Ko Nijeriya Za Ta Iya Lallasa Maroko A Wasan Karshe?

Tawagar ‘yan wasan Nijeriya ta Super Eagles ta kai wasan karshe na cin kofin nahiyar African ‘yan wasan cikin gida bayan ta doke kasar Sudan da ci 1-0, a wasan da suka buga na ranar Laraba.

Wannan ne karo na farko da Nijeriya ta samu zuwa wasan karshe na gasar tun bayan da aka fara buga gasar.

‘Yan wasan tawagar Super Eagles din sun samu zuwa wasan karshen ne bayan sun doke kasar Sudan da ci daya mai ban haushi, ta hannun dan wasa Okechukwu Gabriel a daidai minti na 16 da fara wasan.

Tun da farko dai masana harkokin wasanni sun bayyana damuwarsu ga yanayin yadda ‘yan wasan suke buga wasanninsu musamman a wasannin da suka buga a baya, inda ‘yan wasan ba su buga abinda aka yi zato ba.

Wasan da suka buga kusa dana kusa dana karshe wato ‘Kuarter final’ da kasar Angola Nijeriya aka fara zura wa kwallo a raga, kafin daga bisani su farke kuma su kara, wanda hakan ne ya ba su damar zuwa wasa na karshe.

Yanzu Kasar Maroko ce mai masaukin baki, kuma da Nijeriya za su fafata a wasan na karshe, wasa ne wanda zai dauki ‘yan kallo ganin yadda kasar Maroko take buga was anta, yayin da ita ma Super Eagles ta Najeriya take buga wasa wanda ake ganin suna buga wasa mai kayatarwa.

A wasannin da Nijeriya ta buga a baya tana buga wasan zari-ruga ne wanda kuma irinsa kasar Morocco take bugawa, hakan ya sa ake ganin wasan karshen zai kayatar sosai.

 

Sai dai mai tsaron ragar tawagar ta Super Eagles, Ikechukwu Ezenwa, dan kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ba zai samu buga wasan na karshe ba, sakamakon ciwo da ya ji a wasan kusa dana karshe, sai dai tafiyar tasa ba za ta zama matsala ba, sakamakon a kwai wanda zai maye gurbinsa, mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Plateau United, Dele Ajiboye.

Nijeriya dai tana bukatar samun nasara a wasan domin kafa tarihin lashe gasar, sai dai za ta fuskanci kalubalen mai masaukin baki, Maroko wadda ita ma ba kanwar lasa ba ce. Za’a buga wasan na karshe dai a ranar Lahadi da misalin karfe 8 na dare a filin wasa na Muhammad B dake birnin Casablanca.

 

Exit mobile version