Kokarin Gwamnati Na Bunkasa Noma Zai Samar Da Arziki Ga Kowa A Nijeriya –Munzali

Kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na farfado tare da bunkasa harkar noma a Nijeriya ta hanyar zuba makudan kudade da samar da shirye-shiryen da za su taimaka ga cim ma wannan buri na gwamnati, babbar hanya ce ta samar da arziki ga al’ummar kasar nan, da bunkasa tattalin arziki.

Mataimakin shugaban Kungiyar manoman auduga na kasa, ALHAJI MUNZALI DAYYABU ne ya bayyana haka ga LEADERSHIP A YAU ASABAR lokacin da suke tattaunawa a ofishinsa da ke Kano. A ci gaba da tattaunawar ta su, Munzalin ya nuna yadda gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ke bai wa harkar noma fifiko da ma wasu muhimman tasre-tsare da gwamnatin ta yi domin bunkasa harkokin noma Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

Daga cikin hanyoyi da gwamnati ke bi wajen bunkasa harkar noma a Nijeriya, shi ne bullo da bayar da bashi mai saukin biya ga manoma, ya ya ka kalli yadda wannan shiri na bayar da bashi ke gudana a tsakanin manoma?

Wannan shiri na bayar da bashi za a iya cewa, yana tafiya kamar yadda ake bukata, duk da yake dai ba a rasa wasu ‘yan matsaloli ba, amma dai za iya cewa, shirin na samun nasara. Domin kuwa a karkashin wannan shirin, ba zunzurutun kudi za a ba manomi ba. Za a ba shi kayan aiki da ingantaccen  iri da takin zamani da maganin feshi da ma buhun da bayan an kammala noman za a zuba amfanin. Wannan ya taimaka matuka wajen ganin cewa, duk wanda ya karbi wannan bashin ya yi noma, domin kayan noman aka ba shi.

Ya ya za ka kwatanta gwamnatocin baya da wannan gwamnati kan batun sha’anin noma?

Gasskiya za a iya cewa, wannan gwamnati na taka rawar gani, domin ta nuna kishin bunkasa tattalin arzikin wannan kasa ta hanyar rage dogaro da albarkatun man fetur, wanda gwamnatocin baya suka ta’allaka a kai. Saboda haka ne, wannan gwammnatin karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu buhari ta samar da shirye-shirye wadanda za su taimakawa manoma wajen bunkasa sana’arsu.

Kamar Wadanne shirye-shirye ne gwamnatin ta samar da kake ganin suna taimakawa wajen bunkasa noma a kasar nan.

Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai samar da bashi mai saukin biya ga manoma, shi wannan bashi ba zunzurutun kudi za a dauka a ba manomi ba, za ba shi kudin da ingantaccen iri da maganin ciyawa da na kashe kwari da taki, har ma da buhun da zai sa amfanin bayan ya gama aikinsa. Saboda haka ka ga wannan hanya ce da aka karfafawa manoma yin noman, ba wai a ba su kudi su je su kashe ba kawai. Saboda haka wannan salon bayar da bashi ya taimakawa manoma fadada harkokin nomansu. 

A matsayinka na daya da cikin shugabannin manoma na kasa, shin ka gamsu da kason da gwamnati ke warewa a bangaren noma?

Lallai na gamsu kwarai da gaske, domin kuwa gwamnatin na ware kaso ma fi tsoka a bangaren noma, domin da ma daga cikin manufofin wannan gwamnati shi ne samar da hanyoyin doron tattalin arzikin kasa, maimakon a baya dogaron da aka yi a kan mai gabaki daya.

Saboda haka, na ma wani abu da mutane da yawa ba su sani ba shi, kudin da gwamnatin tarayya ta ware wa bangaren noma ya fi dukkan kudaden da aka ware domin gudanar da ayyukan wasu tituna a Kudancin kasar nan. wannan ya nuna tabbas cewa, gwamnatin maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari dagaske take yi wajen bunkasa noma a Nijeriya, yadda zai zama hanyar dogaro da kai da samar da ayyukan yi ga dimbin al’umma da kuma samar da abubuwan sarrafawa ga masana’antunmu.

Wane tasiri kake ganin rufe iyakokin da gwamnatin Nijeriya ta yi zai haifar, a harkar noma a fadin kasar nan?

Zan iya cewa, gwamnati ta yi hangen nesa matuka wajen rufe iyakokin kasar nan domin kuwa, ma fi yawa kamfanoni ga amfani ana nomawa a cikin kasar nan amma sais u ki sayen na gida su fita kasashen waje su sayo, wannan na taimakawa wajen faduwar farashin amfanin gona a wannan kasa. Idan kuma haka ta faru babban wanda ke shan wahala shi ne manomi, domin kuwa, idan ya kai amfanin gonarsa kasuwa, ba zai samu ribar da yake bukata ba, wadda za ta karfafa masa gwiwa wajen ci gaba tare da kara bunkasa wannan sana’a ta sa ta noma.

Saboda haka wannan rufe iyakokin da gwamnatin tarayya ta yi zai sa dole manyan kamfanonin da ke kasar nan su sayi kayan sarrafawarsu a cikin gida, musamman wadanda ke sarrafa kayan amfanin gona. Wannan za ta sa darajar amfanin ya daga, manoma su ci riba, su yi farin ciki kuma su kara fadada gonarsu. Don haka ka ga wannan babban alheri ne ga manoma.

Idan ka duba yadda aka samu hanyoyin sarrafa shinkafa a kasar nan za ka ko ‘yan kasar wajen ba ta fi ta mu kyau ba. Ka ga abin da ya sa muatane suka yi kokarin gyarata har ta maye gurbin wadda ake kawowa daga kasashen waje shi ne, rufe iyakokin da gwamnatin ta yi.

Wannan ta sa ake ganin cewa, rufe kan iyakokin kasar nan sai sa Nijeriya ta ajiye Naira Biliyan 150 a kowace shekara. wannan kudi zai taimaka sosai wajen kara habaka tattalin arzikin wannan kasa ta mu.

Ka san duk lokacin da wani abu na takura ya faru a  kan dan’adam daga wannan lokacin zai fara nemawa kansa mafita. Saboda haka mafitar da ‘yan Nijeriya suka samawa kansu ita ce, ta samar da inagantacciyar shinkafa wadda za ta kalubalanci ‘yan kasar waje. Zuwa wannan lokaci kuma za a iya cwa, an samu nasarar yin hakan.

Wane sako kake da shi ga manoman kasar nan?

Babban sakon da nake da shi, manoma shi ne, musamman wadanda suka karbi bashi, su tabbatar da cewa, sun biya wannan bashi kamar yadda aka tsara biya. Domin sai wadanda suka karba sun biya ne za asamu damar ba wasu.

Kana da wani sako ga gwamnati?

Babban sakona shi ne, ina yabawa wannan gwamnati karkashin shugaban kasa maigirma Muahammadu Buhari bisa nuna fifiko a harkar noma, wanda hakan kuma ya taimaka wajen wadata kasa da abinci da samar da ayyukan yi ga dimbin al’ummar kasa. Saboda haka ya yakamata, mu ci gaba dab a wannan gwamnti goyon baya yadda za ta ci gaba da samar mana da sabbin tasre-tsare wadanda za su kara taimaka mana wajen bunkasa harkokin noma.

Exit mobile version