Connect with us

LABARAI

Kofi Annan Ya Yi Nagartattciyar Rayuwa –Farfesa Moghalu

Published

on

Wani tsohon jami’in majalisar dinkin duniya, Farfesa Kingsley Moghalu, ya fada a ranar Asabar inda ya bayyana Marigayi Kofi Annan, a matsayin mutumin da ya yi rayuwa abar yabawa.
Moghalu, wanda mai neman tsayawa takarar Shugabancin kasar nan ne a karkashin tutar jam’iyyar YPP, kuma tsohon mataimakin babban bankin kasar nan ne, ya bayyana hakan ne a ta’aziyyar da ya aike na rasuwar ta Kofi Annan.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton mutuwar ta Kofi Annan, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na 7, a tsakankanin shekarun 1996 da 2007, a ranar Asabar ne ya rasu yana da shekaru 80.
Tsohon jakadan na kasar Ghana, ya taba karban lambar yabon nan ta, ‘Nobel Peace Prize,’ ya kuma jagoranci kawo sauye-sauye masu yawa a Majalisar ta Dinkin Duniya, domin kara karfafa ta.
Cikin sanarwar, Moghalu na cewa, “Na fara jinjina ta ne ga Kofi Annan a watan Afrilu, lokacin da ya yi bikin cikar sa shekaru 80 da haihuwa, da ‘yan wadannan baitocin: “Rayuwa zabi ne. Amma a yi zabi mai kyau. Tilas ne kasan ko kai wane ne kuma ka san matsayin ka, inda kake son zuwa da kuma dalilin da ya sa kake son zuwa wajen.
“Wadannan wasu zafafan kalmomi ne daga shi kan shi Mista Kofi Annan din, kalmomi ne da suka amfanar da ni matuka a kan aiki na da kuma rayuwa ta.
“Na jima ina yaba ma kwazonsa, wanda da shi ne yake karfafa ta da ma sauran mutane, ta yanda za mu iya zama ma’aikata nagari, mu kuma iya kafa hukuma mai nagarta.
“Shi a kankansa, ya yi namijin kokari a matsayin sa na shugaban wata babbar hukuma mafi inganci a duk Duniya, ya kuma bar abin koyi masu yawa.
“Cikin ta’aziyyar nawa, na rubuta cewa, ya yi rayuwa ce mai mahimmanci, ba domin kadai zamowan sa tamkar Nelson Mandela ba, ya ma kai wani matsayi ne na ciyar da rayuwar dukkanin bakaken fatan Afrika gaba, kamar irin na wasu kadan irinsa, ya ma so ya kawo wani irin sauyi ne a duniya, wanda kuma ya sami nasarar hakan.
“Ni kaina, kamar sauran milyoyin mutanan duniyar nan, mun yi rashin wannan babban mutumin. Ina mika ta’aziyya ta ga iyalansa, matarsa Nane Annan, ‘ya’yansa, da al’umman kasar Ghana, wanda suka yi rashi mai girma,” in ji Moghalu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: