Umar A Hunkuyi" />

COVID-19: Kokarin Buhari Na Yaki Da Cutar Daga Janairu Zuwa Maris

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar nan a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, 2020, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shelanta cewa, “Yaki da annabar Kwaronabairus a Nijeriya, babu wani abu mai kama da wuce gona da iri, ko kuma nuna halin ko-in-kula a cikinsa. Duk abin da ake yi daukan matakin da ya dace ne daga hukumomin da suka dace da kuma bin shawarwarin kwararru.”

Domin gudun mantuwa, a nan kasa za mu kawo maku wasu matakan da hukumomi da kuma kwararrun jami’ai suka dauka ne a karkashin jagorancin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Duk wannan dan abin da za mu kawo maku kuma, baya ga irin kwararan matakan da wasu gwamnonin Jihohi suka dauka ne .

A ranar 28 ga watan Janairu, 2020, (watau wata guda kafin fara samun rahoton bullar Kwaronabairus na farko), gwamnatin tarayya ta bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin aniyar da take da ita da kuma irin shirin da ta yi na kara karfafa sanya ido a dukkanin manyan filayen sauka da tashin Jiragen sama guda biyar na kasar nan domin hana yaduwar cutar ta Kwaronabairus. Gwamnati ta shelanta filayen Jiragen saman kamar haka; na Enugu, Lagos, Ribas, Kano da kuma na babban birnin tarayya Abuja.

A ranar 28 ga watan na Janairu: Cibiyar kula da yaduwar cutuka ta kasa, (NCDC), ta sanar da cewa, ta rigaya ta kafa wata tawaga ta yakar cutar ta Kwaronabairus, kuma a shirye take da ta kaddamar da sashenta na ko-ta-kwana, ko da za a sami bullar cutar a kasar nan.

A ranar 31 ga watan Janairu: A sakamakon abin da yake faruwa dangane da cutar ta Kwaronabairus a kasar Sin da sauarn kasashen Duniya, gwamnatin tarayya ta kafa wata kakkarfar tawaga wacce aka shirya ta domin tunkarar annobar ta Kwaronabairus, wacce za ta nazarci irin illar da cutar za ta iya yi ko da za ta watsu har zuwa nan Nijeriya. A dai wannan ranar, hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ta fitar da wani jadawali wanda ya sanya Nijeriya da wasu kasashen nahiyar Afrika guda 13 a matsayin kasashe mafiya hadarin da za su iya kamuwa da cutar ta Kwaronabairus.

A ranar 27 ga watan Fabrairu: Nijeriya ta shelanta Kwaronabairus ta farko da ta bulla a cikin kasarta.

Tun a farko-farkon watan Maris: Ministan Lafiya na Nijeriya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da cewa mutane 60 da suka yi wata alaka da majinyacin Kwaronabairus din nan na farko dan kasar Italiya duk an gano su tare da kebe su – wadanda mutane 40 sun fito ne daga Jihar Ogun da kuma mutane 20 da suka fito daga Jihar Legos.

A ranar 9 ga watan Maris: Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ko-ta-kwana na Shugaban kasa wanda zai kula da bazuwar cutar a nan Nijeriya.

A ranar 17 ga watan Maris: Nijeriya ta dage bukin wasanninta na kasa wanda aka shirya gabatarwa a birnin Benin daga ranar 22 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu.

A ranar 18 ga watan Maris: Kwamitin ko-ta-kwana na Shugaban kasa a kan cutar fa Kwaronabairus a lokacin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai ya sanar da cewa ba za a sake barin matafiya daga kasashen nan 13 su sake shigowa Nijeriya ba, har sai an gama da annobar ta Kwaronabairus.

Nijeriya ta haramta shigowar mutane daga kasashen Sin, Italiya, Iran, Koriya ta kudu, Spain, Japan, Faransa, Jamus, Amurka, Norway, Ingila, Netherlands da Switzerland. Duk wadannan kasashen suna da tarihin samun sama da mutanen kasar 1000 da suka kamu da cutar ta Kwaronabairus ne a cikin kasashen na su.

Gwamnati kuma ta dakatar da bayar da biza daga wadannan kasashen.

Gwamnatin tarayya ta kuma dakatar da bayar da biza a lokacin da baki suka shigo cikin kasar nan, ga wadanda suka komo daga wadancan kasashen da aka lissafta a sama. Duk matafiyan da suka komo daga wadancan kasashen na sama bayan an dakatar da shigowar na su za su kasance ne a kebe, tare kuma da sanya idon hukumar ta NCDC.

