dacewa da Real Madrid.

Wadannan sune tambayoyin da ake son duk sabon mai koyar da kungiyar sai ya amsa su kafin Perez ya amince suyi aiki tare.

Duk da cewa Zidane ya lashe kofin zakarun Turai sau uku a jere a cikin shekaru biyu da rabi, har yanzu wasu na ganin Zidane ba kwararren koci ba ne saboda akwai lokuta da dama da yakeyin kura kurai kuma ana ganin rashin kwarewa ce yake kawo hakan.

Wasu na ganin Zidane ya zo ne a sa’a, maimakon yin amfani da kwarewa kuma nan gaba dole akwai lokacin da zaizo sai dai kwarewa tayi aiki ba sa’a ba musamman a wasu hukunce hukuncen da sai manyan masu koyarwa ne suke iyawa.

Zidane ya gaji zubin manyan ‘yan wasa, kuma daga cikin ‘yan wasan da suka buga wasannin karshe a 2017 da 2018 babu dan wasa guda cikinsu da Zidane ya yi dalilinsa na zuwa Madrid. Amma babbar rawar da ake ganin ya taka shi ne yadda ya tafiyar da zubin manyan ‘yan wasan.

Ya girmama ‘yan wasan tare da ba kowa hakkinsa a muhallin da ya dace sannan kuma yayi kokari wajen ganin bai shiga harkar kowanne dan wasa ba kuma sannan an yabawa Zidane wajen tafiyar da lafiyar wasu daga cikin manyan yan wasan kunguiyar da suka hada da Ronaldo da Ramos da kuma Modric.

Sai dai ana ganin cewa manyan kungiyoyi da dama za su yi la’akari da shi a lokacin da suke bukatar gwarzon mai koyarwa Amma a yanzu Zidane ya yi ikirarin cewa zai huta, ba shi da ra’ayi, yana mai cewa ba zai horar da ‘yan wasa ba a kaka mai zuwa.

Wasu na ganin aikin horar da Faransa ne Zidane ke harara musamman idan har Didier Deschamps ya kasa taka rawar gani duk da zubin ‘yan wasan da ke gabansa a gasar cin kofin duniya.

 




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: