Abba Ibrahim Wada" />

Ko Ka San Irin Tarihin Da Manchester City Ta Kafa A Gasar Firimiya?

 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa tarihin da babu wata kungiyar da ta taba kafa wa a kakar wasa a gasar Firimiya a Ingila.

Tun a 15 ga Afrilu Manchester City ta lashe kofin Firimiya na bana, kuma kofin gasar na farko da Pep Guardiola ya lashe a kakarsa ta biyu a kungiyar a matsayin mai koyarwa.

Baya ga kofin da Manchester City ta lashe kuma ta shafe wasu tarihin da aka taba kafa wa a gasar Firimiya, kamar haka:

Maki 100 A Kakar Wasa Daya

Manchester City ta kammala kakar bana da maki 100 a teburin Firimiya, tarihin da ba a taba kafa wa ba a tarihin gasar bayan data doke kungiyar Southampton daci 1-0 a fafatawar ranar karshe a Firimiya.

Ana dab da tashi daga wasan ne  Gabriel Jesus ya ci wa Manchester City kwallon a ragar Southampton, wanda ya taimaka City kafa tarihin da yawan maki 100 a Firimiya a bana.

Yawan Kwallaye

Manchester City ta shiga kundin tarihin gasar Firimiya, inda ta kammala kaka da yawan kwallaye 106 kuma ita ce ta fi yawan cin kwallaye a raga a kaka daya a tarihin Firimiya sannan  ta karya tarihin da Chelsea ta kafa na yawan kwallaye 103 a zamanin Carlo Ancelotti a kakar wasa ta 2009/10.

Yawan Samun Nasara

Manchester City ta buga wasanni 32 ba’a doke ta ba a gasar Firimiya a bana inda ta shafe tarihin da Chelsea ta kafa a kakar wasa ta  2004 zuwa 2005 sannan ta karya tarihin da Tottenham ta kafa a shekaru 57 a matsayin kungiyar da ta fi yawan samun nasara a kakar wasa a Firimiya.

Haka kuma ba a doke Manchester City ba a wasanni 16 da ta kai ziyara a Firimiya, tarihin da babu wata kungiya da ta taba kafawa a gasar kuma a bana Manchester City ta buga wasanni 18 a jere ba tare da an doke ta ba.

Yawan Tazarar Maki

Manchester City ta kammala kaka da tazarar maki 19 tsakaninta da Manchester United da ke matsayi na biyu a teburin Firimiya.

Wannan ne maki mafi tazara a tarihin Firimiya kuma Manchester City ta kafa tarihin kan abokin hamayyarta Manchester United da ta doke Watford ci 1-0 a filin wasa na Old Trafford a ranar Lahadin data gabata sannan yawan tazarar ya nuna yadda Manchester City ta yi wa abokan hamayyarta fintikau a bana.

Dan Wasa Kebin De Bruyne

Dan wasan na Belgium ya kafa tarihin da babu wani dan wasa da ya taba kafa wa a gasar firimiya inda ya taimaka anci kwallaye 16 a kaka daya.

Sannan shi ne dan wasan da ya fi yawan samun nasara a wasannin Firimiya a kaka daya inda ya buga wasanni 31 da City ta yi nasara.

Pep Guardiola

Mai koyarwa Pep Guardiola ya lashe lambar yabo da ake bayarwa wata wata sau hudu a jere a gasar Firimiya.

Kocin da ya jagoranci Manchester City ga nasara a bana, ya ce yana ganin za a dauki lokaci kafin a karya tarihin da ya kafa na samun maki 100 a gasar Firimiya.

Guardiola ya taba kammala gasar La liga da maki 99 a kakar 2009-10 a lokacin da

yana kungiyar Barcelona.

 

Exit mobile version