Nasir S Gwangwazo" />

Kogi 2019: Ka Rungumi Kowa – Buhari Ga Bello

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga zababben Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, da ya rungumi kowa da kowa bayan sake lashe zaben jihar da ya yi a karo na biyu.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a sakon taya murna da ya aike wa Gwamna Yahaya a jiya Litinin, 18 ga Oktoba, 2019, bayan da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da shi Bellon a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Kogi, wanda a ka gudanar ranar Asabar da ta gabata, wato 16 ga Nuwambar nan.
“Ka rungumi kowa ta hanyar riko da kama hannayen ’yan takarar adawa,” in ji sanarwar Shugaban kasar, wacce mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya sanya wa hannu.
A yayin da ya ke taya gwamnan murnar lashe zaben, Buhari ya ce, “takara ce wacce a ka sha gumurzu, amma a ka yi kyakkyawar nasara.”
Sai ya yaba wa magoya bayan jam’iyyarsu ta APC, wadanda su ka dage su ka cigaba da mara mu su baya duk da irin dauki ba dadin da a ka samu. Sai kuma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga wadanda su ka jikkata ko ma su ka rasa rayukansu a yayin gudanar da zaben, musamman a dalilin ayyukan wasu ’yan daba wadanda ’yan siyasa su ka dauki nauyi.
“Dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa na da rawar da za su taka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a lokacin zabe, domin dorewa da wanzuwar dimukradiyyarmu,” in ji shi.
Buhari ya kuma gode wa INEC da jami’an tsaro bisa aiwatar da aikinsu cikin wannan matsanancin yanayi.
Daga nan sai ya ja hankalin Gwamna Bello da cewa, “wannan wata sabuwar dama ce a gare ka, wacce za ka dora ta fuskar inganta rayuwar al’ummarka ta jihar Kogi.”
Daga sai Shugaba Buhari ya yi kira ga wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben ba da su tunkari kotunan zabe maimakon tayar da hankalin jama’a, domin babu alheri a tayar da zaune tsaye.
Idan dai za a iya tunwa, babban jami’in zaben gwamnan da INEC ta nada, farfesa Ibrahim Garba, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU da ke Zariya, a jiya Litinin, 18 ga Nuwamba, 2019, ya sanar da cewa, Gwamna Bello na Kogi ya samu kuri’a 406,222, inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Alhaji Musa Wada, wanda ya samu kuri’a 189,704.

Exit mobile version