Jaridar Le Parisien ta kasar Faransa ta rawaito cewa, kungiyoyin Liverpool da Manchester City da Chelse na cikin kungiyoyi shida da suka nuna sha’awarsu ta sayo Neymar da Kylian Mbappe daga kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta Faransa.
Har yanzu, Neymar na Brazil na hangen ficewarsa daga PSG, yayin da rahotanni daga kasar Sipaniya suka ruwaito cewa, Mbappe ba shi da aniyar sabonta kwantiraginsa da PSG wanda zai kare a shekarar 2022.
A bangare guda, PSG na zawarcin Sadio Mane na Liverpool, inda take fatan kulla kwantiragi da shi da zaran ta raba gari da Neymar kuma wata jarida a kasar Ingila ta ce, Mane na ci gaba da samun farin jini a wurin mahukuntan PSG.
Sai dai babu tabbas ko Mane da Liverpool za su amince da wannan tayi saboda a kwanakin baya dan wasan ya bayyana cewa bashi da burin barin kungiyar ta Liverpool kuma har ya sake sabuwar yarjejeniya da kungiyar.
A watan Yulin daya gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kusa sayan dan wasan Neymar wanda tsohon dan wasanta ne bayan daya nuna cewa yana fatan komawa kungiyar da buga wasa.
Sai dai kokarin da Barcelona tayi akan mayar da dan wasan nata yaci tura duk da wasu rahotanni sun bayyana cewa ta yiwa PSG tayin ‘yan wasa guda biyu sannan zata hada mata da kudi akan Neymar, dan Brazil.