Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ko Wasu ’Yan Siyasar Austriliya Sun Zama Mahaukata Wajen Adawa Da Kasar Sin Sakamakon Rudanin Tunaninsu

Published

on

Kwanakin baya, ma’aikatan leken asiri na Austriliya fiye da goma sun kutsa kai cikin gidan Shaoquett Moselmane, dan majalisar jihar New South Wales ta kasar, don neman shaidun tabbatar da zargin da ake masa cewa ya tuntubi kasar Sin cikin sirri. Amma, bisa labaran da kafofin yada labaran kasar suka bayar, an kutsa gidan Moselmane ne saboda ya taba ziyartar kasar Sin sau da dama, kuma yana da ra’ayin sada zumunta da kasar Sin. An ce, a watan Maris, ya taba rubuta wani sharhin amincewa da kokarin da Sin ta yi wajen yakar COVID-19, sabili da haka, ake daukarsa a matsayin “Mai son kasar Sin”, har ma ya fuskanci suka a siyasance. Ban da haka, ’yan sandan Austrilya sun kuma kai hari kan wasu manema labaran kasar Sin dake aiki a kasar. Shin wannan ce kasar dake ikirarin cewa, tana hakuri da bangarori daban-daban?
A ran 1 ga watan, Austriliya ta sanar da sabon tsarin tsaron kasa, wanda ya yi shirin samar da kudin Australian dollar biliyan 270 a cikin shekaru 10 masu zuwa don kara karfinta na tsaron kasa da zummar jibge sojojinta a tekun India da ma Pacific. Firaministan kasar Scott Morrison ya ce, yana mai da hankali sosai kan bunkasuwar kasar Sin wadda ke barazana ga duniya. Ana iya ganin cewa, wannan matakin da Austriliya ta dauka na hadin kai ne da Amurka don matsawa kasar Sin lamba.
Wasu manazarta suna ganin cewa, bisa jeren sunayen makaman da Austriliya za ta saya da yawancinsu kirar kasar Amurka ne, babu shakka mataki ne na ajiye kudi a cikin aljihun masu sayar da makamai ’yan Amurka.
A cikin shekaru 10 da wani abu da suka gabata, saurin bunkasuwar masana’antu da birane ya samar da dauwamammen bukata ga Austriliya a fannin ma’adinai da makamashi da kuma amfanin sha’anin gona da kiwon dabobbi da dai sauransu. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar kasar ta bayar, a shekarar 2019, yawan kudin dake shafar fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin ya kai dala biliyan 103.9 wanda ya karu da kashi 18%, adadin da ya kai kashi 38.2% bisa na dukkan kudin da kasar ta samu wajen fitar da kayayyaki zuwa ketare. Sin tana rike da matsayin abokiya mafi girma ta fuskar ciniki da kasa mafi girma wajen fita da shigar da kayayyaki Austriliya. Ana iya cewa, Austriliya ta ci gajiya matuka daga hadin kan kasashen biyu a fannin ciniki, keta wannan dangantaka babu wani amfani da zai mata, sai dai ma illata muradun jama’ar kasar.
A wani bangare, Austriliya tana son cin gajiya daga saurin bunkasuwar kasar Sin, amma a wani bangare, tana yunkurin nuna adawa ga kasar Sin don farantawa Amurka. Mahaukatan ’yan siyasar Austriliya ba su fahimci harkokin siyasar kasa da kasa ba ko kadan. Babu shakka, wasu ‘yan siyasa sun fahimci cewa, daidaita manufofin da suke dauka kan kasar Sin a maimakon zama inuwa guda da Amurka, hanya ce daya tilo da za a bi wajen kiyaye jama’ar kasar, don kada su bayyana kansu kamar mahaukata. (Amina Xu)
Advertisement

labarai