Sharfaddeen Sidi Umar">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Ko Talakawa Na Amfana Da Zakka Da Wakafi A Sakkwato?

by Sharfaddeen Sidi Umar
January 29, 2021
in RAHOTANNI
4 min read
Ko Talakawa Na Amfana Da Zakka Da Wakafi A Sakkwato?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kwamitin Sadaka da Rarraba wa Mabukata na Jihar Sakkwato wanda gwamnan mulkin soji, Kanar Yakubu Mu’azu ya assasa a 1996, gwamnatin Aliyu Wamakko ta karfafa tare da mayar da shi Kwamitin Zakka da Wakafi a 2007, ya zama hukuma a karkashin Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal a 2016 sakamakon daga darajarsa domin samun cikakken ‘yancin cin gashin kai, da inganta ayyukan hukumar da tallafa wa al’umma kamar yadda ya kamata a karkashin jagorancin Malam Muhammad Lawal Maidoki.

Hukumar Zakka da Wakafi (SOZECOM) wadda ke karbar makudan kudade a kowane wata daga gwamnatin jihar domin share hawayen marasa galihu ta fuskoki da bangarori da dama, an tsara ayyukan ta domin su karade kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato bakidaya.
Shin ko talakawa, marasa galihu da ‘yan rabbana ka wadatu mu suna cin moriyar ayyukan Hukumar wadda aka yi domin su? Ko kuwa suna kuka da kokawa kan rashin sauke nauyin da aka dorawa Hukumar a shekaru da dama zuwa yau?
A tsayin shekaru sama da shida na mulkinta, Gwamnatin Tambuwal ta kan baiwa Hukumar Zakka da Wakafi wadda ke a karkashin Ma’aikatar Lamurran Addini, tsabar kudi naira miliyan 31, 500 a kowane wata domin gudanar da aikin ta yadda aka shata na tallafawa mabukata.
Hukumar wadda ke karbar Zakka da Wakafi daga bayin Allah tare da rarrabawa mabukata a Gundumomi 85, sunan ta ya yi katutu a zukatan Sakkwatawa a Birni da karkara a bisa ga yadda jama’a ke ribanta da shiraruwanta. Hasalima a kowace shekara Hukumar kan bayyyana karamar Hukumar da ta yi zarra wajen bayar da Zakka da Wakafi wanda galibi nau’ukan kayan abinci ne da dabbobi da kudi. Haka ma Hukumar kan karfafawa mutane da daman gaske maza da mata ta hanyar horas da su sana’o’i da ba su jari domin ganin sun zamo masu dogaro da kai a halastattun sana’oi.
A kan wannan Hukumar ta raba dubban teloli, injunan nika, na’urar sanyaya ruwa, kayan aski, nau’ukan abinci da kayan dafuwar abinci da sauran su da dama domin kuwa a ta bakin Shugaban Hukumar Malam Lawal Mai-Doki ya yi amannar “A koyawa mutum kamun kifi ya fi a bashi kifi.”
Binciken LEADERSHIP A YAU JUMA’A ya nuna cewar Hukumar kan taimakawa marasa lafiya wadanda ba su da halin neman magani da musamman wadanda ke jimawa da cuta har ta ci ta canye ba tare da magani ba. “Ba ka bukatar sai an san ka, ko kuma sai wani sannane ya yi maka hanya kafin a tallafa maka a Zakka da Wakafi, ko kadan babu siyasa a cikin ayyukan mu, a kan yi komai ne a bisa ga cancanta.” In ji Mai-Doki wanda shine Sadaukin Sakkwato.

