Ko Kun San Tushen Jindadi Da Nishadi?

Tushen

Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa daura aure yana nufin kulla wata alaka ce da Ubangiji Madaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa aure ya kasance daga cikin dabi’u na Dan’adam. To amma duk da hakan Allah Madaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaka wacce daga karshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a dauki wannan alaka a matsayin wani abu mara muhimmanci ba.

Daya daga cikin munanan ayyukan da kasashen yammaci suka yi shi ne, rikon sakainar kashin da suke yi wa wannan alaka da rashin ba ta muhimmancin da ya kamace ta. Su dai Turawa suna mu’amala ne da wannan muhimmin lamari, wannan karfaffiyar alaka tsakanin mace da namiji, mu’amala tamkar ta cire riga ko kuma shiga wani shago, wato a matsayin wani abu kawai mai sauki kana iya yinsa yanzu ka kuma canza shi duk lokacin da ka ga dama. Don haka wannan akida ta kan sanya dandanon mutum su kasance masu adawa da ci gaban wannan alaka ta auratayya.

A duk lokacin da daya bangaren macen ko namijin ya ga wani abu ko kuma suka fuskanci wata matsala, to ba tare da hakuri da la’akari da wasu abubuwa ba a kan kawo karshen wannan alaka mai tsarki. Amma shi kuwa addinin Musulunci bai yarda da hakan ba, wato baya kwadaitar da hakan don kuwa a Musulunci an gina tushen iyali ne bisa karfafan tubalai. A ko da yaushe Musulunci ya kan ja kunnen mabiyansa wajen yin taka-tsantsan a lokacin da suke kokarin zaben abokin zama ko kuwa abokiyar zama sannan da kuma yin duk abin da mutum zai iya wajen kiyaye wanzuwar wannan tsarkakakkiyar alaka.

Dole ne ku yi iyakacin kokarinku wajen kare wannan sabuwar alaka, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku amfana da ‘ya’yanta.

Yana da kyau a fahimci cewa, kula da wannan alaka ba ta damfaru ne da irin kudin shigan da mutum yake samu, ko kuma yawan ilminsa ko kuma irin aikin da yake yi kawai ba, don kuwa shu’urin Dan’adam kan aure da gina iyali kusan abu guda ne, babu wani gagarumin bambanci tsakanin masani da malami da dan wasa ko kuma lebura da dai sauransu, hakan kuwa saboda shu’urin guda ne tsakankanin dukkan mutane, babu wani bambanci tsakanin talaka da mai kudi.

Babu shakka kowani guda daga cikin miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nutsuwa gare su bayan sun gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata bukatuwa ce da ma’auratan suke bukatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna bukatuwa da farin ciki da yanayin da yake samar da hakan.

Mai yiyuwa ne macen ko namijin su kasance ‘yan kasuwa, ko kuma ‘yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu sukan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna bukatuwa da yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata bukata ce ta wuce guri ba, a’a, a dabi’ance haka lamarin yake.

Hakika lamarin ba shi da alaka da abin hannun da mutum yake da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su dandani dadin zamantakewar aure ba, rayuwarsu ta kasance cikin kunci, cike take da hassada da haramtattun bukatu da fata.

Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, me yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi, marasa hakuri ko kuma malalaci. Don haka dukiya da mukami da zaman birni ko kauye ba za su canza yanayin zamantakewar iyalai ba matukar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma’auratan biyu.

Allah ya sa mudace a rayuwar auratayya, amin suma amin.

Exit mobile version