Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Roland Koeman, ya mayarwa da tsohon dan wasan kungiyar Andries Iniesta martini bayan da tsohin dan wasan ya bayyana cewa za’a dade kafin a shawo kan matsalar da kungiyar take ciki.
A kwanakin baya ne tsohon dan wasan Andries Iniesta, ya bayyana cewa idan shugabannin kungiyar ta Barcelona basu tashi tsaye ba zasu dade basu shawo kan matsalar kungiyar ba kuma hakan babbar barazana ce.
Sai dai kalaman na Iniesta basu yiwa Koeman dadi ba wanda hakan yasa ya fito ya bayyana cewa bai kamata tsohon dan wasan ya bayyana haka ba saboda kullum suna aiki tukuru wajen ganin sun kawo gyaran da yakamata a kungiyar.
Kakar kwallon kafa ta bana ta nuna rashin kokarin Barcelona a gasar cikin gida, amma tana haskakawa a gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League ta kakar wasa ta 2020 zuwa 21 wadda ake bugawa.
Barcelona tana tare da shugaba na rikon kwarya wanda ke son ragamar mulkin nan gaba, bayan da kungiyar ke fuskantar kalubalen biyan albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da cutar korona ta haddasa a fadin duniya.
Kawo yanzu Barcelona tana ta biyar a teburin La Liga da maki 24, bayan buga wasa 14 a kakar bana bugu da kari kungiyar wadda mai koyarwa Ronald Koeman ke jan ragama ta ci wasa bakwai a La Liga da canjaras uku da rashin nasara hudu da kwantan wasanni biyu.
Barcelona ta yi rashin nasara a wasanni da dama a bana kamar yadda ta yi a shekarar 2017 zuwa 2018 da kuma 2018 zuwa 2019 a La Liga, yayin da ta yi rashin nasara a wasa uku ta kuma lashe kofin a shekarar 2018 zuwa 2019.
Sai dai kuma Barcelona tuni ta kai zagaye na biyu a gasar Champions League ta bana da maki 15, yayin da Juventus take ta biyu da maki 12 a rukuni na bakwai kafin su fafata a wasan yau aga wadda zata zama jagora a rukunin nasu.
A kakar shekarar 2003 Enric Reyna shi ne ya rike Barcelona a matakin rikon kwarya, bayan da Joan Gaspart ya yi murabus daga baya Radomir Antic ya maye gurbin Louis van Gaal a matakin koci.
A waccan kakar Barcelona ta fuskanci kalubalen samun gurbin shiga gasar UEFA Cup, inda kungiyar ta sa kwazo ta kuma samu gurbin a wasan karshe da ta buga sannan kuma a lokacin Laporte ya kalli karawar a matakin shugaban kungiyar a lokacin da ya ci zave ya zama jagora na hudu a kungiyar a kakar.
A kakar wasa ta 2020 zuwa 21 za ta kammala ne da shugaba uku, bayan Josep Maria Bartomeu sai Carles Tuskuets na rikon kwarya da wanda za a zava ranar 24 ga watan Janairun shekara ta 2021.