Connect with us

KIWON LAFIYA

Ko Kun San Yadda Tusa Ta Gagari Likitoci?

Published

on

tusa

Ita tusa wadda a ke ji da kuma yi ba wata abar kunya ba ce kadai, za ta iya kasancewa wata alama ce mai muhimmanci ta yanayin lafiyar jikin shi wanda ya yi ta. Amma kuma har yanzu likitoci sun gagara fahimtar al’amarin nata lamarinta.

Wannan magana ce wacce ba a son a yi ta a fili ba, amma ba shakka kuwa likitoci su na da matsala a kan sanin al’amarin da ya danganci yadda tusa ta ke faruwa, domin a yanzu dai abin kunya ba wani abin a-zo-a-gani da su ka sani game da yadda iskar mai wari ke haduwa a cikinmu.

”Iskar da ke fitowa daga duburarmu ta na gaya ma na abinda ya shafi dan-taki ne (20cm) a cikinmu kawai,” in ji Peter Gibson na jami’ar Monash a Bictoria ta kasar Australiya.

Gibson na son sanin abinda ke faruwa a can cikinmu, wanda ya ke da (nisan 130cm), inda abinci ke narkewa, har a samu yin ita tusar daga karshe.

Shi kuma al’amarin sarrafa abincin da ciki ya ke yi, ya danganta ne ga mu’amullar da ake yi tsakanin su kwayoyin halittarka da irin abincin da m mutum ya ci, da aikin samar da kuzari da kayan ciki ke yi, bayannan kuma da irin kwayoyin halittar da ke jikin shimutum, wanda duka wadannan abubuwa ne da ko wanne za a iya samun wata alama tasa a cikin wannan iska (tusa).

Samun wani fitaccen canjin akan yadda warin tusar mutum ya ke ka iya kasancewa alamar wata mummunar cut ace wadda ta shafi wani daga cikin dukkanin wadancan abubuwa da muka bayyana a can baya wadanda suke haifar da ita tusar.

Gibson ya cigaba da bayyana cewar, ”Mun san dan wani abu kadan game da ita, amma ya kasance abu mai wuyar gaske a san hakikanin abin da ke faruwa game da tusa.

Saboda haka ne tawagar su masanan suka maida hankalinsu akan wani bincike a cikin ‘yan hanjinka, inda za su rika auna iskar tusarka daga wuri zuwa wuri a ko wanne mataki na narka abinci da kayan ciki su ke yi.

Saboda muhimmancin abinda mu ka sani a kan tusa zuwa yanzu ba bu shakka ya ke nuna ma na cewar shi al’amarin tusa muhimmin abu ne da ya ke bukatar ayi bincike.

Idan ya kasance jikin mutum ya na samar da iskar hydrogen da methane masu yawa, to hakan na nuna kenan mai yiyuwa da akwai wata matsala da yadda cikin mutum ya ke sarrafa kayan abinci mai wadanda su ka ba mutum ya samu karfi ‘carbohydrates’).

Alal misali, yin hakan na sa wasu daga cikin sinadaran wannan kayan abinci mai ba mutum karfi (starche, sugar) su rube a cikin ciki.Yawan iskar methane ka iya kawo cikas ga yadda hanjin mutum ya ke motsawa, wannan kuma ya na nufin kenan, hakan zai iya haifar ma da matsalar kasa yin bayan gida lokaci zuwa lokaci, bama kamar ga mutanen da su ke da wata matsala ta hanji.

Sai dai wani al’amari wanda kuma abin takaicin shi ne, takamaimai ba mu san inda wannan iskar ta ‘methane’ ta ke samuwa ba a cikin mutum.

”Abin dai da wasu suke tsammani ko kuma ake dauka kawai shi ne, tana samuwa ne daga can kasar babban hanji, amma dai ba mu sani ba,” in ji Gibson.

Sinadarin hydrogen sulphide ne ke sa tusa doyi ko kuma wari kamar na rubabben kwai. Bayan damuwa da wannan iska ko wari ke haifar wa mutane idan wani ya yi tusa a wuri, idan mutum yana fitar da iskar da yawa to hakan zai iya kasancewa wata alama ce ta wani ciwo a bangon ‘yan hanji wanda zai iya bayar da wani muhimmin bayani,” in ji Gibson.

Wani babban abin mamaki kuma shi ne, har ya zuwa yanzu tabbatacciyar hanyar da a ka fi iya bincike a kan tusar mutum, ita ce ta numfashi, wato ba ta kai tsaye ba; ta duburarshi.

Tun da wata daga cikin iskar da mutum ya ke fitarwa ta tusar shi ta na shiga cikin jininka, kuma ka fitar da ita ta huhunka, zai iya kasancewa a samu burbushin ko0 kuma sauran tusarka ya biyo ta bakinshi.

Amma kuma wani abinda ya ke daure kai shi ne wannan ba zai nuna ma ka inda ainahi iskar ta samo asali ba. Sannan kuma wata iskar da jikinka ya ke fitarwa kamar wadda kwayoyin bakteriya, ko kuma a takaice wadanda suke sanadiyar kamuwa da wata cuta, da su ke tsakanin hakoranka su ke fitarwa, na iya jirkita sakamakon da za a samu.

Wani al’amarin daban kuma shi ne, a rubar da kashin mutum, to daga nan iskar da za a samu ta rubewar kashin za ta iya zama daya da warin ita tusarka. Ko da ya ke dai a nan ma, ba za a gane matsalolin da suke samuwa ba a farkon narkewar shi abincin.

To a nan sai kuma ita tawagar Gibsonta fara kuma ganin akwai hanyar da za su yi maganin wannan kalubalen inda suka kirkiiro ‘yar wata mitsitsiyar na’ura wadda mutum zai haɗiye, kamar kwayar magani.

Yayin da  ita tusar take tafiya a cikin mutum daga nan zuwa can za ta rika aika wa wata kwamfuta bayanan irin iskar wurin da ta je, haka kuma za ta riaa auna wasu abubuwan kamar yanayin zafin wurin da take da kuma guba ko kuma sinadaran da ke wurin.

Gibson ya ce daga karshe na’urar za ta biyo kashi ta fito.Ta wannan hanya likita zai iya samun cikakken bayani na duk wurin da wannan na’ura take. Kawo yanzu wadannan masu bincike sun jarraba wannan dabara a kan wasu aladu kuma nan da ‘yan watanni suke sa ran gwada ta a jikin mutum.

Idan a ka ga cewa wannan ‘yar na’ura ba ta da wata illa a cikin mutum, Gibson ya kara bayar da haske cewar, zai samar da matattarar bayanai ta irin iskar da ke cikin mutum wadda ta shafi cututtuka daban-daban da kuma yanayin irin rayuwar mutum.

Daga nan kuma za a iya sanin irin illar ko kuma matsalar wani magani da ake yi wa mutum na irin  su wadannan cututtuka.

To tun dai har an gano cewa iskar methane tana da dangantaka da matsalar rashin yin bayan-gida ko kuma (kashi) yadda ya kamata, Gibson yana fatan a samu damar gano inda wannan iskar (tusa) take haduwa da kuma lokacin da ta kan samu wato ayi ta ta fito har ma  kai ga jin warinta.

Bugu da kari kuma sai ya ce, ”Abin da kawai  mutum ya ke buƙata shi ne, abin da zai rage samar da wannan iskar wato tusa, wanda shi ne, canza abinci ko kuma wani magani da zai rage wannan matsala ta rashin yin kashi yadda ya kamata a rika yi.

Wanda kuma shi wannan wata babbar matsala ce a duniya a yau.” Ya kara da cewa ”to amma ba za mu iya sani ba har sai mun duba mun gani tukunna.”

Babu ko shakka ma ba za a ga ita matsalar ta Gibson na dagewa da ya yi a akan wannan al’amari na tusa ba. Kamar yadda shi kansa ya bayyana cewar, ”Abin sha’awa ne sosai, kana kara nitsawa a cikin binciken kana kuma kara yin hangen irin hasken da ke tattare da shi.”

Fatarmu dai  ita ce e ya yi nasarar tabbatar da alkawarin da ya yi, kada ita zakuwar ta kare da wata tarin iska ko kuma (tusa) mai dumi kawai ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: