Idris Aliyu Daudawa" />

Ko Rashin Karin-kumallo Na Iya Sanadiyar Mutuwar Mutum?

Lokuta da dama akan bayyana karin-kumallo a mastayin mafi muhimmancin abincin da ya kamata a ci a ko wacce rana, musamman ga rayuwar dan adam.

Wani bincike da kwalejin da ke nazarin cututtukan zuciya a Amurka ta yi, wanda kuma aka wallafa shi a cikin watan Afrilu, ya ce tsallake cin abinci da safe na iya haddasa cututtukan zuciya masu janyo mutum ya rasa ransa.

Tawagar wasu Likitoci da masu bincike daga jami’o’i masu yawa daga Amurka ne suka gudanar da shi binciken.

Tawagar ta nazarci mutane 6,550 da shekarunsu suka fara daga 40 zuwa 75 da ke kan wani tsarin kiwon lafiya tsakanin 1988 da kuma 1994.

Mutanen da aka gudanar da binciken akan su sun bayanna sau nawa su ke yin karin-kumallo.

Kashi biyar cikin 100 na wadanda aka yi nazari akansu sun bayyana cewar ba su taba yin karin-kumallo ba, kashi 11 kuma sun ce da kyar suke yi, su kuma kashi 25 sun ce suna ci amma ba sosai ba.

Masu binciken sun kuma duba yawan wadanda suka rasa ransu zuwa shekara ta 2011 – mutum 2,318 cikin wadanda suka shiga shirin sun mutu – sai suka duba yawan cin abincin safen su.

Binciken lafiya ya bayyana cewar shi al’amarin tsallake karin-kumallo, ko kuma cin abincin safe, na iya yin mumunar illa ga lafiyar jiki, sai dai masanan kimiyya har yanzu na kokarin gano alakar wadanan abubuwan biyu.

A wani tsokaci da ta yi kan binciken, ma’aikatar lafiya ta Birtaniya ta wallafa wasu kalamai cewa jaridar ta Amurka, ”ba za ta iya tabbatar da cewa rashin karin-kumallo ne ke saka cututtukar zuciya ba. Yawancin mutanen da binciken ya gano cewa ba sa karin-kumalo sun taba shan Taba, ko giya ko ba su cika motsa jikinsu ba, ko kuma ba sa cin abinci mai kyau.”

Gidauniyar kulawa da yawan jama’a da kuma ci gaba a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, UNEPA ta yi kira ga kasar Nijeriya cewar ta kara zage damtse domin tabbatar da, an dauki wasu sababbin hanyoyi wadanda za suyi maganin mutuwar mata masu juna biyu. Dukkan matsalolin da ake fuskanta dangane da hakan kamata ya yi, ace an samu kawo karshensu, sai kuma shiga tsarin iyali da kuma tabbatar da an ganin an daina yin dabi’ar nan ta yadda ake zaluntar wani jinsi hakanan.

Jami’in asusun da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke kulawa da al’amarin na Nijeriya, Mista Edward Kalion ne wanda ya yi wannan kiran, wajen bikin gidauniyar, wanda ta cika shekaru hamsin, da kuma taron da aka yi a kasar Masar shekaru 25 da suka wuce na ICPD. Wato taron yadda za a tunkari yawan jama’a na duniya da kuma cigaban su a shekarar 1994.

Ya ci gaba da bayanin cewar duk kuwa da yake akwai cigaban da aka samu tun daga shekarar ta 1994, wani abu daya wanda ya rage shine, har zuwa yanzu ba a cimma muradin matakin da aka dauka, a taron na Cairo wanda ake sa ran duk al’ummar duniya za su amfana da shi muddin idan an aiwatar da matakin da aka dauka. Kamar dai yadda ya cigaba da bayani, shi cigaba kamata ya yi ko wanne sako da lungu ya san cewar shima ana yi da shi. Ga kuma mata da ‘yan mata har yanzu shi burin nan da yakamata ace an cimma mawa, basu san ma halin da ake ciki ba.

Kasashen duniya mata 800 da yawa suna mutuwa  ko wacce rana a sanadiyar matsalolin da suke fuskanta, lokacin da suke da Juna Biyu wato Ciki da kuma haihuwa. Sai kuma wasu 111 wadanda suke mutuwa ko wacce rana lokacin haihuwa. Bayan nan ma da akwai yanzu mata miliyan 214 wadanda su basu son daukar Ciki, sai dai kuma basu son yin amfani da maganin hana haihuwa na zamani.

A kasar Nijeriya daya daga cikin mata hudu wadanda suke son amfani da maganin hana daukar ciki, basu da hanyar da zasu yi hakan. Bugu da kari kuma akwai miliyoyin mata wadanda matsalar yake- yake ta shafa, da kuma sauran matsaloloi daban- daban ba za su iya haihuwa ba.

Ya yi karin haske wanda yake nuna duk da yake su kasashen duniya suna dai imanin za su iya cimma shi burin, wato na muradan ci gaba ko kuma SDG nan da shekara tya 2030, kuma lalla kuma akwai ita maganar matakin da aka dauka lokacin taron ICPD a Cairo babban birnin kasar Masar.

Exit mobile version