Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon D'Or
  • English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

byAbba Ibrahim Wada
3 days ago
Ballon D'Or

Kyautar lashe gasar Ballon d’Or yanzu ta zama kyautar da take auna kokarin dan wasa ko kuma wadda take fayyace dan wasan da ya fi nuna bajinta a duniyar kwallon kafa musamman a tsakanin matasa.

A karshen watan da ya gabata ne aka yi bikin karrama gwarzon ‘yankwallon kafa na duniya na shekarar 2025, inda aka karrama fitattun ‘yanwasa da suka nuna bajinta da kwarewa a kungiyoyi da kasashensu a kakar da ta wuce. Kyautar Ballon d’Or, karramawa ce da take da matukar tasiri a kwallon kafa, inda duk da cewa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA tana karrama gwarazan da take gani su ne kan gaba a duniya, an fi kallo tare da amfani da karramawar ta Ballon d’Or a matsayin wadda ta fi daraja.

  • Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
  • Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

A taron na, fitaccen danwasan kasar Faransa da kungiyar PSG, Ousmane Dembele ya lashe kyautar ta bana a bikin wanda aka yi a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa.

Aitana Bonmati ce ta lashe Ballon d’Or ta bangaren mata, wanda shi ne karo na uku da ta lashe kyautar a jere. Wani abu da ya ja hankalin masu bibiyar karramawar daga Nijeriya shi ne yadda mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta mata wato Super Falcons, Chiamaka Ndanozie ta zo ta hudu a cikin masu tsaron raga mata a duniya.

Wadanne fitattun ‘yan kwallon kafan Nijeriya ne suka kusa lashe kambun a tarihin karramawar?

BICTOR IKPEBA – 1997

Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997.

ADEMOLA LOOKMAN – 2024

A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a gasar cin kofin Afirka.

FINIDI GEORGE – 1995

Finidi George danwasan Nijeriya ne da ya yi tashe sosai a shekarun baya a Nijeriya da kungiyoyin Turai. Ya samu shiga cikin zaratan ‘yankwallo na duniya ne a shekarar 1995 bayan nasarar da ya samu a kungiyar Ajad ta Holland, inda ya samu shiga cikin jerin bayan an fadada karramawar zuwa kasahen da ba na turai ba.

A gasar Champions League ta shekarar 1995, Finidi ya zura kwallo tara, sannan ya bayar aka zura kwallo 11 kuma a shekarar ne Ajad ta lashe gasar Champions League da gasar Eredibisie ta kasar Holland da wasu kofuna uku. Amma a shekarar dan wasa Finidi ya kare a mataki na 21 a shekarar 1995.

BICTOR OSIMHEN – 2023

Danwasan kwallon gaba na Nijeriya wanda a yanzu haka yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Galatassary ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Napoli wajen lashe gasar Serie A karon farko a shekara 33, sannan ya lashe wanda ya fi zura kwallo a shekarar ta 2023.

A shekarar ce Osimhen ya zo na takwas a duniya sannan kuma duka a shekarar dan wasa Bictor Osimhen shi ne ya lashe gwarzon dankwallon Afirka mafi kwarewa a shekarar 2023.

NWANKWO KANU – 1996 DA 1999

Shahararren dan wasa Nwankwo Kanu na cikin zaratan ‘yankwallo kafa ‘yan Nijeriya suka dade suna jan zarensu a harkar tamaula. A shekarar 1996, Kanu ya samu kuri’a 14, inda ya zo na 11 bayan ya lashe kofin Olympic da aka buga a Atlanta, da kuma rawar da ya taka a kungiyar Inter Milan ta Italiya.

Haka kuma a lokacin da ya koma Arsenal, tsohon kyaftin din na Nijeriya ya sake samun shiga, inda a shekarar 1999 ya zo na 23 a duniya. Sanan tsohon danwasan na Arsenal ya lashe karramawar gwarzon dankwallon Afirka sau biyu a shekarun 1996 da 1999.

ASISAT OSHOALA – 2022 DA 2023

Mace mai kamar maza, Asisat Oshoala ita ce ‘yarkwallon Nijeriya mace da ta fi lashe kambun gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka. Sannan ita ce mace ta farko daga Nijeriya da ta fara shiga jerin wadanda aka karrama a Ballon d’Or ta mata. Bayan lashe gasar Champions League ne ta zama gwarzuwa ta 16 a duniya a shekarar 2022, sannan ta sake zuwa ta 20 a shekarar 2023.

CHIAMAKA NNADOZIE – 2025

A bikin karramawar ta bana kuma, mai tsaron ragar kungiyar Brighton & Hobe Albion ta Ingila, Chiamaka Nnadozie ce ta samu tagomashi, inda ta zo ta hudu a cikin masu tsaron raga mata a duniya, wanda shi ne matsayi mafi girma da Nijeriya ta taba samu a karramawar. Chiamaka Nnadozie ta lashe kofin gasar cin kofin Afirka na mata sau biyu a 2018 da 2024.

A Afirka dai an samu dan wasa George Weah, dan kasar Liberiya wanda ya taba lashe kyautar Ballon d’Or a duniya, kuma tun daga wancan lokacin har yanzu ba a sake samun wani dan wasa daga nahiyar Afirka ba da ya sake lashe kyautar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane
Wasanni

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni
Wasanni

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

October 6, 2025
Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar
Wasanni

Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar

October 6, 2025
Next Post
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version