Abba Ibrahim Wada" />

Ko Kasan ‘Yan Wasan Gaba Da Real Madrid Za Ta Saya?

Babban daraktan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Jose Angel Sanches, ya tattauna da wakilin ‘yan wasa Miralem Pjanic da Luca Jobic a kokarin da kungiyar takeyi na siyan ‘yan wasan gaba domin tun karar kakar wasa mai zuwa.
Real Madrid dai ta shirya kashe makudan kudade domin tunkarar kakar wasa ta gaba kuma tuni kungiyar ta fara siyan dan wasan baya, Elder Militao domin kara karfin baya yayinda kuma take cigaba da zawarcin ‘yan wasan gaba dana tsakiya.
dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Miralem Pjanic da dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Benfica, wanda yake zaman aro a kungiyar Eintracht Franfurt sune ‘yan wasan da kawo yanzu kungiyar take tattaunawa da wakilinsu, Fali Ramadani, domin ganin sun samu damar daukar ‘yan wasan.
kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta hanyar babban daraktan nata ta shirya wani zama domin ayi Magana da wakilin ‘yan wasan akan ko zasu iya siyansu musamman ma dai dan wasan gaba Luca Jobic, wanda ya zura kwallaye 22 cikin wasanni 36 daya buga a wannan kakar.
Shima dan wasan tsakiyar na Jubentus, yana son aiki tare da Zidane wanda hakanne ma yasa Real Madrid take ganin tana da damar siyan ‘yan wasan sai dai har yanzu Real Madrid bata kai tayin kudi ba ga kungiyoyin da ‘yan wasan suke.
Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ya wa re makudan kudade domin ganin kungiyar ta dawo hayyacinta bayan da ta kasa lashe kowacce gasa a wannan kakar kuma tana mataki na uku akan teburin laliga.

Exit mobile version