Idris Aliyu Daudawa" />

Ko Madara Na Rage Kaifin Ciwon Gyambon Ciki?

Yawancin mutane suna ganin cewar madara taba kawo saukin gwambon ciki abinda aka fisani da ulcer, wasy daga cikin masu fama da ita cutar suna shan madara mai yawa, saboda suna da wannan tunanin, amma kuma su masana sun bayyana cewar irin wannan al’amari yana sanar da matsalar fiye da kawo gyara. Saboda hakan yana taimaka ma wajen samar da wasu sinadaran juice da kuma acid na ciki.

Amma kuma kamar dai yadda Mrs Sarah Abagi ta bayyana gaskiya ne madara tana samar da babbar matsala, ta wani tumbi wannan kuma zai kawo wata matsala ta bangaren yadda su sinadaran gastric su ma za su iya shida marsala daga nan su samar da wani zafi mai tsanani ga shi gyambon cikin, maimakon kawo sauki.

Da kuma aka tambaye ta wasu al’amuran da akan yi wadanda suka hada da jika plantain shan tafarnuwa, zuma da kuma citta, za su iya samar da sauki, sai ta bada amsar a  matsayin ta na wadda ta kware a bangaren kayayyakin abinci, ta fi sabawa da mutane su yi amfani da madara. Hakanan kuma ita bata san sauran wasu abubuwa ba, wadanda marasa lafiya suke amfani dasu sai dai idan sun yi magana akan su.

“Wannan lokaci mutane suna yin duk abubuwan da suka ga dama, mu kuma ba zamu iya cewar wani abu ba, akan abubuwan da mutane suke yi, wadanda kuma bai kamata ace an ci gaba da yin su ba, kamar dai yadda ta jaddada.

Don haka ta bada shawara maimakon a rika amfani da madara ya kamata mutane su rika amfani da ruwan ganyaye masu taimakawa wajen kwantar da sinadarin acid da yake cikin jiki.

Kwararriyar a bangaren kayayyakin abinci ta bayyana cewar bai kamata mutane su kaurace ma ganuaue ba, lokacin da suka fama da gyambon ciki ko kuma ulcer.

Ta bayyana cewar “Idan mutane zau ci ganyaye to sai su ci wdanda basu da wata matsala, kamar karas, spinach, ruwan lemun, wadanda suke da alkaline wadanda suke taimakawa wajen kawo sauki wajen zafin da ciki yake yi.

Ta kuma bayanin cewar mutanen wadanda suke da ulcer wato gyambon ciki ya kamata su rika cin ganye cikin abincinsu, su kuma tabbatar da suna cin abinci a daidai lokacin daya dace.

“Mutum ya samu lokaci ya tauna abinci sosai saboda ba za a samu wanda ya rage ba wanda zai iya samar da matsala ga shi gyambon cikin ba, a kuma tabbatar da abincin bai da maiko sosai, bai kuma da zafi.

Exit mobile version