A ranar 18 ga watan Maris: Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima, ta dakatar da bayar da shirin horaswa ga masu yi wa kasa hidimar da suke a rukuni na A na kwanaki 21 har sai abin da hali ya yi. An fara gudanar da shirin horaswan ne a ranar 10 ga watan Maris, wanda kuma ake sa ran kare shi a ranar 30 ga watan na Maris, kafin a dakatar da shirin baki-daya kwaki 8 da fara shi.

A ranar 18 ga watan Maris: Nijeriya ta haramta yin tafiya zuwa kasashe 13 wadanda suke da mafi hatsarin kamuwa da cutar sune kuwa kasashen: Amurka, Ingila, Koriya ta kudu, Switzerland, Jamus, Faransa, Italiya, Sin, Spain, Netherlands, Norway, Japan da Iran.

A ranar 18 ga watan Maris: Hukumar gudanar da wasan kwallon kafa ta kasa ta dakatar da dukkanin wasannin kwallon kafa a kasar nan na tsawon makwanni hudu.

A ranar 19 ga watan Maris: Diyar Shugaban kasa ta kebance kanta a bayan da ta komo daga wata tafiya da ta yi zuwa kasar Ingila.

A ranar 20 ga watan Maris: Gwamnatin Nijeriya ta sanar da kulle dukkanin manyan makarantu, Makarantun Sakandare da na Firamare na kasar nan.

A ranar 20 ga watan Maris: Nijeriya ta tsawaita haramcin tafiya zuwa wasu kasashe guda biyu, su ne kuwa kasashen Sweden da Austria.

A ranar 20 ga watan Maris: Nijeriya ta sanar da kulle manyan filayen Jiragen sama na Enugu, Fatakwal da Kano.

A ranar 21 ga watan Maris: Kamfanin sufurin Jiragen kasa na kasa ya sanar da dakatar da sufurin fasinjoji  tun daga ranar 23 ga watan na Maris.

A ranar 21 ga watan Maris: Nijeriya ta sanar da kulle sauran manyan filayen Jiragen sama guda biyu da suka rage, na Abuja da kuma Legos.

A ranar 23 ga watan Maris: Alkalin alkalai na kasa, Mai Shari’a Tanko Muhammad, ya umurci da a kulle dukkanin kotunan kasar nan daga ranar 24 ga watan na Maris.

A ranar 23 ga watan Maris: Nijeriya ta sanar da dakatar da taron majalisar zartarwa ta kasa da kuma na majalisar zartarwa ta Jihohi na kasa har sai abin da hali ya yi.

A ranar 23 ga watan Maris: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar da dakatar da dukkanin ayyukanta har na tsawon kwanaki 14.

A ranar 24 ga watan Maris: Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu na kasar nan ta dakatar da aikace-aikacenta na tsawon kwanaki 14.

A ranar 24 ga watan Maris: hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gwamnati ta sanar da dage shirya jarabawar a dukkanin makarantun hadin kai guda 104 da suke a sassan kasar nan wanda a baya aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan Maris.

A ranar 24 ga watan Maris: Hukumar babban birnin tarayyar kasar nan ta sanar da kulle dukkanin shaguna da kasuwanni gami da wuraren shakatawa da suke a babban birnin tarayyan ba tare bata lokaci ba, face dai masu siyar da kayayyakin abinci, magani da sauran kayan bukatu na yau-da-kullum.

A ranar 24 ga watan Maris: Hukumar ta babban birnin tarayya ta sanar da haramta yin duk wasu taruka a Cocina da Masallatai.

A ranar 25 ga watan Maris: Gwamnati ta sanar da kulle filin Jiragen sama na garin Asaba, tun daga ranar 27 ga watan Maris; kan iyakoki na kasa daga ranar 29 ga watan Maris.

A ranar 26 ga watan Maris: Babban bankin kasar nan ya sanar da gudummawar da aka samu domin yakar annobar ta Kwaronabairus, daga hannun manyan attajiran kasar nan su Bakwai da kuma wasu bankuna. Bankin Access Bank ya hada karfi da babban attajirin nan na Afrika, Aliko Dangote, domin samar da kayayyakin magani da wuraren kebe wadanda suka kamu da cutar a sassan kasar nan.

A ranar 26 ga watan Maris: Gwamnatin tarayya ta karbi gudummawar akwatuna 107 daga kasar Sin wadanda suke kumshe da kayayyakin maganin cutar da suka hada da ababen toshe baki da hanci, da tufafin kare kai, da garkuwan fuskoki gami kuma da ababen duba cutar.

