Ko Kun San Bikin Bazara Na Sinawa?

 

 

Akwai bukukuwa da dama a kasar Sin, daga cikinsu, bikin bazara wato Spring Festibal a Turance ya fi kasaita. Bikin bazara ya kan zo ne lokacin da Sinawa ke ban kwana da tsohuwar shekara, suna shiga cikin sabuwar shekara bisa kalandar wata ta gargajiyarsu. Bikin bazara na da matukar muhimmanci ga al’ummar Sinawa tamkar bukukuwan sallah ga al’ummar Hausawa. A cikin bayani na yau, za mu gabatar muku yadda bikin yake kasancewa gami da wasu al’adun gargajiya da abinci da suka jibanci wannan biki.

Ko kun san ina dalilin da ya sanya Sinawa ke kiran bikin sabuwar shekara da suna “Bikin Bazara”?

Dalilin da ya sa haka shi ne, saboda kasar Sin wata kasa ce da ta shahara a fannin aikin gona tun zamanin da, kuma wannan yana da nasaba da matsayinta a taswira da yanayinta. Kasar Sin tana arewacin bangaren duniya, kuma an kasa fasalolin yanayin ta gida hudu a kowace shekara, wato lokacin bazara, da lokacin zafi, da lokacin kaka, da kuma lokacin hunturu. Saboda ana yin matukar sanyi da kuma dusar kankara a lokacin hunturu, shi ya sa tun tuni a kan jira zuwa lokacin bazara wanda ake iya samun yanayi mai dumi, da kuma furanni masu kyan gani domin yin wannan biki. Kaza lika game da al’ummar Sinawa mai aikin gona, kaddamar da aikin shuka na ire-ire a lokacin bazara, wata alama ce ta zuwa wata sabuwar shekara. Idan an fara yin bikin bazara, hakan na alamta cewa, lokacin bazara yana zuwa, bishiyoyi da ciyayi za su farfado, kuma za a kaddamar da aikin shuka ire-ire, daga baya kuma za kai ga aikin girbi.

Sinawa suna baiwa bikin bazara sunan “Nian”, wanda ya zama biki mafi girma ga Sinawa daga cikin bukukuwan duk shekara.  A lokacin kusa da bikin baraza a kowace shekara, Sinawa su kan share daki, da sayen abinci masu dadin ci iri iri da sabbin tufafi. Ana fara bikin bazara ne daga ran 30 ga watan Disamba na kalandar wata ta gargajiya ta kasar Sin, wannan ce rana ta karshe ta tsohuwar shekara bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar Sin.

A wannan rana, iyalai na haduwa, da ajiye jajayen takardun da ake mannawa a gefunan kofa don isar da sakon alheri, da yin wasan tartsatsin wuta, da cin abinci tare. Bayan cin abinci, mutane suna hira da juna, tare da yin irin abincin da ake kira Jiaozi tare. A halin yanzu, iyalai da dama suna haduwa da kallon bikin maraba da bikin bazara a kan talibijin, mutane ba su yin barci a duk daren don maraba da zuwan sabuwar shekara, ana kiran wannan da sunan “Shou Sui”.

A safiyar rana ta farko ta sabuwar shekara, mutane suna tafiya zuwa gidajen iyalai da abokai. Lokacin da suke ganawa da juna, su kan ce “barka da sabuwar shekara”, da “fatan za a samu arziki a sabuwar shekara”.  Kana mutane su kan baiwa kananan yara kudin fatan alheri, a kan kiran shi da sunan “kudin Ya Sui”, ma’anarsa ita ce nuna fatan alheri ga yara a sabuwar shekara.

Ko yaushe ne asalin wannan muhimmin biki wato bikin bazara a idon Sinawa?

An ce, a lokacin da da can, akwai wani dodo mai karfi da ake kira da suna “Nian”. A rana ta karshe ta kowace shekara, yana fita ya lalata gonaki ya raunata mutane da dabbobi.  A wani lokaci, “Nian” ya fito waje amma ya tsere domin ya ji tsoro.  Dalilin da ya sa hakan shi ne ya gano tufafi masu launin ja a kofar wani gida da yara dake wasan tartsatsin wuta.  Don haka, mutane sun gane “Nian” yana jin tsoron launin ja da hasken wuta da kuma babbar murya.  Daga baya, mutane su kan ajiye jajayen takardun da ake mannewa a gefunan kofa da fitila mai launin ja da kuma yin wasan tartsatsin wuta.  Lokacin da “Nian” ya zo, ya ga akwai hasken wuta mai launin ja, ya kuma ji babbar murya, ya kan ji tsoro, ba zai iya fita waje ba. Mutane sun magance illar da “Nian” ke kawo musu, don haka ake kiran wannan rana da sunan “Guo Nian”, wato tsira daga hannun “Nian”.

Sinawa na da al’adun gargajiya iri daban-daban a wajen bikin bazara, ciki har da manna hotunan waliyin ba da kariya masu launin ja a kofar gida.

A ganin Sinawa, wadannan hotuna za su bada kariya ga duk iyalai daga aljannu ko masifa, gami da samar musu da zaman lafiya da alheri.

Game da wannan al’ada, akwai wani labari dake cewa, tun shekaru aru aru da suka gabata, akwai wani sarki a kasar Sin wanda aljannu suka hana shi sakat, sai masu gadinsa guda biyu suka dauki makamai suka tsaya a wajen kofa don ba shi kariya, abun da ya sa ya iya shiga barci. Amma, masu gadi biyun su tsaya a wajen kofa cikin tsawon lokaci ba wani kyakkyawan zabi ba ne wajen warware matsala daga asali, shi ya sa sarkin ya sa aka yi hoton surar masu gadi, sa’an nan aka manne su a kofa, domin kawar da aljannu.  Abun ban mamaki shi ne, bayan da aka manne hotunansu a kofar, aljannu ba su sake zuwa wurin sarkin ba. Sannu a hankali, fararen-hula sun fara kwaikwayar abun da sarkin ya yi, na manne hotunan waliyin dake bada kariya a kofa.  A harshen Sinanci, ana kiran wannan hoton “Men Shen”.  “Men Shen” ya kan kunshi hotuna biyu, kuma a kan manne su a gefen hagu da na dama a kofa.

A kasar Sin, a dauloli da kuma wurare dabban-daban, akwai irin wannan waliyin bada kariya da yawan gaske.  Akasarin hotunan waliyin, ana samun asalinsu ne daga jarumai ko kuma gwarzaye daga labarai da tatsuniyoyi na lokacin da na kasar Sin.  A halin yanzu, makasudin manne irin wannan hoto a kofa da Sinawa ke yi ya dan canja, wato daga kawar da aljannu da masifa kawai, zuwa nishadantar da jama’a a lokacin bukukuwa.  A ganin Sinawa, hotunan waliyin bada kariya da aka manne a kofa suna iya taimakawa ga samar da zaman lafiya da alheri ga jama’a, da bada kariya ga gidajen Sinawa.

Ban da al’adun gargajiya masu ban sha’awa, al’ummar kasar Sin su kan dafa abinci na musamman a yayin bikin bazara, ciki har da wani nau’in abinci wanda ya fi shahara a duk fadin duniya, wato Jiao Zi a yaren Sin.

Jiaozi shi ne “dumpling” da Turanci, nau’in abinci ne da ya fi samun karbuwa daga wajen Sinawa a yankin arewacin kasar Sin.

Jiao Zi yana da tarihi na tsawon shekaru sama da 1800, a baya, an taba yin amfani da shi a matsayin magani, an ce, shahararren likita a zamanin da a nan kasar Sin Zhang Zhongjing ne ya samar da irin wannan abinci. Tun can baya, a lokacin hunturu, akwai sanyi matuka, kuma annoba tana yaduwa, fararen hula da dama suna fama da sanyi da yunwa, har sanyi ya kan lalata kunnuwansu.

Likita Zhang Zhongjing ya ji tausayi, ya tsai da kuduri cewa, zai yi kokarin taimaka masu.  Daga baya ya dafa naman tunkiya da barkono da magunguna cikin tukunya tare. Da suka dafu, ya yanka su kanana da wuka, ya sa su cikin makunshi da aka samar daga garin alkama, ya daure su, ta yadda kunshi ya yi kama da siffar kunne, ya sake dafa “kunne”, da ya dafu, likita ya bai wa masu fama da ciwon su ci, duk wanda ya ci “kunne” guda biyu tare da miya mai zafi, bayan kwanaki sama da goma, sai suka warka, kana ba su ji tsoron sanyi ba.  Daga baya, an koyi hanyar kintsa Jiao Zi ta likitan, ana kintsa nama da kayan lambu a ciki, ake kiran shi da sunan Jiao Zi.  Bisa dalilin nan ne, siffar Jiao Zi ta yi kama da kunne.

A yankin dake arewacin kasar Sin, an saba da shirya Jiao Zi kafin karfe sifiri na daren ranar karshe ta wannan shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wato jajiberin bikin bazara, kuma ana cin Jiao Zi ne tsakanin karfe 11 na daren ranar karshe da karfe 1 na daren ranar farko ta sabuwar shekara.

Ma’anar al’adar ita ce, a ci Jiao Zi a daidai lokacin da yake tsakanin tsohuwar shekara da sabuwar shekara. Ana cin Jiao Zi ne a wannan lokacin domin yin addu’ar neman samun fatan alheri, da haduwar iyalai a sabuwar shekarar dake tafe.  A baya, Sinawa a yankin dake arewacin kasar Sin ne sun fi son cin Jiao Zi, amma yanzu Jiao Zi ya riga ya samu karbuwa ga Sinawa a fadin kasar Sin, har ma wajen al’ummun kasashen duniya baki daya.

To, masu karatu, wannan shi ne bayani game da yadda bikin bazara wato Spring Festibal na al’ummar kasar Sin ke kasancewa, gami da wasu al’adun gargajiya da abinci na musamman da suka shafi bikin.

Malam Bahaushe kan ce, gani ya kori ji, kuma Allah daya gari bamban.  Muna fatan wata rana in Allah ya yarda, ku ma za ku zo kasar Sin ku ganewa idanunku yadda bikin bazara ke kasancewa.

Murtala Zhang, Zainab Zhang, Jamila Zhou, ma’aikata ne na sashen Hausa na CRI. Sun rubuto daga Birnin Beijing.

 

Exit mobile version