Abba Ibrahim Wada" />

Ko Ka San ‘Yan Wasan Da Kwantiraginsu Zai Kare A Karshen Kakar Bana?

Messi

Wasan kwallon kafa ya ci karo da koma baya a fadin duniya tun bayan bullar annobar cutar korana a kakar bara kuma hakan ya sa aka fara dakatar da dukkan wasanni domin gudun yada annobar daga baya aka ci gaba da fafatawa amma babu ‘yan kallo.

Cikin kalubalen da cutar ta haddasa har da matsin tattalin arziki da kungiyoyi suka fada, wadanda suka dunga rage albashin ‘yan wasa da jami’ai da sauran matakan matse bakin aljihu duka saboda cutar.

Hakan ne ya sa kungiyoyi ke kasa sayen ‘yan kwallo kudi da yawa kamar yadda ake yi a baya a lokacin cinikayyar ‘yan wasan kwallon kafa domin ko lokacin da aka ci kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a watan Janairu, kungiyoyi sun fi zabar tsarin karbar aron dan kwallo maimakon su saya ya zama mallakinsu.

A karshen kakar bana ake sa ran karkare wasannin gasar nahiyoyi a wasu kasashe a Turai da sauran wurare sai dai kuma kawo yanzu akwai wasu fitattun ‘yan wasa da yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar nan da ya kamata su ci gaba da buga wasa.

Cikin ‘yan kwallon nan sashin hausa na BBC ya hada ‘yan wasa 11 da za su iya gagarar kowacce kungiya idan suka hadu da ita saboda kwarewarsu wanda hakan ya zama abin mamaki saboda duk da kwarewarsu amma kungiyoyinsu sun kasa basu kwantiragin da suke bukata ya yinda kuma wasu suka gaji da zaman kungiyoyin da suke.

Gianluigi Donnarumma (AC Milan)

AC Milan na taka rawar gani a gasar Serie, yayin da mai tsaron ragarta Gianluigi Donnarumma ya kama raga sama da sau 200 tun bayan da ya fara buga mata wasa yana mai shekara 16 a duniya.

Yanzu yana da shekara 21 da haihuwa kuma daya daga fitattun masu tsaron raga a duniya da ake cewar zai kai fam miliyan 50 kudin sayen shi sai dai kuma AC Milan ta yi shiru kan batun tsawaita zamansa a kungiyar.

Wasu masu tsaron raga da kwantiraginsu zai kare a bana sun hada da Fernando Muslera da Lukasz Fabianski na kungiyar kwallon kafa ta West Ham United da Sergio Romero na Manchester United da kuma Asmir Begobic.

Jerome Boateng (Bayern Munich)

Boateng wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Jamus na buga wa Bayern Munich wasa sosai a bana kuma tsohon dan wasan na Manchester City mai shekara 32 ya amince zai ci gaba da zama a Jamus amma har yanzu kungiyar ba ta zauna da shi ba kan tsawaita zamansa ba.

Sergio Ramos (Real Madrid)

Sergio Ramos ya buga wa Real Madrid wasanni 700 sannan kyaftin din na Real Madrid ya kusan buga wa kungiyar wasanni9 700 da cin kwallo 100 sai dai cikin watan Maris zai cika shekara 35, kuma Real Madrid ta yi masa tayin tsawaita kwantiraginsa kaka daya amma wasu rahotanni na cewar kungiyar ta ce za ta rage albashinsa daga fam miliyan 10.5 zuwa fam miliyan 8.8 idan ya amince zai ci gaba da zaman kungiyar.

Dabid Alaba (Bayern Munich)

Alaba shi ne na biyu mai tsaron baya da ake cewar zai bar Bayern Munich a bana, bayan da suka kasa cimma yarjejeniyar tsawaita zamansa kuma dan wasan mai shekara 28 a duniya wanda ke iya buga wasan tsakiya an yi ta alakanta shi da cewar Real Madrid zai koma a badi.

Har ma ake cewar Real Madrid za ta dunga bashi fam miliyan 204,000 a kowanne mako, bayan an fitar da haraji amma banda Real Madrid akwai kungiyoyi irinsu Chelsea da Manchester City da suke bibiyar dan wasan.

