Ko Layin Dogo Zai Farfado Da Martabar Tattalin Arzikin Arewa?

Layin Dogo

Babu shakka Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi dogon tunanin da ta karkata akalar ayyukanta a bangaran farfado da layin dogo  wanda a cewarta  domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya ne uwa uba yankin Arewa wanda ya sha bakar wuya a wannan gwamnati.

Wannan da ma wasu dalilai ka iya zama sila a gwamnatance don a tallafawa wannan yanki na Arewa, duba da irin bakin talauci da rashin aikin yi da ya dabaibaye matasan wannan yanki.

Tun lokacin zuwa wannan gwamnati ta shugaba Muhammadu Buhari aka yi tunanin cewa, wannan yanki na arewa zai farfado tare da bunkasa musamman ta fuskancin ayyukan noma da aka dade ana yi tun kaka da kakanni.

Sai dai abubuwa da suka biyo baya, sun canza tunanin mutane kwarai da gaske, saboda haka kuwa ya koma gefe ya fara tunanin abinda zai zame masa madogara, domin dai jiran kawon shanu ba zai yi wa kowa amfani ba.

A dalilin haka, jikin kowa ya yi sanyi, sai dai kaiwa aka ga gwamnatin shuagaba Buhari ta dage wajan bunkasa wannan bangare na harkar jirgin kasa wanda daman ana jiransa a wannan yanki, domin dai yana daya daga cikin cigaban da duniya tasa gaba.

Idan har dama ta samu, wannan yanki na arewa ya amfana da wannan aikin na tiriliyoyin nairori to lallai yankin arewa kakarsa ta yanke saka, zai fara bankwana da bakin talaucin da ya yi masa katutu.

Haka ita ma maganar zaman kashe wanda da matasa miliyoyi suke yi, akwai tabbacin zai rage so sai da kaso mai yawa, domin babu yadda za a yi a kawo wannan cigaba kuma a cigaba da samun irin wadannan matsaloli.

Mutanen Arewa tuni suka kosa da ganin an kawo wannan cigaba, amma sai yanzu a wa’adin mulkin shugaba Buhari karo na biyu abin ya iso yankin arewa ta karshe in nufin jihar Katsina.

Ganin yadda aka tsara wannan layin dogo da zai taso daga jihar Kano ya biyo ta Danbatta zuwa Daura ya ratsu ta Mashi zuwa Katsina ya wuce Jibiya sannan ya yada zango a jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar, yasa kowa ke maida hankalinsa wajan hangen bunkasar kasuwancin a wannan wurare.

Sai dai kadda a manta, baban fatan da ake da shi a yanzu shi ne ganin an fara wannan aikin an kuma gama lafiya domin sai wannan aikin ya tabbata ne kuma wakana sannan wadanan abubuwan da na lissafa za su kasance.

Mu na ganin irin yadda ayyukan wannan gwamnatin suke tafiyar hawainiya wajan aiwatar da su, saboda haka baban fatanmu anan shi ne shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki akan wannan sha’ani su dubi Allah ayi wa arewa wannan kokarin a karon farko, wannan aiki ya samu cikin lokaci kuma cikin nasara.

Ba a fatan kuskurewa domin wannan kamar ita ce dama ta karshe da wannan yanki ya samu, bayan ya samu tagomashi daga wannan gwamnati ta Buhari da jami’ar sufuri da kuma kwallejin gwamnatin tarayya duk a garin Daura yanzu kuma ga wannan baban aiki, bayan ga wasu da lokacin ba zai bari a yi bayani ba.

Masana tattalin arzikin sun bada tabbacin ire-iren wadannan ayyuka za su taimaka matuka gaya wajan farfado da tattalin arzikin da ya yi doguwar suma, amma akwai abubuwa da suka bayyana za su faru, kafin fita daga wannan kangi baki daya.

Sun bayyana cewa an yi wa tattalin arzkin mugun rauni saboda haka sai an samar masa da magani an raini shi kafi ya tashin ya farfado ya kuma dawo cikin hayyacinsa wanda daga nan ne ake fatan cewa al’umma suma za su dawo cikin hankalisu ta wannan fuska.

Idan duk wannan yanki na arewa ya tsallake wadancan gadoji na aikin wannan hanya ta layin dogo ma’ana an samu yinsa cikin lokacin an fitar da kudi an baiwa ‘yan kwangila an tsawata an bi su kwaf da kwaf sun yi aiki mai nagarta an kaddamar da shi, to shikenan zance zai kuma sabo fil a leda.

Haka kuma ya kamata a yi duba da idon basira dangane da wannan batu mai matukar mahimmaci, duk inda ake maganar tattalin arziki to magana ce baba da ya kamata a sa hankali da zurfin tunani wajan yin ta, muna ganin irin abubuwan da suka faru kafin bayar da kwagilar wannan aiki na layin dogo.

Misali, yanzu kuwa zai maida hankali da tunaninsa cewa harkar kasuwanci zata bunkasa ta wannan hanya, inda za a rika cinikaiya daga wasu kasashe makwabtan Najeriya zuwa cikin Najeriya, sai dai kadda a mata wannan harka fa ba abu ne da zai faru ba salin alin a wannan gwamnantin ba .

Batun rufe kan iyakokin Najeriya alama ce ta cewa, idan har ba gwamnati ta sauya tunaninta ba, har gobe akwai sauran rina a kaba, domin  kuwa zai so ganin yadda za a bude hada-hadar kan iyakokin Najeriya domin cigaba da wannan kasuwanci da zai taimaka wajan farfado da tattalin arzikin wannan yanki na arewa da aka samar da wannan layin dogo domin su.

Ko yanzu nan, shugaban kasa ya bada umarnin bude kan iyakokin domin cigaba da wasu huddudin da aka dakatar da su tsawon lokaci, amma rahotanni na cewa su fa shugabanin hukumomin tsaro musamman kwastan sun ki bin wannan umarni domin a fara cigaba da harkokin da aka amince da su a hukumunce.

Ko shakka babu hakan na nuna inda ake dai, nan ake ba a motsa ba balanta a fara tafiya, rijiya ta bada guga ya hana, kuma akwai tabbacin cewa shugaba Buhari ya kauda kai da wannan batun domin ba a kara jin ya ce uffan ba game da wannan bude kan iyakokin ba.

Bakar azaba da al’ummomi daban-daban suka sha ko kuma suke cigaba da sha a dalilin rufe bodojin Najeriya har gobe ba su fita ba, to idan aka kawo wannan layin dogo, ya  za a yi ke nan, wasu za a ba dama su yi kasuwanci ko kuwa wadanda daman suke cikin harkar ne za su cigaba da yin ta?

Sannan wani abu mai matukar mahimmacin da ya kamata kowa ya sani shi ne, wannan aikin bashi ne za a ciyo domin ayi shi, kuma har gobe ba a bayyana ta hanyar da za a biya wannan bashi ba, sai dai ana tunanin gwamnatocin masu zuwa za su cigaba da biyanshi ko suna su ko ba su.

Muna fatan wannan gagarumin aikin da wannan gwamnati ta yi tunanin yi a wannan yanki na arewa domin farfado da tattalin arzikin wannan yanki yasa ya zama mai amfani koda hamsin bisa bisa hamsin ne.

Domin shi ya fi komin sauki ayi shi domin arewa, amma wasu daga wata uwa duniya su zo su fi kowa cin amfaninshi, Allah Ya sawake.

 

Idan Allah ya kai mu sati mai zuwa zan cigaba daga inda na tsaya.

Exit mobile version