An bayyana cewa zaben 2015 da aka gudanar a kasar nan daya kawo Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki ya karbi Gwamnati cikin ruwan sanyi saboda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ana kada shi kafimma a fadi sakamakon zabe, ya yi mubaya’a ya taya Buhari murna, ya nuna juriya da karbar kaddara, wanda ba a taba yin haka a duk fadin Afrika ba. Daya daga cikin yan jam’iyyar PDP a jihar kano masu biyayya ga Kwankwasiyya.Alhaji Nasiru Husaini Agalawa ya bayyana haka da yake bayyana hasashensa game da daga zabe da aka yi.
Ya ce, a siyasar Buhari ba zai iya wannan rungumar kaddara ba yazo dan yazo yana kuka da tsadar rayuwa a lokacin a lokacin ana sai da ledar taliya Naira 80 ana sayar da litar man fetur Naira 85 amma da saida ya hau taliya takai Naira 200 man fetur N145 a baya idan mutum 10 ka gani a Kano kafin Buhari ya hau mulki na sane, amma yanzu da kyar zaka samu uku a cikin goma nasa saboda an gane maganarsa a baki daban-daban dana zuci .
“Wannan daga zabe akwai tabbacin APC bata da nasara ne da yardar Allah PDP ce ke da nasara, kosu bayar ko karsu bayar ko su yi zabe na gaskiya ko akasin haka PDP ce da nasara manuniya ta tuna idan aka yi zabe na gaskiya mune da nasara”cewar Agalawa. Tashin kaya ba a taba samun irin wannan ba zuwan Buhari, da mai hali zai iya sayen mota da bata wuce Naira 400,000 ya bayar kyauta ga jama’a yanzu wannan ita ce kusan Miliyan daya ba a iya saye.
Ya yi nuni da cewa kasar Saudiyya basu kaimu yawa ba, duk abin da suke ci shigo musu da shi ake amma nan da akeda kusan mutum miliyan 200,000,000. An ce ba za a kawo musu abinci ba bayan ba kowane yake noma ko halin noma ba. Hatta aikin hajji kafin Buhari da miliyan daya saika biyawa mutum biyu amma yanzu ko mutun daya bazai isa ka biyawa ba. Buhari duk maganarsa PDP ta lalata kasa shi kuma gashi yazo ya gaza tun mulkinsa na soja ya canza kudi a kwana bakwai, yasa kudimmu samun rauni a duniya.
Duk Duniya in kazo mulki sai ka nemi masana su fada maka hanyar gyara, amma shi ba ruwansa da kowa domin ya nuna shiya iya, shi ne mai gaskiya ya zai sami nasara da ake zato?
Alhaji Nasiru ya ce, dan haka dan an daga zabe, a hasashensu rashin nasara aka hango, ba sati daya ba ko shekara aka daga sai ya fadi, sai PDP ta karbi Gwamnati.Wasu ma da suke son Buharin wannan daga zabe ya sa sunce ba za su yi shi ba.
Alhaji Nasiru Husaini Agalawa ya ce, su yan Kwankwasiyya suna da biyayya da hadin-kai basa makauniyar biyayyya da Buhari ya gyara kasa, za su iya binsa. Ko zage-zage ba su yarda su yi da dan wata jam’iyya ba dan ba su da inda yafi kasar nan gyara suke so. Don a ci gaba da yi wa Gwamnati biyayya, duk abin da ta ce a yarda inta daga zabe, a yarda in ta ce, azo ayi, a fito ayi zabe domin PDP ta karbi Gwamnati a ci gaba da samar da romon dimakradiyyar da da al’umma za su anfana ta fannoni da dama a inganta tsaro a kauda talauci idan suka karbi Gwamnatin tarayya dana Kano.