Ko Manchester City Za Ta Hakura Da Dan Wasan Gabanta?

Manchester City

Tuni dan wasa Harry Kane ya bayyanawa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham cewa zai ci gaba da zama a kungiyar wanda hakan ya kawo karshen cece-kucen da ake yi na cewa zai koma Manchester City a wannan kakar.

Kyaftin din tawagar ta Ingila, Harry Kane ya ce zai ci gaba da zama a Tottenham a kakar bana, zai mayar da hankali kan samarwa da kungiyar nasarori kamar yadda ya saba yi duk shekara. Tun farko an sa ran Manchester City ce za ta dauki dan kwallon a kakar nan, bayan da ya nemi izinin barin kungiyar daga shugaban kungiyar Daniel Leby, sai dai Leby bai yadda ya kulla wata sabuwar yarjejeniya da dan wasan mai shekara 28 ba.

Kane ya buga wa kungiyar wasan farko a bana a Premier League da Tottenham ta je ta doke Wolberhampton 1-0 a Molineud, kuma kociyan kungiyar, Nuno Espirito Santos ya ce labari ne mai kyau da Kane ya kawo karshen makomarsa a Tottenham da cewar zai ci gaba da zama.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta  Pacos de Ferreira a Europa Conference League ranar Alhamis, bayan da ta yi nasara a wasan farko da ci 1-0 a fafatawar cike gurbi. Kane wanda kwantiragin sa zai kare a karshen kakar wasa ta 2024, ya sanar zai ci gaba da buga wasa a Tottenham, saura kwana shida a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai ranar 31 ga watan Agusta.

Kyaftin din tawagar Ingila bai buga wa Tottenham wasan makon farko da Tottenham ta ci Manchester City 1-0 a gasar Premier League da karawa da Pacos de Ferreira a Europa Conference League.

Exit mobile version