Connect with us

WASANNI

Kociyan Kasar Uruguay Ya Sake Sabon Kwantaragi

Published

on

Kocin kasar Uruguay Oscar Tabarez ya sake rattaba hannun tsawon shekaru hudu da hukumar kwallon kafa ta kasar inda zai cigaba da zama mai horas da kungiyar har zuwa shekara ta 2022 bayan kammala gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Katar.

Kocin mai shekaru 71 a duniya, yana fama da ciwon Neuropathy wanda a sanadin haka baya iya tafiya sai da sanda, kuma shi ne mai horarwa na farko a tarihin kwallon kafa da ya taba jagorancin kungiya zuwa gasar cin kofin duniya har sau hudu, yanzu kuma yana harin na biyar a kasar Katar.

Tabarez shi ne horaswa da yafi kowanne adadin wasanni a matsayin koci da wasanni 185 kuma ya kware wajen koyawa tawagar ‘yan wasan kasar kwallo inda aka bayyana babu kamarsa a nahiyar kudancin amurka

Kafin karbar ragamar jagorancin kungiyar kwallon kafa ta kasar Uruguay, ya fara horas da kungiyoyi daban-daban a cikin kasar ta Uruguay da kuma kasar Colombia, tare da kungiyar kwallon kafa ta Borca Junior dake kasar Argentina, sai kuma babbar kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dake kasar Italiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: