Ko Kasan Irin Kalubalen Dake Gaban Messi?

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Argentina da Barcelona, Lionel Messi ya yi bajinta da yawa a fagen kwallon kafa a duniya da za a dade ana tunawa da shi ciki har da lashe kyautar Ballon d’Or shida da karbar takalmin zinare a yawan cin kwallaye a Turai da sauransu, sai dai duk da haka akwai kalubale dake gabansa guda 10.
1. Tarihin yawan buga wa Barcelona wasanni.
Ba a dade ba Messi ya haura tarihin da Andres Iniesta ya kafa, ya koma na biyu a jeren wadanda suka yi wa Barca wasanni da dama, yanzu ya yi wasanni 692, wanda ke na daya shi ne dabi Hernandez wanda ya buga wasanni 767 kafin tabar kungiyar.
Sai dai wasu suna ganin abune mai wahala Messi ya karya tarihin da dan wasa dabi ya kafa a kungiyar na buga wasannin da yawa yayinda wasu suke ganin tabbas idan har ya cigaba da buga wasa a Barcelona har zuwa kakar wasa ta gaba zai iya kamo dabi, musamman ma idan yana yawan buga wasa baya zuwa jinya.
“Babban tarihine kasancewa a Barcelona da kuma buga wasanni masu yawa sai dai duk da cewa akwai wanda ya fini yawan buga wasa nima ina fatan kasancewa na kamo shi sannan in wuce shi domin kasancewa wanda babu kamata a kungiyar” in ji Messi, a lokacin daya kamo Iniesta wajen buga wasanni.
Sai dai shima kociyan kungiyar ta Barcelona, Enesto balberde, ya bayyana cewa idan har Messi ya cigaba da zama a kungiyar tabbas zai karya tarihin da dabi ya hada kuma yana fatan Messi zai kare kwallons a Barcelona.
2. Takalmin zinare na bakwai a La Liga da Turai
Messi ya lashe takalmin zinare karo na shida wajen cin kwallaye a gasar Turai, kuma a lokacin kan jagoranci zura kwallaye a raga a gasar La Liga, saboda haka ana sa ran ko zai lashe na bakwai.
Sai dai wasu suna ganin yanayin yadda dan wasan ya fara buga kakar wasa ta bana babu tabbas din idan zai iya lashe kyautar wanda yafi zura kwallo a raga sannan kuma ita kanta kungiyar ta Barcelona bata buga wasa mai kyau kamar na kakar wasan data gabata.
Wasu suna ganin zuwan dan wasa Antonio Griezman zai kara rage yawan kwallayen da Messi yake zurawa a raga saboda shima Griezmann yana zura kwallaye a raga musamman a kungiya daya baro ta Atletico Madrid.
3. Yawan lashe kofuna da Ryan Giggs da bitor Baia suka yi
Idan har Barcelona za ta ci kofuna uku nan gaba, hakan zai bai wa Messi damar haura tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ryan Giggs, kuma mai horar da tawagar ‘yan wasan Wales a tarihin da ya kafa.
Kawo yanzu ya wuce tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da kungiyar Porto bitor Baia da kofi daya kuma tabbas idan har Barcelona ta cigaba da samun nasara zai iya kafa tarihin anan gaba kadan.
A wannan kakar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara kakar wasa da burin lashe gasar cin kofin zakarun turai da gasar laliga da kuma gasar cin kofin kalubale na Copa Del Rey wanda sukayi rashin nasara a wasan karshe a hannun balencia a kakar wasan data gabata.
4. Lashe kofin Zakarun Turai na Champions League Sau biyar
Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin zakaru na Champions League a bana a filin wasa na Ataturk da ke babban birnin kasar Turkiyya, wato Istanbul, idan har Barcelona ta lashe kofin shi ne karon farko da Messi zai daga a matsayin kyaftin, kuma na biyar jumulla.
Sai dai yanayin yadda ake buga kakar wasa ta bana yana nuna cewa akwai babban kalubale a gaban Barcelona, musamman idan akayi duba da irin salon wasan da kungiyar kwallon kafa ta Liberpool take bugawa, wadda itace ta doke Barcelona a wasan kusa dana karshe a kakar wasan data gabata.
5. dan Barcelona da ya fi yawan buga wasan hamayya na El Clasico
dabi Hernandez ne ke rike da tarhin yawan buga wa Barcelona wasan hamayya na El Clasico, sai dai Messi wanda ya buga wasan sau 41, idan ya buga wanda za a yi ranar 18 ga watan Disamba zai yi kan-kan-kan da na Hernandez.
‘Yan wasan Real Madrid uku sun buga El Clasico 42 daidai da na dabi, inda Sergio Ramos har yanzu ke buga wasannin daga cikin sauran da tuni sun bar kungiyar wasu kuma sunyi ritaya daga bu

Exit mobile version