A ranar 27 ga watan Maris: Gwamnatin tarayya ta saki naira bilyan 10 ga Jihar Legos da kuma naira bilyan Biyar ga babban birnin tarayya Abuja, a matsayin tallafi na musamman ga hukumar kare yaduwar cutuka ta kasa NCDC domin samar da kayan aiki, samar da jami’ai da wuraren bincike a sassan kasar nan.

Kulle manyan filayen Jiragen sama na kasar na, da kuma kan iyakokin kasa na kasar nan har na tsawon makwanni hudu a matakin farko, domin bayar da damar kasar nan ta gabatar da wasu tsare-tsaren da suka dace, da samar da kayayyakin yakar wadanda suka kamu da cutar a gidajensu.

Manyan Jiragen daukan kaya na ruwa ne kadai da suka shafe sama da kwanaki 14 a ruwayen kasarmu za a bari su iso tashoshin Jiragen ruwan namu, bayan an bincike su sosai an yi masu gwajin cutar an kuma tabbatar da ba su yiwo guzurin annobar zuwa cikin kasarmu ba.

Hukumar ta NCDC za ta kirawo dukkanin jami’anta da suka yi ritaya domin karfafa jami’ai a cikin hukumar.

Hakanan kuma, dukkanin jami’an hukumar ta NCDC da sauran kwararru da suke wajen kasar nan domin karo ilimi ko kuma halartar wasu taruka na musamman za su hanzarta komowa. Rundunar Sojin sama ta kasar nan za ta yi aikin jigilar komowa da wasu ‘yan Nijeriya musamman daga kasar tsakiyar Afrika.

Gwamnati kuma ta fara duba yiwuwar yin gyara a kasafin kudinta.

Shugaba Buhari ya bukaci Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari da ya yi aiki tare da kungiyar masu masana’antu ta kasa domin tabbatar da samar da mahimman ababen bukata kamar na kayan abinci, magunguna da makamantansu.

Ministan lafiya ya sanar da cewa wadanda suka kamu da cutar ta Kwaronabairus guda 65 duk suna da tarihin yin tafiya zuwa kasashen waje a cikin makwanni biyu da suka gabata.

Ministan lafiyar ya yi tsokaci da cewa, a yanzun haka dai Jihar Legos ce ke matsayin cibiyar masu dauke da cutar ta Kwaronabairus a kasar nan.

Ministan kuma ya karafafa zaburantar da ma;aikatan sashen lafiya a dukkanin matakai da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana domin ganowa da bayar da hadin kai ga dukkanin wadanda ake tsammanin sun kamu da cutar ta Kwaronabairus a kowane sashe na kasar nan. Ya kuma kara da cewa, a lokacin da ya kasance duk an kulle tashoshin Jiragen kasa, kan iyakokin kasa na kasar nan da manyan filayen Jiragen sama na kasar nan, ya kuma kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakan kariya a kan tashoshinmu na Jiragen ruwa.

Ministan ya karfafa tsarin nan na nisantar juna a lokacin da yake cewa, ya sha nanata hakan. Ya kuma kara da cewa an bayar da umurnin a kasa baki-daya da kuma mataki na Jihohi da a takaita yawan tarukan jama’a, da suka hada da na tarukan Addini da na bukukuwa, siyasa da aikace-aikacen makarantu da sauran su.

A ranar 27 ga watan Maris: Shugaban ma’aikta na tarayya ya fitar da farar takarda  inda yake umurtan ma’aikatan gwamnati da suke a matakin albashi na 12 zuwa kasa da su rika gabatar da ayyukansu daga gida.

Ana kuma ci gaba da kokarin zakulo dukkanin wadanda suka yi wata alaka da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

Ma’aiakatar lafiya ta tarayya tana yin aiki ba-ji, ba-gani, tare da kwamitin ko-ta-kwana na Shugaban kasa a matakin Jihohi domin yakar cutar ta COBID-19, ta hanyar sake yin dubi a kan matakan da suka dauka domin kare lafiyar ‘yan kasar Nijeriya.

Ministan lafiya ya kuma karfafa samar da layukan wayar ko-ta-kwana na hukumar ta NCDC wadanda suke kasancewa a bude a kowane lokaci cikin awanni 24. Hakanan Jihohi su ma suna da na su layukan wayar ta ko-ta-kwana, wadanda za a iya kiransu a kyauta kai tsaye domin amsa tambayoyi a kan annobar ta Kwaronabairus, ya kuma bukaci al’umma da su hanzarta sanar da labarai na gaskiya da suka shafi cutar ta COBID-19.

Exit mobile version