Wasu masu tsaron baya da yarjejeniyarsu zai kare a karshen kakar wasa ta bana sun hada da Eric Garcia na Manchester City wanda ake saran zai koma Barcelona da Juan Bernat da Patrick ban Aanholt na Southampton da kuma Thiago Silba na Chelsea.

Fernandinho (Manchester City)

Fernandinho Mai shekara 35 da haihuwa dan asalin kasar Brazil ya buga wa Manchester City wasa sama da 300 ya kuma lashe Premier League uku da FA Cup sai dai watakila Pep Guardiola ya kawo wani matashin domin ya maye gurbinsa domin shi kansa dan kwallon bai yanke makomarsa ba, shi ya sa wasu rahotannin ke cewar kungiyoyin kudancin Amurka na zawarcinsa.

Georginio Wijnaldum (Liverpool)

Georginio Wijnaldum ya lashe Champions League da Premier League a Liverpool sannan har yanzu dan kasar Netherlands din, Wijnaldum bai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ba, kuma ana cewa watakila shi ne na farko a kungiyar da ya lashe Champions da Lig zai bar Anfield a bana bugu da kari dan wasan mai shekara 30 ya dade yana mafarkin son yi wa Barcelona wasa wadda Ronald Koeman ke horarwa.

Memphis Depay (Lyon)

Manchester United ta bai wa dan wasa Memphis Depay damar gwada sa’a a kasar Faransa tare da Lyon wadda kwantiragin da suka kulla ta shekara hudu za ta kare a karshen kakar bana, amma har yanzu basu cimma matsaya ba kuma DFepay mai shekara 26 a duniya dan kasar Netherlands ana ta alakanta shi da zai koma Barcelona, yayin da Borussia Dortmund ke son zawarcin dan kwallon.

Julian Dradler (Paris St-Germain)

Yarjejeniyar dan kwallon tawagar Jamus din Dradler zata kare a kungiyar Paris St German a karshen kakar bana sannan dan wasan mai shekara 27 a duniya ya bayyana cewar zai karkare kwantiraginsa a PSG, zai kuma sanar da inda zai koma a cikin watan Maris.

Wasu masu buga tsakiya da kwantiraginsu zai kare a kakar wasa ta bana sun hada da Hakan Calhanoglu na AC Milan da Henrikh Mkhitaryan na Roma da Jabi Martinez na Bayern Munchen da kuma Juan Mata na Manchester United.

Angel di Maria (Paris St-Germain)

Angel Di Maria bai ji dadin zaman da ya yi a Manchester United ba, amma yana taka rawar gani a Paris St Germain, wanda ya lashe Ligue 1 guda hudu da kai wa karawar karshe a gasar kofin zakarun turai na Champions League a bara sannan dan wasan ya yi shiru duk da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana.

Lionel Messi (Barcelona)

A karshen kakar nan yarjejeniyar kyaftin din Lionel Messi zata kare a Barcelona kuma tun farkon kakar bana Messi ya nemi izinin barin kungiyar, bayan da kungiyar ta kasa taka rawar gani a bara da rigingimu da suka faru a kungiyar sai dai tuni dai Manchester City ta nuna sha’awar daukar dan kwallon ya yinda PSG itama ta fara Magana da dan wasan.

Sergio Aguero (Manchester City)

Aguero wanda shi ne ke kan gaba a cin kwallaye a tarihin Manchester City a yana fama da jinya a kakar bana sai dai wasu rahotanni sun ce an bukaci dan kwallon mai shekara 32 a duniya da ya raba albashinsa biyu na fam 260,000 a kowanne mako idan har yana son ya ci gaba da buga wasa a kungiyar.

Wasu fitattun masu cin kwallayen da kwantiraginsu zai kare a karshen kakar wasa ta bana sun hada da Zlatan Ibrahimobic na AC Milan da Olibier Giroud na Chelsea da Steban Jobetic da kuma Troy Deeney na Watford.

Exit mobile version