Ko kun san?

  1.  Emmanuel Adebayor: Adebayor haifaffen Togo ne wanda yake buga wa kulob din Aston billa na Ingila kwallo.  Ya yi Kwallo a kulob da dama a Nahiyar Turai ciki har da kulob din Real Madrid.  Yanzu haka yana kokarin canza sheka ne zuwa kulob din Crystal Palace na Ingila. Dan kwallon ya Musulunta ne a kasar haihursa watau Togo inda aka gan shi yana karbar shahada daga wajen wani malamin addinin Islama da ke kasar.
  2. Franck Ribery: Ribery dai shahararren dan Kwallon Faransa ne da yanzu haka yake buga kwallonsa a kulob din Bayerrn Munich da ke Jamus. Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya karbi addinin Musulunci ne a shekarar 2002 inda ake kyautata zaton matarsa Wahiba Belhami Balarabiya ita ta ja ra’ayinsa har ya Musulunta.  Tuni dan kwallon ya kara sunan Bilal a jerin sunayensa.
  3. Eric Abidal Eric: Tsohon Dan kwallon Faransa da kuma kulob din Barcelona na Sifen.  Ya daina buga kwallo ne saboda matsalar ciwon zuciya.  A shekarar 2011 ce likitoci suka gano dan kwallon yana fama da matalsar ciwon zuciya sannan a shekarar da ta zagayo ne kuma aka yi masa aiki bayan an yi masa dashen sabuwar zuciya al’amarin da ya tilasta shi yin ritaya daga buga kwallon kafa.
  4. : Emeka Ezeugo, tsohon dan kwallon baya ne a kungiyar kwallon kafa ta Kasa watau Super Eagles. Yana daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da ya gudana a Amurka a shekarar 1994. A watan Fabrairun 2012 ne dan kwallon ya koma Musulmi bayan ya karbi shahada.
Exit mobile version