Ahmed Muh'd Danasabe" />

Kogi: An Halaka Masu Satar Mutane Da Kama Masu Tsegunta Mu Su

Kungiyar mafarauta da yan sintiri na neighborhood watch dake kananan hukumomin Okehi da Adabi sun samu nasarar hallaka masu garkuwa da jama’a su uku da kuma kama masu taimaka musu da bayanai su biyu akan babban hanyar Lokoja zuwa Okene dake jihar Kogi.
Masu satar jama’ar wadanda suke shirin kaiwa jama’a masu balaguro akan babban hanyar Lokoja zuwa Okene hari, dubunsu ta cika ne a ranan asabar a yayin da masu taimaka musu da bayanai suka shiga komar mafarautan da kuma yan sintirin.
Manyan masu taimakawa gwamna akan sha’anin tsaro masu kula da kananan hukumomin Okehi da Adabi, Hon Abdulkareem Ohiare da Hon Joseph Omuya Salami ne suka jagoranci mafarautan zuwa maboyar masu garkuwa da mutanen biyo bayan rehorun sirri da suka samu.
Mafarautan wadanda suke sintiri da misalin karfe 4 da 30 na sanyin safiyar ranan asabar, sun damke masu taimakawa masu garkuwa da jama’ar da bayanan, Godwin Peter, dan asalin kauyen Ikeje dake kananan hukumar Olamaboro da Sanni Habib dake Unguwar Idoji na karamar hukumar Okene.
Bayan anyi musu tambayoyi ne,sai suka amince da cewa su suke taimakawa masu garkuwa da jama’ar da bayanai yadda suke gudanar da aika aikansu,sannan daga bisani suka jagoranci manyan masu gwamna shawarwari akan tsaro na kananan hukumomin Okehi da Adabi da kuma mafarautan zuwa ainin maboyar masu garkuwa da jama’ar.
Zuwa maboyar ke da wuya, sai mafarautan suka fara musanyar wuya da masu garkuwa da mutanen inda nan take aka bindige uku daga cikinsu har lahira, a yayin da kuma sauran suka tsira da raunukan harbin bindiga.
Makaman da aka gano daga masu satar jama’ar sun hada da bindigogi kirar raful guda uku da harsashai da dama da amawali ko badda kama( face mask) da kuma asirai.
Da suke jawabai bayan samun nasarar dakile masu garkuwa da jama’ar, Hon Ohiare  da Hon Omuya sun godewa gwamna Yahaya Bello a bisa kudurinsa na samar da kwararan tsaro a da kuma kawar da ayyukan batagari a fadin jihar Kogi.
Sun kuma ce lallai kam gwamnan ya kafe a matsayinsa na cewa ko kadan ba zai sasanta ko yin sulhu da batagari ba, sannan suka shawarci batagarin da su sauya tunaninsu ko kuma yabawa aya zaki.

Exit mobile version