Gwamnatin kasar Jamus ta ce ba zata bai wa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool izinin shiga kasar domin karawa da kungiyar da take wakiltar Jamus din ba, wato RB Leipzig a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da zai gudana ranar 16 ga wannan wata saboda matakan da kasar ke dauka na yaki da cutar korona.
Ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce ranar Alhamis Rundunar ‘yan Sandan kasar ta shaidawa kungiyar RB Leipzik kan matakin da aka dauka, bayan da kungiyar ta bukaci gwamnati da ta saukaka mata dokar wajen bai wa Liverpool damar ziyarar kasar.
Wannan mataki ya sa kungiyar Leipzig da Liverpool neman wani wuri yanzu haka inda za su kara domin kaucewa wancan mataki da gwamnatin Jamus ta dauka wanda bai yiwa kungiyar dadi ba.
“Tabbas mataki ne wanda baiyi mana dadi ba kuma baiyi wa kowa a wannana kungiya dadi ba amma a haka dole zamu hakura mu nemi hanyar da zamu bi wajen ganin mun samu damar buga wasan dake gaban mu” in ji shugaban kungiyar ta RB Leipzig
Kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig dai zata fafata wasa da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a gasar cin kofin zakarun turai na bana a zagaye na biyu bayan kammaka wasannin rukuni kuma wasan farko kamar yadda aka tsara kungiyar ta Jamus ce zata karvi bakunci.