A wani lamari irinsa na farko a Jihar a tsayin shekaru, Hukumar kan kai kudade a asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu danfodiyo (UDUTH) da Asibitin kwararru ta Jiha, da Asibitin WCWC da Asibitin masu tabin hankali da ke Kware da kuma Asibitin mata da kananan yara ta Maryam Abacha da Asibitin kashi da ke Wamakko duka a Sakkwato wadanda ake baiwa kudade kama daga dubu 500 zuwa naira miliyan biyu a kowane wata domin taimakawa marasa galihu.
Baya ga wannan manyan dakunan shan magani kamar Raudha, Mai-Gobir, Nasiha da kuma Zumunchi duka Hukumar na kai masu kudade kama daga naira dubu 300, dubu 500 zuwa dubu 700 a kowane wata domin bayar da magani ga mabukatan marasa lafiya a ta bakin Mai-Doki.
Shin ko Gwamnatin Tambuwal na tallafawa marayu maza da matan da suka rasa iyayen su domin nuna masu cewar su ma ‘ya’ya ne? Wakilinmu ya labarto cewar tuni marayu suka zama ‘yan gata a Gwamnatin Tambuwal domin kuwa Hukumar Zakka da Wakafi kan kebe naira miliyan 2, 000, 000 a kowane wata domin tallafawa iyayen marayu domin su ja jarin sana’o’i daban-daban domin daukar nauyin marayun da aka bar masu. Haka ma ta kan koyawa marayu sana’oi da ba su jari domin su dogara da kan su.
Daga cikin kudaden da Hukumar ke karba a kowane wata ta kan cire naira miliyan shida domin lalurorin marasa lafiya a duk wata. Haka ma a kowane wata Hukumar Zakka da Wakafi kan yi wa akalla mutane 500 magani a Asibitin masu fama da tabin hankali da ke Kware, suna kuma kwantar da marasa lafiya kamar 35, 40 zuwa 50 daga cikinsu wadanda cikin ikonsa Ubangiji kar warkar da tabin hankalin da ke garesu su dawo suna rayuwa cikin mutunci.
“Na jima cuta na wahalar da ni, kuma ba ni da hali, aka ba ni shawarar neman taimakon Hukumar Zakka da Wakafi wadanda suka tallafa mani kuma na samu lafiya. Daga baya kuma na sake samun tallafin sana’a don haka ya zama wajibi in gode masu.” In ji Tukur Mamman.
Daga cikin ayyukan jinkai da Hukumar Zakka Da Wakafi ke aiwatarwa akwai bayar da tallafin kudi naira 6, 500 a kowane wata ga makafi, kutare da guragu marasa karfin da ke cikin rajista a kananan Hukumomi 23 domin inganta jin dadin su da kawar da su a saman tittuna da sunan mabarata. “Ba shakka muna cin moriyar wannan shirin a tsayin shekaru wanda ya yi matukar tasiri a gare mu da iyalan mu.” In ji wasu da dama da suka amfana.

A bisa ga tasirin Hukumar da aminta da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi da ita wajen wanzar da gaskiya da adalci a ayyukanta, ta jagoranci Hukumar wajen bayar da tallafin Gidauniyar dangote ga mata 23, 990 wadanda Attajiri mafi kudi a Afirka da kansa ya yi tattaki ya karfafawa da naira dubu 10, 000 ga kowace mace daya ciki har da wadanda ke a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira da ke a Rabah domin zama masu dogaro da kai.
Duka baya ga wanna a kokarin ta na taimakawa al’umma da sanyaya zukatan su a watan Ramadan mai albarka; Gwamnatin Jihar Sakkwato a kowace shekara kan fitar da daruruwan miliyoyin kudade a uwar Hukumar Zakka da Wakafi wato Ma’aikatar Lamurran Addini da ita kanta Hukumar domin tallafawa mabukata a lokutan Azumi da bukukuwan Sallah karama da Sallah Babba.
Daga ciki a kan sayi abincin da ake rabawa marasa galihu tare da tufafi da kuma manyan dabbobi a lokutan Sallah domin marasa galihu da musamman marayu su gudanar da shagalin Sallah cikin walwala da jin dadi tamkar iyayen su na numfashi a duniya.
Hukumar Zakka da Wakafi wadda ta kan shiga lungu da sakon ciki da wajen jiha domin ilmantar da sababbin Musulunta, haka ma a kwanakin baya da hadin guiwar Gidauniyar tallafawa al’umma ta katar sun gudanar da shirin duba idanun marasa lafiya 1, 000 wadanda aka baiwa magani tare da yi wa wasu aiki kyauta. Haka ma Hukumar a lokuta mabambanta ta kan jagoranci dashen itacen da ke bunkasa tattalin arziki da yaki da gurgusowar Hamada a matsayin Wakafi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yawaitar Hadurran Ababen Hawa A Nijeriya (III)

Next Post

Korona Ta Kashe Mutum 27 A Nasarawa, Ana Tsimayen Sakamakon Gwajin Mutum Dubu – Gwamna Sule

RelatedPosts

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Sharfaddeen Sidi Umar
8 hours ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Tuhumar Malam Abduljabbar Za A Yi, Ba Mukabala Da Shi Ba– Sheikh Khalil

by Sharfaddeen Sidi Umar
2 days ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja Shugaban Majalisar Malamai na Shiyyar...

ISWAP

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai Bakwai A Dikwa

by Sharfaddeen Sidi Umar
2 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri A harin bayan nan da mayakan...

Next Post
Korona Ta Kashe Mutum 27 A Nasarawa, Ana Tsimayen Sakamakon Gwajin Mutum Dubu – Gwamna Sule

Korona Ta Kashe Mutum 27 A Nasarawa, Ana Tsimayen Sakamakon Gwajin Mutum Dubu – Gwamna Sule

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version